Sashe 159
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a É—auko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata".
Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faÉ—i, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.
Ayshercool
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please ðŸ™
Adam yayi ta maza ya ce "Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai".
Cikin matsanancin takaici ta ce "Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni É—in ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi".
Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faÉ—a.
"Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wulaƙanta ni, ka ƙi ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?"
"To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?" Rumaisa ta yi maganar tana riƙe ƙugunta.
Adam ya kalli rumaisa ya ce "Wuce ki je mota ki jirani"
"To saman motar zan hau ko ƙarƙashin tayoyi? Tun da a rufe take".
"Duk in da ya yi miki" kallon banza ta yi wa samha ta wuce.
Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ƙwaila ce ta gaske.
"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne".
"Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam".
Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai muƙadarri ne na Allah. Daga haɗuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ƙaddarar Allah ce".
"Ba ka son ta kenan?"
"Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a'a ba, ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi haƙuri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha".
Rumaisa kuwa ranta a ɓace, ta ƙarasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci.
Jamil ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaɓa ya bar Samha? Saboda wannan abar?".
Jabir ya ce "Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faÉ—i fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya"
Zabura Jamil ya yi ya ce "Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?".
Jabir ya ce "Tambayeta ka ji"
Juya musu ƙeya rumaisa ta yi, tana wasa da ƙasa da ƙafarta.
"Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun Æ´an bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?" Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A'isha ta rasu.
ÆŠaga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki.
"Magana nake yi miki, aisha ƙanwata ce, jami'in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ƙarya ne kawai haɗin baki ne?" Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka.
Sheƙeƙe rumaisa ta ce "To mijinta ma shi Adam ɗin ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na ɗauka ma babar wasu ce".
Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya riƙe hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana.
Adam ya ƙaraso ya ce "Lafiya kuwa?"
Rumaisa ta ce "Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya".
Adam ya buÉ—e motar, ya ce wa rumaisa "Shiga ki jirani"
BuÉ—e motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki.
Adam ya kalli Jamil ya ce "Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karɓi ƙaddara ba, ka ƙi halartar ɗaurin aurena, kuma ka ƙi yi mini Allah ya sanya alkhairi".
"Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?" Yayi maganar yana nuna motar adam.
Adam ya sauke hannun Jamil ya ce "Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu".
Jamil ya ce "Adam ka na da ƙwarin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun 'yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuɓuta, wani mataki ka ɗauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na ɓoye mana?".
Nan da nan Adam ya hasala ya ce "Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da buƙatar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki".
Cikin sauri Jabir ya ce "Jamil, bai kamata ka faɗi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi haƙuri"
Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buÉ—e ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi.
Sai da suka É—an yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?.
"Su wa?" Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce "Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba"
Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tuƙinsa.
Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin.
Suka je ɓangaren jakunkuna ya ce ta zaɓi jakar makaranta.
Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so.
Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi.
Gidajen ƴan uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ƙule da yadda wasu suke karɓarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ƙarama da aure.
Babu wanda ya sake ƙona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu.
Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa'ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba.
"Ragowar Æ´an bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka".
Adam ya ce "Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye É—anku, amma ta amince da aurensa".
Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Yo ba dole ba, ai ko a turu kake É—an mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaÉ—ayin abun duniya ne kawai".
Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa.
Adam ya ce "To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je".
"Ahh haba dai, na saka a É—ora muku girki ai".
"A'a Alhamdilillah, a ƙoshe muke".
Hajiya Lubabatu ta ce "Gaskiya ban ji daÉ—in wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba".
Adam ya ce "Bakomai ana koya mata"
Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ƙaraso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karɓa ta miƙawa rumaisa ta ce "Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ƙyalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala".
Rumaisa ta sha kunu, ta ƙi karɓar ledar.
"Ki karɓa mana" rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a"
Hajiya Lubabatu ta ce "Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a'a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce".
Ya kalli rumaisa da ke kusa da shi ya ce "Ki karɓa, ba a mayar da kyautar matan sarakai".
"Bana so" ta faÉ—a yadda shi kawai zai ji.