Sashe 127
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Allah ya taimake ka, dama wata muhimmiyar magana ce ke tafe da ni, wani hukunci na yanke da zartar da shi dole sai da izininka, kuma kai zaka yi mini jagora zuwa ga tabattauwar abun cikin hukuncin Allah"
Ya jinjina mata kai cikin nutsuwa alamar yana sauraren ta.
Ta ɗora da cewa "To bisa ga al'ada ta masauratar nan, duk cikakken ɗa a gidan nan, a kan yi masa zaɓi na matar da zai aura, ko ya kawo wadda yake so ƴar mutunci idan ta yi a aura masa. wani abu ne ya taso a kan yarinyar nan rumaisa, ƴan unguwar su suna ta yaɗa jita-jitar wai ciki ta yi aka kaita aka ɓoye ta haihu, sunanta dai ya ɓaci a unguwar su, na ga babu wata hanya da zamu bi domin wanketa face Adam ya aureta, duba da irin matsanancin son da take yi wa yaron nan da ta zo da shi, har ina ganin kamar rabata da yaron na shiga hakkinta, saboda na san ciwon abun, ga wannan abu da ya kunno kai game da rayuwarta, na ga abu ɗaya zan iya yi shi ne in sanya adam ya aureta, amma ya ka gani ranka ya daɗe?".
Turaki ya ce "Ikon Allah, kin ga nan Jamil ya zo mini da zancen, akwai buƙatar Samha ta maye gurbin Fulani, duba da yadda ta daɗe tana son adam, dan har na yi na'am na so na tuntuɓeki, to sai gashi kuma kin zo da wani zance da yakamata a tsaya a duba. Tabbas! Idan har da yadda zamu yi yarinyar nan bai kamata mu bari ta wulaƙanta ba, dan haka a wannan karon ma samha sai dai ta yi haƙuri, ko kuma idan yana da ra'ayi ya haɗasu biyu, amma rumaisa ita tafi cancanta ya aura, duk da ƙanƙantarta".
Ammi ta É—an ji rasss, ba za ta yi fatan adam ya haÉ—a rumaisa da samha ba, duk da rumaisa yarinya ce amma ba za ta yi fatan ta zama bora ba, tun da dai haryanzu ba ta isa rayuwar aure ba, tana son ya aureta ne dan ya inganta rayuwarta, a haka idan ta ce za su cigaba da É—awainiya da rumaisa, Æ´an uwanta ba zasu harda ba, dan ta lura suna da gudun abun hannun wani.
Turaki ne ya katse mata tunanin ta hanyar cewa "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kin san akwai ƙalubale, a ƙa'idar masarauta, ƴaƴan sarakuna ƴaƴanmu suke aure, ko ƴaƴan wasu manya, akwai gwagwarmaya idan aka kai maganar nan gaban su wambai"
"Allah ya taimakeka shi ya sanya na zo wurinka, na san kai kaÉ—ai ne zaka iya shiga lamarin nan ka tsayawa adam, jikina yana bani akwai alkhairi a game da lamarin nan, rumais alkhairi ce ga adam"
Ya ɗan yi shiru ya ce "To babu laifi, in Allah ya yarda idan na dawo, zamu yi magana da su, na sanya zancen cikin addu'a idan alkhairi ne Allah ya tabattar ya kawo komai da sauƙi"
"Amin ya rabb, idan komai ya daidaita bana son abun ya wuce watanni uku, kar wani abun ya kutso"
Turaki ya ce "Babu damuwa, babu abun da zai gagara da ikon Allah"
Ammi ta risuna, ta sake yi wa turaki godiya, sannan ta tashi ta fita.
Samha ce ta raka ammi har mota, tana yi mata ta gaida gida.
Ammi na tafiya samha ta koma É—akin ta, ta É—au wayarta ta kira jamil.
Yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Yaya jamil, yau ma ammi ta zo wurin mai girma turaki, dan Allah idan ka zo yau ka tuntuɓe shi da maganar, ka ji ko ita suka yi?"
Jamila yayi tsaki ya ce "Ke kin fiye abun haushi wallahi"
"Dan Allah yaya ka taimaka".
Ya ce "Gaskiya bana nan, bana gari sai dai ki jirana dawo, idan na dawo kuma yana umara, na san duk abun da ake ciki dai, in dai a kan maganar ne zasu tattauna da mama"
Samha ta É—an yi shiru sannan ta ce "To shikenan, na gode " ta kashe wayar cike da fatan Allah ya sa tattaunawa suke a kan ta maye gurbin Fulani.
***
Ana idar da sallar magariba, Huzaifa ya saka rumaisa a gaba yana ta mata faɗa, ta ƙi cin abinci sai mita take a kan abun da aka yi mata a unguwa.
Aikowa aka yi wai ana sallama, ganin ba a faÉ—i da wa ake sallamar ba, ya sanya Usman tashi ya fita ya ga waye yake yin sallamar.
Aikuwa yana fita ya tarar da mijin maƙwabciyarsu, ya kawo ƙarar rumaisa a kan abun da ta yi musu, na jifa a cikin gida ta yi musu ɓarna, ga uwa uba fashewa matarsa baki ada marmara da rumaisa ta yi.
Usman ya ce "Malam shamsu ai ɓarnar da matarka ta yi mana ta fi wadda ruma ta yi mata, shiru kawai muka yi, duk yadda ruma take girmamata bai hanata yi mata ƙazafi a cikin unguwa ba, ba dan mama ta hana ba, ga kuma albarkacin aure, sai na yi mata wankin babban bargo a cikin unguwar nan, amma tun da abun ya zo da haka, kawai duk sai mu haɗu mu yi haƙuri".
Cikin takaici malam shamsu ya ce "Au haka ma zaka ce? Ta rotse mana ƙwan lantarki na tsakar gida, ta fashe mana glass ga zubarwa da matata jini, amma ka gaya mini wannan maganar?".
"To me zance maka, yanzu dai idan baka haƙura ba, kai ma ka tsinto duwatsu ka yi mana jifa a cikin gidan, ko in kirawo maka rumaisa ka daketa ko? Sai ka huce" aikuwa malam shamsu ya harzuƙa ya fara zage-zage, Usman kuwa ya zage shima yana ramawa, suka nemi bawa hammta iska.
Mama har ta manta da Usman ya fita, ta jiyo zage-zagen usman, yana idan baa rufe masa baki ba, sai ya falla masa mari, kuma ya ɗaga shi ya buga da ƙasa.
Cikin tsananin faÉ—uwar gaba mama ta taso, hankali a tashe za ta fita, Huzaifa ya ce "Mama ba zaki fita ba, yaya usman bai fiye faÉ—an rashin gaskiya ba, kuma yaya Abubakar yana kusa, na san zai raba"
Mama ta ce "Kai dan ubanka bani hanya, kar ya janyo mini magana, na ji da malam shamsu suke yi, ba zai wuce a kan abun da rumaisa ta yi bane, usman in dai a kan rumaisa ne, ko ba ta da gaskiya goya mata baya yake yi, shi ba ya bin komai a sannu, wani fannin halinsu ɗaya da ita, zuciyarsu babu afuwa" mama na cikin maganar yaya Abubakar ya shigo hannunsa riƙe da na usman yana yi masa faɗa.
Usman ya ce "Haba yaya, mu bamu suka fi yi wa illa ba, sun yi mana baƙin fenti a unguwa, bamu yi magana ba sai shi, wai shi tattabara wanda ya yankewa ƙauna cibiya, shi ga mai mata, banzar matar da fuska kamar baƙar jaka, wallahi da namiji ce sai na yi mata shegen duka".
Rumaisa ta ce "Ƙazama da ita ba, mai bleaching"
Mama ta dungurewa rumaisa kai, Abubakar kuma ya cigaba da yi wa usman faÉ—a.
Usman ya ce "Da ne nake adawa da aurar da rumaisa, amma wallahi yanzu na zubar da makaman yaƙi na bi, wallahi party zamu shirya na tashin hankali a unguwar nan, mu hayo dokuna ayi ta kilisa, zamu kaita gidan manyan mutane, mu ga ƙarshen munafurci, mu rufe bakin munafukai" ya kalli rumaisa ya ce "Ke, dan ubanki na daina adawa da auren nan, ki yarda kawai, kuma daga yau daga ita har mijinta kar ki sake gaishe su, ta kuma yi miki maganar banza, zan samo miki duwatsu, daga nan har bamfai ba mai shari'a da ke yarinya ce, na tsaya miki ayi da ni".
Mama ta ce "A'a babu ruwana, kai maimakon ka saita yarinyar nan, ku bi komai a sannu amma kana yi mata huÉ—ubar tsiya, Nuraini har da kai fa kake zigata take rashin ji, babu ruwanka da mutumin nan ku fita sabgarsu, ni ba zan iya tashin hankali da mutane ba".
Usman ya miƙe ya ce "Mama irin masu haƙurinki ake cuta, komai ki ce ayi haƙuri a barwa Allah, da haƙurinki muka ɗauko, muna zaune za a fille mana wuya ki ce mu yi haƙuri"
Dariya rumaisa ta yi, mama kuwa ta rarumi takalmi, ta jefawa usman, ya goce tare da shigewa É—akinsu.
Ruma ta ce "Allah ya biya yaya usy nawa, Allah ya bar mini kai".
"Ki cigaba rumaisa, yayi ta ɗoraki a keken ɓera ya kai ki ya baro, tun da ke dai ba namiji bace ba".
***
Ko da ammi ta koma gida, Nusaiba da Iman suka tareta suna tambayarta yaya suka yi da turaki?
Nan ta kwashe komai ta gaya musu, iman ta ce "Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya mai girma turaki ya shawo kansu komai ya tafi cikin sauƙi, ni dai ina sonta wallahi"
Nusaiba ta ce "Mhmm, ni kam kawai yadda za ayi zaman nan nake hangowa, ba fa sa shiri ammi, kin ga ita tana da tsiwa, shi kuma akwai faÉ—a"
Ammi ta ce "Ke rabu da shi, rayuwar aure ta fi ƙarfin wasa, idan suka zauna za su nutsu, sannan a rayuwarsa da ita akwai wani darasi da nake fatan ya koya, kuma kan ayi auren ai dolensa ya dinga zuwa wurinta su saba"
Iman ta yi murmushi ta ce "Akwai rikici kenan?"
Ammi ta ce "Ta bani tausayi É—azu da muka yi waya, wai an ce ta yi cikin shege, ana yi mata kallon Æ´ar iska, saboda ta zo da sabir, idan ban saka takawa ya aureta ba, shikenan an yi mata mummunan tambari, mutane É—a idan ba na su bane ba, sun din ga janyo masa jafa'i kenan"
Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya shirya, ya tabbatar da alkhairi" suka amsa da amin.
Baba uwani da take laɓe ta ji hirar ta su sama-sama, sannan bakomai ta ji ba, amma a abun da ta jin, ta ƙudurce za ta je ta sanar da Mummy.