← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 174

Sashe 28

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannu a hankali yake danna system ɗin da ke gabansa, kamar ya na tausayaa mata, hannunsa ɗaya kuma riƙe da cup ya na shan tea, idan ba ka kalleshi sosai ba, zaka ɗauka Mahmud ne a zaune.
Muryarta ce take dawo masa kunnesa, kamar a yanzu take magana *laa sarki ne wannan? Sarki ka juyo ka kalleni* ya tuna ƙarfin hali da ta dubi ɗaya daga dogarinsa, ta ce masa bawa, koma dai wacece a muryarta ya ji akwai yarinta da kuma tsananin tsaurin ido, idan sarkin ne shi a haka zata yi masa magana kenan, ba girmamawa?
Iman ce ta fito daga sashin Ammi, hakan ya kaste masa tunaninsa, ta ƙaraso falon ta zauna, ta kalle shi ta ce "Barka da hutawa ranka ya daɗe" tun ɗazu Nusaiba take falon, tun da suka gaisa ta ja bakinta ta tsuke, ta kasa ce masa komai, shi ma kuma bai kulata ba, amma Iman na fitowa ya yi murmushi.

"Barkanki dai auta ta Ammi, kin tashi kenan?" Ta jinjina masa kai sannan ta ce "Once again Ya hanya, ya kuma ibada?"
"Alhamdilillah, ya karatun?"

"Ina nan ina ta yi Yaya, ka yi mini Addu'a kuwa da ka je?"

Ya jinjina kai ya ce mata "Sosai, ban yiwa kai na Addu'a da na yi miki ba, na so mu tafi tare da ke, amma na san Ammi ba lallai ta yadda, sai dai ku je umarar azumi ke da ita"

Iman ta yi murmushi ta ce "Nima ina yi maka addu'a sosai yaya, Allah ya kawo abin da Ammi take ta fata"

Nusaiba ta jinjina kai, da wani ne ya tsare Yaya da wannan maganar da ya shiga uku, to wa ma ya ga fuskar hakan, ai sai Iman É—in.

"Iman, ai kuma zaku iya samarwa Ami abin da take burin, ku fito mana da tsayayyu, a wuce wurin kawai"

Iman ta É—an rausayar da kai ta ce "Sai dai Anty Nusaiba, amma ni dai kam sai a hankali " tayi maganar jiki a sanyaye.

Alama ya yi mata da hannu da ta zo.
Ta tashi ta tafi in da yake ta zauna, ya matsa kusa da ita, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Na ji abin da ya faru lokacin ina Saudiyya, abin bai yi mini daɗi ba sam, da Ammi ta yi shawara da ni, ba za ta yanke wannan hukuncin ba, ai Allah ke da rayuwar kowanne bawa. Ki ɗau abin da ya faru a matsayin Mafi alkhairi, Allah ya tanadar miki mafi alkhairi, ni kai na example ne a gareki, dan haka mu cigaba da Addu'a gaba ɗaya" ta jinjina masa kai ta na share hawaye.

*******
Usman ne a zaune ya gama cin abinci, ya kalli Abdallah ya ce "Kai ka san wani hau da wannan Anas É—in yayi mini yau?"

Abdallah ya ce "Sai ka faÉ—a"

"Wai ni zai tara ya ce mini ya na son ruma, yarinyar da ko ciwon kan ta ba ta sani ba, ni kuwa na ci ubansa, sai kaÉ—an na kikkifa masa mari"

Abdallah ya yi dariya ya ce "Ba abokin ka bane ba, na ga filin ball É—in ku É—aya ma"

"Dan abokina ne, sai ya ce yana son ƙanwata, mahaukacin ina ne shi?"

"Amma wallahi yaya Usy ba ka kyauta mini ba, 'yan ajinmu na Islamiyya su yi ta labarin saurayi, ni kuma ba ni da saurayi, duk wadda ba ta da saurayi fa wai baƙin jini ne da ita, sai an kai ta wurin malamai sun yi mata Addu'a "

Abdallah ya ce "Saurayin uban wa? Ke ya zaki yi da wani saurayi, ko yake shi Anas É—in ne ma mara hankali, shi ma irinki ne ai mara kan gado perfect match"

ÆŠan saroro ta yi ta ce "Wai Anas É—in gidan mai taya?"

Abdallah ya ce "Ƙwarai kuwa"

Ta ce "Taɓ, Astagfirullah Allah ba irin wannan ba, kenan addu'a ta ba ta karɓu ba, ina ta Addu'a Allah ya bani saurayi mai kyau, mai kuɗi, mai ƙarfi sosai wanda zai din ga goyani kamar girman brownstrawman na wrestling, kawai sai wani Anas ya ce yana so na, wata uwar ƙeyarsa kamar sirdin keken baban su Ade, gashi siriri da kaɗan ya fi taliya. Ina ga sai na ƙara dagewa da Addu'a ".

Usman ya ce"Ke, kina halitta ne da zaki din ga kushe wasu? Kin ga ki shiga hankalinki, ba ke ce baki da kamun kai ba, dole kowa ma ya ce zai ce yana son ki, kuma wallahi idan ba ki shiga hankalinki ba, sai na bashi ke"

"Allah ya kiyaye, wallahi ba zan aure shi ba, gashi baƙi ƙirin kamar an rina shi".

"Ke zan ci ubanki na kuma jin kina kunshewa wani halitta, ke kyan ne da ke. Ni kullum fatana Allah ya baki miji na gari ko ya fi biri muni" mama ta yi maganar a hasale.

"Mama biri kuma, ba amin ba gaskiya, dan Allah idan irin wannan addu'a ki yi mini ki daina, ni wallahi kyakykyawa na ke so"

"Kyan banza da na wofi, kyan É—an maciji ki auri kyan ya din ga gasaki ba gara mummuna na gari ba"

Ruma kamar za ta yi kuka ta ce "Ina wani abin arziki a muni"

Mama ta hau ruma da faÉ—a, ruma ta yi shiru, amma a duk sa'ar da mama ta ce Allah ya bata miji nagari duk muninsa a zuciyarta za ta ce ba Amin ba.

Yau ruma Alla-Alla take gari ya waye, sai murmushi take ita kaÉ—ai.

Yasir ne ya lura da ta na fara'a, dan haka ya ce "Wai ke murmushin me ki ke yi ne haka?"
Ta gyara zama ta ce "Ka san tun da na shiga sakandare, ban yi faɗa da kowa ba, so nake na zama 'yan mata, in din ga tsayawa a cacar baki, to ni cacar baki ba ta biya mini buƙata, na fi son na haɗawa yarinya malaman jikinta, muka yi faɗa da wata yarinya, ka san ni ba na zagi, ta dinga zagina in gaya maka, amma ban yi kuka ba.
Kawai yau na ga babarta ta zo makarantar mu, da ƙyar ta shiga ofishin principal saboda girmanta, ina ga ta yi rabin bangon ɗakin mama.
Kai ina ga fa ta yi yakuzuna na jikin receiver girma, koma ta fishi, shi ya sa nake son Allah ya kaimu gobe, za ta gane ba ta da wayo, ba dai har da cewa babata tsohuwa ba ce, wallahi a jikin allo zan zana babarsu.

Ayshercool
08081012143
[19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.

14

Buɗe baki Abdallah ya yi ya na kallon ruma, bil haƙƙi take maganar har cikin zuciyarta.

"Ke fa hankali bai wadaci ƙaramar ƙwaƙwalwarki ba, sai ki je allo ki zana babar wasu, idan aka zana taki zaki ji daɗi?"

"Ai ni na yi alƙawarin na daina dambe, ta zageni na kasa ramawa, saboda ashar take yi, ni kuma bana zagi, gaba ɗaya ta cuceni ta ɓata mini rai, ni kuwa ba ta san ba a taɓani a ci bulus ba, wallahi sai ta gane kurenta"

Abdallah ya girgiza kai ya ce "No, ki nemi wata hanyar dai, amma ban da iyaye, ba abin wasa bane"

"Iyaye ba abin wasa bane, ta ce mini mara tarbiyya babata tsohuwa, sai na ci buhun ubanta, ranar ma a sanyi ta sameni, da sai na tayar mata da aljanu na yi mata dukan tsiya, to bana som daga shigata makarantar a tsaneni ne, ayi mini mummunar shaida". Duk yadda Abdallah ya so nusar da ruma, ta yi biris ta ƙi fahimta ta yi alwashin ramuwar gayya a kan abin da aka yi mata.

*****
Nasihar da takawa yake yi mata, a hankali ta ji ta ratsata sosai da sosai, daga ita har shi suna fuskantar jarrabawa daban-daban, wanda hakan yake jefa Ammi cikin damuwa.

Nusaiba ta kalli Takawa da Iman ta ce "Iman 'yar gidan yaya, Ammi ta ki yayan ma naki"
Murmushi iman ta yi tana sake gyara zamanta.

Turo ƙofar falon aka yi, suka ɗaga kai gaba ɗayansu suka kalli ƙofar. Jabir ne ya shigo, da sallama a bakinsa. Suka amsa masa gaba ɗaya, hankalinsa ya na kan Iman ya na ƙare mata kallo. Hakan ya sanya ta haɗe rai tana ɗan kawar da kai gefe.

Yayi murmushi ya kalli Adam ya ce "Ni zaka yiwa haka, ka dawo amma sai dai na ji a gari ko ka neme ni"

Takawa yayi murmushin gefen baki ya ce "Ai idan ka san na dawo, zaka dameni ne ka sani yawo a gari, shi ya sa na yi shiru so nake sai na huta, shi ya sanya ma ban zauna a gidana ba, na yo nan"

Nusaiba ta ce "Uncle J, ina wuni?"

"Lafiya lau Nussy, Iman ba magana ne? 'yar rigima"

Ba dan ta so ba ta ce gaishe shi, gaba É—aya kwanan nan ba ta son abubuwan da Jabir yake mata, wanda ta kasa gane kan su.

Suna tsaka da hirar sai ga sallamar su Fauziyya da Ruƙayya, tare da Samha suka shigo falon.
Gaban Iman ya faÉ—i da ta ga Samha, musamman wani irin kallo da take bin ta da shi, da Iman É—in ta kasa gane wane irin kallo ne.
Jabir suka fara gaisarwa, sannan cikin girmamawa suka gaida Takawa. Cikin halinsa na ko in kula da kuma tsare gida ya amsa musu.

Fauziyya ce ta gyara zama ta ce "Yaya ashe ka dawo, bamu san ka dawo ba, sai É—azu Mummy ta ce mana, ai ka dawo"

"Eh na dawo" ya faɗa a taƙaice.

"Masha Allah, ya ibada?"

Ya amsa da "Alhamdilillah"

"To Allah ya sa an yi karɓaɓiyya".
Chapter 28 · 0% Book details