Sashe 15
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa, balle ya kare kansa.
An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ɓata masa jiki da ruwa da ƙasa a gogaggen uniform ɗin sa, ta haɗa hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.
Da ƙyar wani malami ya ɓanɓareta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba.
Malamin ya dubi ruma ya ce "Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?"
Cikin kuka ta ce "Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba". Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa.
Yayin da hankalin ɗaliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta duƙunƙuna masa kamar ya faɗa taɓo.
Haƙuri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa.
Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba kaÉ—an ba.
Auwal ɗan ajin su Yasir ne, ya san ƙanwar yasir ce, sai dai sam bai taɓa shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a durƙushe a wurin ba, yayi mamakin ƙarfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.
Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, haƙuri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ƙyale ruma ba sai ya ɗau mataki a kanta.
Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal haƙuri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi haƙuri.
Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ɗin ma tsoron taɓata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.
*********
Gaba ɗaya ruma ba ta wani ɗokin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ƙara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama taƙi sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ƙin jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci.
Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.
"Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?"
Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce "Na gaya maka bana son sunan amma ka ƙi daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji"
Huzaifa ya ce "Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ɓarar da ke ba".
"Hmm haƙuri halin abin ƙaunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba" girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ɗakin mama.
Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.
Mama ta dubi ruma ta ce "Murmushin me ki ke yi ne?"
Ruma ta ɗagowa mama takarda ta ce "Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ƙarfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ɗin nan ɗari biyu da hamsin, zamu yi mu da 'yan wata makaranta"
"Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ƙarfi ko kunya ba ki ji ba" Abdallah ya faɗa a hasale.
"To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba" tayi maganar cikin taɓara.
Mama ta ce "amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?"
Ruma ta tsuke fuska ta ce "Wato mama ke ma dai daƙiƙiyar zaki ce mini ko?"
Abdallah ya ce "To mecece idan ba daƙiƙiyar ba" gaba ɗaya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi.
Babu wanda ya bata ƙwarin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.
Zaune yake a cikin chemist É—in, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist É—in ta ce "Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai" na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana É—aga kai suka haÉ—a ido.
Murmushi ta yi masa ta ce "Yaya auwal ina wuni" juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.
"Baka da lafiya ne?" Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ɗin yake zuƙewa.
A hankali ya ce "lafiya lau, ya su yasir?"
"Suna nan lafiya, ya jiki?"
Da sauƙi ya bata amsa, yana tuna yadda ta damalmala masa kaya a islamiyya, da yadda yayanta ya rutsata ta bashi haƙuri amma ta ce sai dai ya mutu, ba zata bayar ba, idan suka haɗu a makaranta, sai ta tsaya ta harare shi, har da murguɗa baki, amma wai yau take gaishe shi, har da su yaya bayan ko yayan nata yasir ba ta ce masa yaya.
"Deluwa wannan hamsin ɗin taki za ta karɓuwa kuwa?" Cewar mai chemist.
"Awaisu mai chemist, duk ranar da na tashi jajjaga maka rashin mutunci, a kan kirana da deluwa, sai ka yi kuka" ta faÉ—a very serious.
Dariya ya yi ya ce "Ke, ai ko ban kai sa'an 'yan biyun gidanku ba, na san na girmi Aliyu, amma ni zaki saka kuka?"
"To shikenan, ka cigaba zaka gani, bani maganina na tafi"
Bayan ya bata maganin ta kalli auwal ta ce "Yaya auwal, Allah ya ƙara lafiya" tana gama maganar ya fita tana tsalle kamar kwaɗuwa.
Tun da ga ranar da suka haÉ—u da auwal a chemist, kullum ta ganshi a makaranta sai ta gaishe shi, duk da baya sakar mata fuska idan zai amsa, amma bai sanya ta daina ba.
****
Ɗaya ga watan ramadan, bayan gari ya ɗauka an ga wata, mutane na ta shirin ɗaukar azumi, da asuba mama ta tashi kowa sahur, amma da ƙyar ruma ta tashi ta yi sahur, saboda nauyin bacci.
Ranar ɗaya ga azumin ya kama asabar ce, ruma ta ce gaskiya ba zata iya zuwa islamiyya ba, tun ƙarfe goma take jin kamar zata mutu.
Wajen ƙarfe sha biyu na rana, ta dinga yiwa mama kuka tana burgima wai hanjinta na gutsutstsurewa ita fa mutuwa zata yi.
Aliyu ya ce 'mama dan Allah ki ƙyake yarinyar nan, tun da ba zata yi ba ta je ta ƙarata".
"Aikuwa sai ta yi, idan ya wajaba a kan ta wa zai mata?"
"Mama ki bari ua wajaban sai ta yi, kalli fa kamar zata rasu"
Mama ta ce ruma ba zata karya azumi ba, mama tana can tana salla, ya kandamowa ruma ruwa ta sha ta karya azumi.
Sai da mama tayi kamar ta zane Aliyu dan takaici, a ganinta sangartar ruma ta yi yawa.
Abu kamar wasa, ruma taƙi yin azumi, idan ma ta ɗauka ta ji wuya, sai ta karya abin ta, idan aka sha ruwa kuwa tafi uban kowa zaƙewa, daƙyar ska samu ta yi shida, shima Usman ya ce bai yarda da ingancinsu ba. idan aka ce ta je sallar asham kuwa sai ta ce ita wallahi gajiya taje yi da tsaiwa, ƙafafuwanta sai sun fara suɗewa ake ruku'u, nan ma sai bayanta ya kusa karyewa ake ɗagowa ba zata iya ba. mama kuwa ta gaji ta kamata ta zaneta da mafici.
Idan kuwa aka matsa ta je sallar asham, wataran a can cikin yara ake tsintowa mama ruma tana tsalle -tsalle ko dambe a maimakon salla, tilas mama ta hanata zuwa take titsiyeta su yi a gida.
Sai da salla ta gabato, ruma ta sake da tabattar da mama ba zata yi mata wani É—inkin ba, ta dinga yi wa mama magiya, a kan ta yi mata wasu kayan, amma mama ta ce ba zata yi ba, lokaci ne da zata rama rashin jin da ruman take yi mata.
Gaba daya É—okin sallar ya fita daga kanta, saboda ba ta son kayan da aka sai mata, gashi sallar bana ko arzikin takalmi da jaka bata samu ba, dan haka ta ce ba zata yi ko kitson salla ba.
Mama ta bata kuÉ—i ta ce taje ayi mata lalle, dan ba zata yi salla haka ba.
Ruma ta tafi ƙunshi tun safe, sai bayan la'asar ta dawo.
Mama ta kalli lallen nan babu kyan gani, kamar ana saka shi aka É—auraye.
Kafin mama tayi magana mai lallai ta kira mama, suka gaisa.
Mai lalle ta ce "Mama, wallahi kar ki ga lallen ruma bai yi kyau ba, ana saka mata wai sai an cire ba ta so ta gaji, da na ƙi cire mata, ta cire abinta wai kashi take ji"
Mama ta ce "To shikenan, kar ki damu na gode sosai" ta kalli in da ruma ta tsaya ta ci magani kawai ta jinjina kai ba ta ce mata komai ba.
Tun magariba, ruma taga mama ta kwaɓa lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.
Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yinƙura zata tashi, ta ji motsin leda a ƙafarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ƙafarta duk leda.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama me ya sameni?"
"A ina?"
"Wannan ledar mecece?"