← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 174

Sashe 166

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalli rumaisa yana jiran ya ji me za ta ce "Wai cewa yayi zai ƙara aure, saboda ba ni da nono!!!"

Tirƙashi!.

Ayshercool

*Chat me on what's app, to subscribe yours 08081012143, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank*
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Sai da falon yayi tsit na wucin gadi, Adam bai taɓa tunanin wautar rumaisa ta tsananta har haka ba. Ji yake tamkar yayi layar zana ya ɓace daga wurin.

Ta kuma cewa "Ammi, kuma yana yawo babu riga a cikin gidan nan, kuma alhalin ni ba muharammarsa ba ce, Yaya usy ya ce yayyena ne kawai muharramaina, amma yake yawo ba riga, ina kallonsa, ko kunya ba ya ji".

Wani kallo ya yi wa rumaisa, amma ta share shi ta ce "Ai dama na rantse sai na faɗa mata, ammi ta ce duk abun da ka yi mini na rashin kyautawa na gaya mata. Hmm ni  ko za a shekara nawa idan aka yi abu bana mantawa, ina riƙe da shi a zuciyata, ina sane sai yau na ce bari na gaya wa ammi".

Ammi ta yi murmushi cike da dattaku ta ce "Haba dai, wace irin kishiya ana zaman lafiya, tsokanarki yake yi kawai, wanda yake da wannan zuƙeƙiyar yarinya, ina ruwansa da wani ƙara aure. Kuma in dai saboda wannan abun ne, rai dai an fille wa fara kai, muna zaune Allah zai kawo su".

"Ammi ai hijjabi zan koma sakawa, ya daina saka mini ido, dama na ce gara in gaya miki, ba zan gayawa mama ba, saboda na fuskanci yanzu mama ta fi son sa a kaina, cewa za ta yi ƙarya nake yi, kuma ita ta ce duk wanda ya gaya mini maganar banza, wadda ta saɓa da tarbiyyar da take yi mana, in je in gaya mata. Shiyasa nake gaya mata komai, amma na san a wannan karon da zan gaya mata abun da ya yi, ba zata yadda ba".

"Da gaskiyarki kam, mama ta yi iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar ku, bai kamata ta rushe ba, Allah ya cigaba da dafa muku, bar mini litattafan naki na cigaba da gani, duba ɗakina, ko Sabir ɗin ya tashi, zamu yi wani sirri da ke".

Rumaisa ta tashi ta nufi É—akin Ammi, ka sa haÉ—a ido Adam ya yi da ammi, ji yake kamar ya zama guguwa ya bar wurin, saboda takaici da kunya.

"Takawa" ya É—an É—aga kai amma bai kalli ammi ba.

"Ka din ga sanin me zaka gaya mata, tun da ta ce ko za a shekara nawa ba ta manta abu, na ga hakan a cikin idonta, a hankali zaka nusar da ita abun da ya shafi sirrin aurenku naku ne, ta daina faɗa, na san kana haƙuri amma ka ƙara nan gaba zaka ci ribar hakan in sha Allah". Ya jinjina wa Ammi kai ya tashi ya nufi ɗakin ammi, bin bayan rumaisa.

Ammi ta ce "Dan Allah kar ka yi mata wani abun, Allah ya taimake ka, daga ni sai ku ta faÉ—a, Iman ta riga ta tafi amsa waya, kar ka ce zaka yi mata wani abu".

"Babu abun da zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haɗa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taɓa zuwa gida ba".

Ammi ta ce "Masha Allah, babu laifi"

Rumaisa tana zaune a gaban sabir, da yayi ruf da ciki a kan gado, yake ta bacci, sai shafa sumar kansa take yi tana murmushi. Da hannu É—aya ya É—aga rumaisa ya juyota tana fuskantar sa.

"Me na yi maka?".

"Ban sani ba, ke wace irin yarinya ce sai ka ce na'ura mai ƙwaƙwalwa, kanki gaba ɗaya baya gaya miki abun da ya dace, iya abun da aka zuba miki shi ne yake aiki a kanki, ammi fa sirikarki ce, ya dace ki gaya mata wannan maganar?".

Ta kalleshi ta ce "Meye wani sirika kuma, ni ammi babata ce, haka mama ta gaya mini, ka ci sa'a da ba komai na gaya mata ba, har da cewa nonona bai fi girman wake ba, duk wannan rufa maka asirin da na yi ba ka gode ba, ga  gingimen asirin da na daɗe ina rufa maka"

Adam ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba dai aure ba, zan ƙara aure ba zan zauna da ke ba kamar namiji ba, ba zan iya ba daga nan ki je ki cigaba da faɗa"

"Ni ba zan kula ka ba baban sabir, na san haushina ka ke ji saboda na faÉ—i abun da ka ke yi, ni da kai idan na ce zan yi maka nasiha, ba yadda za ka yi ba, amma yanzu na san idan ammi ta yi maka faÉ—a zaka yadda"

Rumaisa ta zubawa sabir ido, Ammi ta shigo, ta ce "Maman sabir, Haryanzu ba ki gama ganin sa ba?".

"Wallahi kuwa ammi, bana gajiya da kallonsa ni ai".

Ammi ta zauna a gefen gado ta ce "Zo ki zauna a kusa da ni mu yi sirri Æ´ar auta".

Rumaisa ta tashi ta zauna a kusa da Ammi, Ammi ta ce "Kin ga dai ba kya so ya yi miki kishiya ko?" Rumaisa ta ce "Eh".

"Meyasa ba kya so?".

"Kai, ammi duk mata kowa sai na ji ta ce ba ta son kishiya, shiyasa nima na ce ba na so".

"To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faÉ—ar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daÉ—i".

Ruma ta ce "Ammi, ba dan ya ji haushi na faÉ—a ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daÉ—i ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini".

"Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faÉ—i irin wannan a gaban wani kin ji?"

"To ammi, in Allah ya yarda".

Ammi ta dafa kafaÉ—arta ta ce "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa'a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan É—auko, har gida ta din ga koya miki ".

"Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya"

Ammi ta ce "Waye papa kuma?"

"Baban Sabir "

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku"

Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta.

Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu.

Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani ɓangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaɗi.

Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu.
Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa.
Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta ɓullo wani wuri.

Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi.

Bayansa ta gano ta ce "Papa" a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta ɗan tsura masa ido, sai kuma ta ce "Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taɓa sawa na shigo gidan nan" ta yi maganar tana ƙarasawa in da yake.

Ya ce "Wow, ashe zamu sake haÉ—uwa, sannunki, ya ki ke?"

"Lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana zama a kujerar da ke facing ɗin sa.

"Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?"

Da É—an mamaki ta ce "Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

"Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?"

Ya É—an yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha É—azu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito.

"Da gaske ke adam ya aura?".

Rumaisa ta ce "Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?".

"Ina ƙasar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji".

Cikin mamaki rumaisa ta ce "To ta yaya kuna gida É—aya, amma ba ka sani ba, wai ku ba Æ´an uwa ba ne?".

"Eh, kowa babarsa daban".

"To, ku Æ´aÆ´an kishiyoyi ne?".

Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce "Eh".

"Taɓ to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?".

"Ni ma ba ya zuwa wurinmu"

Ruma ta ce "Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi".

"Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?"

"Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daÉ—i".

Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce "Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?"
Chapter 166 · 0% Book details