← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 174

Sashe 50

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ko zaki rama ne, ko da yake ba ki da abin ramawa ai, banbancin talaka da mai arziki kenan, na ga saƙonki, abin da ki ka ce na taɓa ɗin ni ban ganshi ba ranar, shi ne na biyoki yanzu in duba in gani ko akwai".

"Wai kai É—an iska ne?" Tayi maganar ba tare da jin nauyinta ba, ga babban mutum kamar Takawa, saboda ya kaita bango.
Maganar ta dake shi, amma ya ce "Eh shi ne, yayyen naki maza da ki ke taƙama da su, sai na kamasu na rufe, kuma na rushe gidan na ku, na ga ta tsiya".

Karo na farko da ruma ta tsaya aka sakata kuka, hawaye ya wanke mata fuska.

"Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka" tayi maganar har da dukan ƙirjinta.

Girgiza kai ya yi, ya buɗe motarsa ya shiga, ta durƙusa ta ɗebi taɓon wurin ta fara watsa wa motarsa, ya taka reverse ya sake wanketa da taɓon wurin ya tafi.

(*ALHAMDILILLAH, TIRKA-TIRKA, YA KUKE GANIN ZATA KAYA A TSAKANIN RUMAISA DA TAKAWA? WACE IRIN LARURA CE DA TAKAWA, KUMA MEYE ALAƘARSA DA MAITA DA HAJIYA JAMILA TA FAƊA? YA ZATA KASANCE? WANE DEAL NE KHALIFA YA SAKA SAMHA? MEYE TARIHIN GIDAN SU TAKAWA, DA ASALIN GABARSA DA ƊAN UWANSA. ME ZAI FARU IDAN RUMA TA JE KATSINA??? WA RUMA ZATA AURA, SHIN ZA TA NUTSU KO KUWA? KAR AYI BABU KU, MAI BUƘATAR BOOK2 YA TUNTUƁENI TA LAMBAR WAYATA 08081012143 YA YI PAYMENT*

Ayshercool
Whats app only, ban da kira Please 🙏 0808101214

[8/22, 11:40 PM] Maman Aslam: *Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haÉ—a mini document É—in littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haÉ—a mini document É—in littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

*AYSHERCOOL*

Cikin damuwa Huzaifa ya dube shi ya ce "To me ka gani da ba ka yarda da shi É—in ba?"

Cikin sanyin jiki Yasir ya ce "Wallahi kawai, ni mutanen cikin motar ne ba su yi mini ba"

Tsaki Huzaifa ya yi ya ce "Ka fiye matsala wallahi, dan Allah kar ma muje gida ka yi wannan zancen ka É—aga mata hankali" Yasir bai kuma cewa komai ba, suka tafi gida, sai dai shikaÉ—ai ya san abin da yake ji a jikinsa.

Ruma kuwa da suka tafi, sai kallon hanya take, tana murmushi dan tun da take, ba ta taɓa tafiya mai nisa ba, kuma ta yi sa'a a wurin taga take, dan haka take ta leƙe tana murmushi. Sai dai tun shigarsu, Aliyu ya lura da Mutanen da suke zaune a  gaban su, tun da suka hau motar mutanen suke waya da wani yare, wayar taƙi ci taƙi cinyewa, gashi ba mai iya fahimtar abin da suke faɗa a wayar.

Ruma kuwa sai surutu take wa Aliyu, kamar an jefeta a ka, ta ce wannan ta ce wancan. Aliyu dai bai tanka mata ba, sai Adduoi yake yi yana cigaba da kallon mutanen da tsarguwa da wayar da suke ta yi.

Ruma ta É—auko wayar nan ta wurin Yasir, ta din ga É—aukar kanta a hoto, ga wayar duk a ragargaje amma sai É—agawa take tana hoto, har da hoton hanya É—auka take, ta hau yin videon cikin motar tana É—aukar mutane.

Ko da suka bar gari suka shiga jeji, sai wannan mutane suka ce wa direba ya sauka daga kan kwalta, ya tafi ta gefen titi kan burji, ba tare da musu ba kuwa direban ya bi umarninsu, kuma aka rasa wanda zai yi magana a kan hakan kowa yayi shiru.

"Wai ya na ga ana bin gefen titi, ga kwalta É—oÉ—ar a lailaye?" Ruma ta yi maganar har sai da kowa ya waiwayo yana kallonta. ÆŠaya daga cikin mutanen ya yi murmushi amma ba wanda ya kulata.

"Ke uban wa ki ka ji yayi magana, sai ke haziƙa mazaruƙs, kar na sake jin bakinki ko na make ki" Aliyu yayi mata maganar cikin kashedi. Tura baki ta yi ta kawar da kanta gefe. Sai dai ba aje ko ina ba, ruma ta fara cewa Aliyu ita fa wannan zaman motar ya isheta.

"Wallahi idan baki kiyayeni ba sai na zane miki jikinki, ni na yi dana sanin tahowa da ke, babu wanda ake jin bakinsa sai ke? Ki rufe mini baki na gaya miki"

Kamar zata yi kuka ta ce "To ni fa na gaji ne, kuma yunwa nake ji, su wannan mutanen na gaba, ba tun da muka taho suke waya ba suke surutunsu, babu wanda ya damesu sai ni zaka ce na ishi mutane, ni wallahi yunwa nake ji ulcer ta zata tashi"

Riƙe kunnenta Aliyu ya yi ya ce "Yi mini shiru, a gidan uban wa ki ke da ulcer?"

"Cikina ne ya fara ciwo, yunwa nake ji"

"Wallahi zan zaneki idan baki shiru ba" haka ruma tayi shiru tana ƙoƙarin goge hawaye.

Sai da suka zo wani ƙaramin ƙauye, mutanen nan suka ce a tsaya, nan ma direban ya bi umarninsu ya tsaya, kowa yana son yin magana amma yana tsoro.

Aliyu ne ya fara fusata ya ce "Direba ya na ga an tsaya? Mu da muke sauri?"

Direban ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, wani saƙo za su karɓa mu wuce, yanzun nan ba daɗewa zamu yi ba in sha Allah"

Aliyu ya ce "Amma ai ba a haka, sai a nemi alfarmar na mota ba a tsaya kawai ba, wannan shiga hakki ne ai"

Sai da Aliyu ya yi magana, sannan sauran mutanen cikin motar suma suka fara ƙorafi a kan abin da aka yi.
Yayin da mutanen suka yi shiru ba su kula kowa ba.

Sun kai mintuna sha biyar, sannan wasu mutane suka ratso cikin dajin  a babura, mutanen suka sauka, suka karɓo wata uwar jaka, sannan suka dawo motar. Ɗaya daga cikin su ya dubi ruma cikin gurɓatacciyar hausar sa ya ce "Ke ki ka ce ki na jin yunwa ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh.

Ya bata wata baƙar leda, ta karɓa ta ce "Na gode" Aliyu ya bi ruma da kallo dan ya rasa me yakamata yayi mata, kawai ba ta san mutum ba ya bata abu ta karɓe.

Gasashshiyar kaza ce a ciki, da ruwan roba, ta waro ido ta ce "Laa yaya kaza ce"

Ya harareta ya ce "Mayya, tun da baki taɓa cin kaza ba, idan ki ka ci sai na miki dukan tsiya"

Ta ɓata fuska ta ce "To in mayar masa, in ce ka hanani ci?" Banza yayi mata, ganin bai kulata ba ya sanya ta saka hannu ta hau cin abarta.

Da ta ci ta ƙoshi ta ɗaure sauran, ta kwanta a jikin Aliyu ta hau bacci.

****
Lafiya Adam ya sauka a Abuja, ya sauka a hotel É—in da zai zauna na kwanaki biyu, dan ba ya son a san da zuwansa, shi ya sanya ya sauka a hotel, sai dai gabansa ya tsananta faÉ—uwa ya rasa dalili, ya kira Ammi ya kai sau uku, amma ta ce masa komai lafiya babu wata matsala.
Da yamma ya shirya ya ce bari ya É—an fita ya je wurin abokansa, ko ya É—an rage damuwar da ya rasa meya haddasa masa ita.
Sai dai yana fita harabar hotel ɗin, ya ji kansa ya wani sara, yayi ƙoƙarin basarwa  ya fita, amma ya kasa ƙafarsa ta yi masa nauyi ya ji yana nema ya faɗi, a hankali ya juya ya koma ɗakin da ya sauka, ya nemi wuri ya kwanta, saboda yadda yanayin jikinsa ya sauya tamkar zai fita hayyacinsa.

***
Ruma na farkawa daga baccin da ta yi, ta cewa Aliyu kashi take ji, shi kuma ya ce sai dai ta riƙe kayanta sai sun sauka, don ko zata yi hauka ba zai saka a tsaya ba, ba zai bari ma ta yi kashi a daji ba.
Ta din ga matse ƙafa tana nema ta yi masa kuka, har sai da ta fara janyo hankalin mutanen da ke motar.
"Wai kai ba ka ga yarinya bace ne? A tsaya ta yi mana" cewar É—aya daga cikin mutanen da Aliyu ya kasa yarda da su.

Aliyu ya ce "A'a ba zata yi ba, idan mun je in da zamu ta yi" ya bawa mutumin amsa yana tsuke fuska. Ai bayan batun kashi ta cigaba da kuka, ita fa zai zubo, kuma ta gaji da zaman motar nan. Kan Aliyu ya yi magana motarsu ta yi faci, a tsakiyar jeji.

Fasinjoji suka din ga tsaki suna mita, masu ruwa suka É—aura alwala kasancewar azahar ta yi, suka yi salla.

Wanda ya bawa ruma kaza ya kalli Aliyu ya ce  "Abokina tun da an tsaya gyara motar, ka shiga da ita ta samu wuri ta biya buƙata mana".

"Ɗan uwa ai na gaya maka ba abin da zata yi sai mun je, ƙyaleta ƙarya ma take ba wani kashi da zata yi"

Kowa yayi salla amma banda wannan mutanen, ana ta fafutukar sauya taya, tabbas da a gari motar nan ta lalace, da ba abin da zai hana Aliyu ya canza musu mota, saboda bai yadda da mutanen nan ba, shi ya san me ya gani, kuma yana tsoro yayi magana su cutar da su.
Aliyu yana salla, ruma ta tsaya tana ta ƙarewa dajin kallo tana ɗaukar hoto da akwalar wayarta kamar abin da ta fito yi kenan.

"ÆŠan uwanmu ku ba kwa sallar ne?" Ruma tayi maganar tana zama É—an nesa kaÉ—an da É—aya daga cikin mutanen.

Ya kalleta ya ce "Sai mun je gida zamu yi"

"To wai Meyasa kuke ta sawa ana tsayawa a hanya ne? Duk ku ka ja muka daÉ—e fa"

Ya ce "Saƙo muka karɓa a wurin 'yan uwanmu"
Chapter 50 · 0% Book details