Sashe 152
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Usman ya ce "To, wallahi ki ka dawo da kayan Abincin nan, bai ci komai ba, to tabbss rashin mutunci ki ka yi masa, kuma zaki daku" ta gyaɗa kai, ta tafi soron ta tarar da shi, ta ajiye masa kayan a gabansa ta zauna ta ce "Ga abinci nan" ya ɗago ya kalleta ya cigaba da taɓa wayarsa.
"To, ni dai zan juya maka baya, ka ci, dan ba zan yi wahalar banza ba, tun safe ake azabtar da ni a gidan nan saboda zaka zo, zan juya maka baya, ka ci idan ba zaka iya ci a gabana ba"
Ta juya masa baya, ta É—auko goruba tana ci.
A ransa ya ce "Na ga ta kaina ni Adamu, wai wannan ce matar da zan aura?"
Ta waiwayo ta ce "Wai ba zaka ci ba? To wallahi ba zaka ja mini duka ba.
Ta ɗauki coca-cola, ta tsiyaya a kofi, ta shiga hijjabinta ta sha, ta buɗe meat pie, ta ɗauki ɗaya, ta shiga hijjabinta ta ci, ta gutsuri wani ta ajiye ta ce "Yauwwa, dan ba zaka ja mini duka ba, an ce idan har na koma da shi ba ka ci ba, yaya usy zane ni zai yi"
Adam ya zubawa sarautar Allah ido, ita a rayuwarta ba ta san kara ba, idan ana neman mutum kai tsaye da ba ya rufi, to kowa ya bi bayanta.
Kamar wadda ta ci wani abun maye, ta takure abun ta, ta haÉ—a kai da gwiwa ta hau bacci, shi dai ikon Allah kawai yake kallo, wannan zance ya zo, ko kallon drama.
Ya mayar da hankali kan wayarsa, yana dannawa.
Usman da yake kaiwa yana komowa ya ce "Kai shirun nan yayi yawa, bari na duba"
Wata irin razana rumaisa ta yi "Iman!" Ta faɗa da ƙarfi, tare da faɗawa jikin Adam gaba ɗaya jikinta yana rawa, hakan yayi dai-dai da shigowar su Usman cikin rige-rige, domin ganin abun da yake faruwa, saboda ihunta da suka ji.
Ayshercool.
08081012143*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
Bayan motar ta shiga suka tafi, sai da suka kai ta gida sannan suka wuce.
Ko da mai sunan baba ya koma gida, mama ya tarar a É—aki tana rungume da rumaisa, tana ta rarrashin ta, su Aliyu duk sun zauna sun yi jugum suna kallonsu.
Ƴan uwa sai bawa rumaisa haƙuri suke yi.
"Meye haka?" Ya faÉ—a a kausashe.
Gwaggo ta ce "Ka san lamarin aure, dole za ta ji babu daÉ—i za ta yi kewar mahaifiyarta, kuka take yi"
"Saboda shirme, ku kuma ku ka zo ku ka sakasu a gaba babu mai tsawatar mata? Tana fama da tension da hayaniya na biki, ke kuma kin zo kin sakata a gaba kina kuka? Da wanne za ta ji? Tashi ki cire wannan kayan, ki yi wanka ki nemi wurin kwanciya"
Mama kasa cewa komai ta yi, rumaisa ta tashi tana kuka, ta shiga uwar É—akan mama.
Su usman daurewa kawai suke yi, dan gaba É—aya jikinsu yayi sanyi da suka ga tana kuka, ba su ba shi kansa gogan jikinsa a sanyaye yake.
***
Samha har ta gaji da kuka, kowa da irin shawarar da yake bata, ta banza da ta arziki, tana kwance a kan gadonta ta yi rigingine, tana tunanin yadda za ta aiwatar da malamin da suke zuwa wurinsa ya bata, dan ta yi alwashin raba Adam da kowane irin farin ciki, in dai abun da ya shafi aure ne.
Ba ta san a karo na nawa wayarta ta yi ringing ba, cika mata kunnuwan da wayar ta yi ne ya sanya ta É—aga, ta saka a kunnenta ba tare da duba ko waye ba.
"Babbar yarinya, ashe abun da ya faru kenan, yayanki zai angwance da wata ba ke ba?"
"Murna ka kira ni ka yi mini, ko kuma ci mini mutunci?"
"Babu É—aya, jaje kawai na kira na yi miki, tare da mamakin abun da zai saka Adam kawar da kai a kan cikakkiyar mace mai aji kamar ki Samha, ban da so makaho ne, tuntuni nake jaddada miki, ki rufe ido a kan wannan son, mu yi duk mai yiwuwa mu ga bayan adam, amma ki ka dage a kan cewar ke ba za a cutar da shi ba, ai kina son sa, yanzu son wace ranar yayi miki?"
A hasale Samha ta ce 'Look wakili, i don't have time, for all this now allow to rest"
Khalifa ya ce "Ba ki da wani hutu samha, lokaci ne kuma zai cigaba da ƙure miki, kan ki farga yayi miki nisan da ko tafin ƙafarsa ba zaki hango ba, let's join hands together"
Kashe wayar ta yi ta ajiye, tare da faÉ—in "Shashasha kawai".
Iman ita kaÉ—ai a É—akinta, ta yi wanka ta sauya kaya, sai dai ta kasa manta fuskar mai sunan baba, yau yayi kyau sosai, sai dai yanayin muzuransa ko tunawa ta yi sai ta ji gabanta ya faÉ—i, dan har suka kawota gida, ban da kwatance, ko abokin nasa ba ta ji yana yi wa magana, balle ita ya kulata.
Æangaren mai sunan baba ma, mamaki yake yi, yadda tsoronsa ke bayyana sosai a kan fuskar iman, ya san yana da kwarjini sosai, sai dai ita ya lura ba kwarjini kawai yake yi mata ba, tsoronsa take ji, tsoro kuma ba na wasa ba. TaÉ“e baki yayi ya cigaba da sabgoginsa.
Washegari ya kama ranar da za ayi dinner, rumaisa ta tashi da ciwon kai, saboda kukan da ta sha jiya, idanunta duk sun yi ja.
Ta wuni a uwar ɗakan mama, tun ƙarfe uku yayyenta suka tafi fara nasu shirin, a ƙarfe ukun kuma, aka aiko da motar kaita wurin kwalliya.
Maƙwabta na ta mamakin wani hamshaƙin ne haka zai auri rumaisa, sai abu ake yi kamar wata babbar budurwa.
A wurin kwalliyar ma, kuka take ta yi, Habiba da su hauwwaliya suna ta rarrashin ta, amma ta ƙi tsayawa.
Mai kwalliyar ƙawar nusaiba ce, dan haka ta kirata ta sanar da ita halin da ake ciki. Nusaiba ta gaya wa takawa, ya din ga mitar shi ba ya son a tsaya wannan shafe-shafen aje a ajiye mutane su na jira.
Ƙarshe dai da kansa ya tafi wurin kwalliyar da shi da bashir.
Ya je ya tarar duk an yi wa ƙawayenta kwalliyar ban da ita.
Ya kalleta ya ce "Zaki tsaya ayi kwalliyar ne, ko kuma mu tafi a haka?".
"Ni bana son auren nan na fasa, mama ta ce wai barin gidanmu zan yi, ni na fasa" ta yi maganar cikin kuka.
Bashir ya ce "Haba rumaisa, an gama tara mutane, ki bari idan aka gama sai ayi duk maganar da za ayi".
Adam dai ya ƙule ƙarshe, Bashir ne yayi ta bata haƙuri, sannan ta tsaya aka yi.
Mai kwalliyar ce ta fito da rumaisa reception, ta yi kyau kamar ba ita ba, kayanta iri É—aya da na Adam.
Hauwwaliya har da tsalle, tana koÉ—a rumaisa.
Bashir ne ya din ga yi musu hotuna, sai dai daga ita har adam babu wanda yake walwala.
A harabar wurin bikin, suka tarar da su Aliyu, sun haÉ—e cikin shadda iri É—aya, hatta huluna da agogo iri É—aya suka saka, motar na tsayawa, ta buÉ—e ta fice ta nufi wurin su Usman.
Abdallah ya din ga É—aukar rumaisa a hoto.
Usman ya ce "Allah sarki lantarkin gidanmu, zaki tafi ki barmu a duhu, zaki barmu da É—an hasken da ba zai ishemu ba"
Rau-rau ta yi da ido, za ta yi kuka, ya girgiza mata kai ya ce "Yau ranar murna ce, da yi wa Allah godiya, ki bari mu je mu yi rawa mu ci kaji, idan an koma gidan kya yi kukan, dan kukanki ba zai hanani cin abinci ba na gaya miki"
Bisa ga al'ada, ƙawayen amarya da ƴan uwanta ne ke shigo da ita, sai dai wannan amaryar, yayyenta maza ne suka shigo da ita, ga ta ƴar mitsitsiya a gaban angon nata, kamar ƴa da uba.
Abun ba ƙaramin ƙayatar da mutane yayi ba, sai dai fa wasu surutu suka fara da raina wayon takawa, na auren ƴar mitsitsiyar yarinya.
Taken gidan sarauta aka saka wa shigowar ta su, ga maroƙa da suka biyo su suna yi musu busa, tare da kirari.
Rumaisa ta kalli yadda hall É—in ya cika, dama tun daga haraba motoci ba a magana, manyan mata masu shiga ta alfarma, gaba É—aya taga ido a kanta, ga takalmi mai tsini, take ta ji jiri na É—ibarta.
Adam ne ya fuskanci haka, dan haka ya riƙe hannunta, sai da ta ɗan waro ido, ta sake kallon mutane ta ga kowa sai ƙoƙarin ɗaukarsu a hoto yake yi, ta sake sunkuyar da kanta a cikin mayafi, tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Adam amma ya riƙeta sosai.
Har kan high table suka raka rumaisa, suka zaunar da ita, kowa ya gansu sai ya ce Masha Allah, tare da jinjina rumaisa a matsayin ƙanwar zaratan maza har bakwai.
Iman ce ta fito stage, ta karɓi mic, tare da gabatar da addu'a, da fatan alkhairi ga amarya da ango.
Jabir ba ƙaramin mamaki ya yi ba, ganin rumaisa ita ce matar da takawa zai aura, ya din ga tunanin yaya aka yi hakan ta kasance bai sani ba?. Me Adam zai yi da wannan yarinyar ƴar talakawa mara kunya.
Sai da aka yi kamu, kan a fara gabatar da dinner, duk wani abu da ƙawayen amarya za su yi, yayyen rumaisa ne suka yi shi.
Dangin su Adam sun so su farfaɗi maganganu, da yin rashin mutunci a wurin, mussaman da kusan kowa ya san Samha tana son shi bai aureta ba, amma kasancewar su Abubakar da mai sunan bab a wurin, suka cika wa mutane ido, kowa ya riƙe gulmarsa.