Sashe 71
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta É—an yi shiru sannan ta ce "Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya"
Ya ce "Wallahi na yadda addu'a ki ke yi mana, ko kuma daga can gidanku ake yi, ban da haka ba a taɓa kawo ɗan iskan mutum mara tsoro irin ki ba".
"A'a nifa ba 'yar iska bace, so nake ku kasheni, amma kun ƙi ya zan yi, kalli yadda na koma kamar 'yar jari bola, wataran a gidamu mama sai ta yi mini wanka sau biyu a rana, amma yau ban san adadin kwanakin da na shafe ban yi wanka ba, tun ina warin har na daina".
"To ai ko ni ma sai na yi miki wankan, akwai kogi a gaba"
Aisha tana daga can nesa, amma ko ƙifta ido ba ta yi a kan ruma, dan kar wani abu ya faru, ruma tayi zaman dirshen sai zuba take, duk da ba ta san mai ruman take cewa ba, amma hirarta kawai take yi da su hankali kwance.
Ba ta sake bi ta kan Anty Aisha ba, har aka yi sallar asuba, ruma ta yi salla tayi kwanciyarta bacci.
***
"Mummy, wallahi na san in da maganin nan yake, a É—akin iman yake, kuma na sake tabattar da takawa yana nan da wannan ciwon mai kama da na aljanu, mai kuma kama da na hauka"
Mummy ta kalli Fauziyya a tsanake ta ce "Fauziyya, bana son shirme da ƙarya fa".
"Haba mummy, kamar wata ƙaramar yarinya, kin ga yadda ya shaƙe iman a ɗakinta kuwa, ya ɗage mata riga baki ga ba"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Kin tabattar kin ga in da maganin yake? Idan kin tabattar ina son gaya wa uwani ta kawo mini shi, dan da maganin wannan malamin yace zai mini aikin da zai kawo ƙarshen hankali a jikin adam, kin ga ba shi ba sarauta kenan"
"Wallahi mummy na gani, sai dai akwai mukulli a drower mudubinta ne"
"Fine, kafin nan, ina son ayi raising issue na cewar yayi yinƙurin yi wa iman fyaɗe, wani sashin kuma ace an kama shi shi da ita, hakan zai ƙara ɓata sunansa, da yi wa zuriyar binta baƙin jini a cikin masarautar nan"
Fauziyya ta É—an yi jimm sannan ta ce "Anya Mummy, decision É—in nan naki bai yi tsauri ba kuwa?"
"Ban gane tsauri ba, duk wannan fafutukar ba dan ku nake yi ba, ki shiga hankalinki fa"
"Am sorry, ba zan sake ba duk hukuncin da ki ka yanke dai-dai ne"
Mummy ta yi ƙwafa ta tashi ta fice.
***
Habiba ƙawar ruma kullum sai ta je layinsu ruma, ta tambaya ko an ga rumaisa, dan tsoron zuwa gidan su ruma take saboda yayyen ruma, tsoro suke bata, ita a da can ma idan ba dole ba ba zuwa take yi ba, balle yanzu da suke cikin damuwa da tashin hankali.
A ƙofar gidan su ruma take tsaye tana leƙe.
"Me ki ke dubawa ne?" Ta ji muryar usman.
Da sauri ta waiwaya tana kallonsa.
"Me ki ke yi a nan?" Ya maimaita.
Habiba ta ce"So nake na ji ko zan ji yo muryar ruma ta dawo"
Cikin sanyin jiki usman ya ce "Ruma ba ta dawo ba Habiba, na san kina yi mata addu'a, to ki cigaba kar ki daina dan Allah".
Hawaye ya cika idon habiba za ta yi kuka, usman ya ce "Kar ki yi kuka kin ji, maza tafi gida kar a neme ki kin ji"
Haka nan ta juya ta tafi gida.
***
Ruma kuwa sai da rana ta take, sannan ta tashi daga baccin da take yi,ta tashi zaune ta ɗaga kai suka yi ido huɗu da Aisha, amma rumaisa ta kawar da kanta gefe taƙi kula Aisha.
Sai dai a kallo É—ayan da ruma tayi mata, ta hango damuwa a fuskar aishan.
Gaishe da mutanen wurin tayi, ta koma gefe ta tattara duwatsu ta hau 'yar carafke.
"Sannu rumaisa, ke rayuwarki baki da wata damuwa, yau ba kya jin yunwar ne?" Cewar wanda suke kira da sha tara.
"To kun bani abincin ne?"
"Ga abinci nan barde ya kawo miki kina bacci"
"Nifa na gaji da buredin nan ba yau ba gobe... Au ashe waina ce yau" tayi maganar tana murmushi, yayin da mutane suke kallon tsabar samun wuri da ruma ta yi.
Ta koma gefe da nufin ta fara ci, suka yi ido huÉ—u da Aisha ta zubo mata ido,haka nan ruma ta ji jikinta yayi sanyi, dan haka ta tashi ta je gaban Aisha ta zauna ta ce "zo mu ci"
Aisha taƙi magana, kawai ta zubawa ruma ido.
"Mu ci mana" ruma ta sake maganar tana kallon idon aisha, amma ga mamakinta taga hawaye a kwance a cikin idonta.
"To Meyasa kuma zaki yi kuka?" Ruma tayi maganar kamar ita ma ta yi kukan.
"Meyasa ki ke fushi da ni ruma? Na ji daɗin kwanciyar da na yi a kan ƙafafuwanki, har na ji ina son yin bacci, amma ki ka tashi ki ka barni" tayi maganar cikin damuwa.
Ita ma ruma cikin damuwar ta ce "Ba ke ce ki ke cewa zaki mutu ba, na gaya miki kuma bana so".
"To na daina, amma ki matso kusa da ni in kwanta a kan ƙafarki, ko zan ɗan ji daɗin kwanciyar, kwana na yi ina ciwon baya da ciwon mara, ƙafafuwana kamar ana sara mini su"
"To mu ci wainar, sai ki kwanta"
Ta girgiza wa ruma kai, ta karkata da ƙyar ta kwanta a kan cinyar ruma, sannan ta kalli ruma ta ce "Har na ji daɗi, mu daina faɗa dan Allah ƙawata, gurin nan yana bani tsoro, da sakani cikin damuwa ke kaɗaice ƙwarin gwiwata, idan na ganki nake jin daɗi, kuma ko ina cikin damuwar barkwancinki na sakani nishaɗi".
Murmushi ruma ta yi ta ce "Ni wallahi idan ki ka ce baby ruman nan, sai na ji kamar na fara rarrafe da shan hannu, kamar wata jaririyar zanin goyo, wai da mama baby take ce mini da har a yanzu sai na din ga fitsari a wando, zan zuba taɓar wallahi".
Cikin dariya Aisha ta ce "Ki gauraya da mai sunan baba ba" tare suka cigaba da dariya, kamar babu abin da yake damunsu duk su biyun. Can aisha ta ce "Wai ina É—an kunnenki, na ga kunnenki babu yari".
Ruma ta haÉ—iye lomar wainar da ke bakinta ta ce "Ai ni ina ga sai salla salla nake saka É—an kunne, nifa kamar su Huzaifa haka nake yawona, dan da za a barni, zan iya yawo da gajeren wando a cikin unguwa, in je ayi mini askina"
Aisha ta girgiza kai ta ce "Ruma idan na biye miki, sai ki saka na fara naƙuda yanzu" ta saka hannu ta ciro ɗan kunnayen kunnenta, ta sakawa ruma.
Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni fa bana son É—an kunne, idan suka dameni tsaf zan ciresu na watsar"
"Ruma kin san kuÉ—in abin da na saka miki a kunnenki kuwa? Gold ne tafiyayye daga dubai, dan Allah kar ki yar".
"To ni me zan da shi?" Ruma ta tambaye ta tana shafa kunnenta.
"Bar miki na yi, ga wannan ma, ta miƙawa ruma ɗan kwalin kayanta, ta ƙulle wani abu a ciki ta ce "Sarƙar ɗan kunnen ce, da zobuna da kuma sarƙar ƙafa".
"To su kuma me za ayi da su?" Aisha ta ɗan yi shiru, daga bisani kuma ta ce "Ajiya ce na baki, zan karɓa, idan kuma ban karɓa ba na bar miki"
"To ni yanzu wannan ajiyar taki, a kaina zan ɗaurata ko kuma ƙuguna zan ɗaurawa, dan tsaf zan manta ya kama gabansa na kama nawa"
"Amana ce fa, ki kula da su sosai" ruma ta takurawa aisha sai da ta ɗan ci wainar nan, amma kallo ɗaya zaka yi wa aisha ka san bata da lafiya, amma sai ƙarfin hali take tana biyewa rumaisa.
A 'yan kwanakin nan kusan kullum, akwai kalar mutanen da suke zuwa wurin nan, wasu idan sun zo su É—auki manyan jakunkuna.
Yau ma wasu ne suka zo a babura kusan huɗu, amma su waɗan nan sanye da baƙaƙen coat, suma fuskokinsu a rufe, ruma ba ta damu da su ba, ta mayar da hankalinta kan aisha, tana fatan kar ƙarar baburan nan nasu ya tasheta.
Bayan mutanen sun tattauna da waÉ—anda suka sace ruma, kai tsaye aka nuno musu in da su ruma ke zaune, suka tunkari su rumaisa.
Tsayawa ruma ta yi taga ikon Allah,wurin wa aka zo, wurinta ko kuma wurin Aisha....
Ayshercool
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYARÂ DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*