← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 174

Sashe 43

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Yasir ya bata wayar nan, aka samu sauƙin neman magana a cikin gida, kusan koda yaushe tana kan wannan jagwal ɗin wayar, kuma Yasir abubuwan karatu yayi mata following, dan haka su tafi gani, kuma sosai suke ɗauke mata hankali, ya fi bata da daddare idan ya tabattar ta gama ayyukanta, da assignment, sai ya bata ta zauna a kusa da shi ta kalla, da lokacin kwanciya ya yi ya ƙwace wayar ya korata ta kwanta.

***
Zuwa la'asar Ammi ta É—an samu nutsuwa, sai dai kallo É—aya zaka yi mata ka san tana cikin damuwa.
Takawa ya fuskanci damuwa ƙarara a fuskar ta, sai dai ganin yadda take basarwa ba ta son magana, ya sanya shi yin shiru bai yi ƙoƙarin tilasta mata jin abin da yake damunta ba.

Wurin Jabir ya tafi, domin samun sauƙin wasu damuwoyin da suke damunsa, kasancewar sa ɗan uwa ɗaya tilo da ya fi yarda da shi.
Jabir na ganinsa ya ce "Sarkin matsala, tun kafin ka yi magana, fuskarka ta nuna akwai damuwa, yau kuma menene?"

Takawa ya É—an yi shiru, sannan ya ce "Khalifa Usman wakili"

Jabir ya tsuke fuska ya ce "Ba zaka rabu da sabgar wannan yaron da ahalinsa ba ko?"

A hankali Adam ya É—an lumshe idonsa, ba ya son yin dogon jawabi da ga Jabir, tun da shi jabir haryanzu ya kasa gane abin da yake nufi game da khalifa, dan haka kawai yayi shiru ya cigaba da tunani.

"Ina Ammi?"

Adam ya buÉ—e idonsa ya kalli jabir, amma bai yi magana ba, so yake yayi masa zancen muryar nan da yake ji, wadda haryanzu ya kasa daina jinta a kunnuwansa, amma ya san da ya É—ago zancen Jabir zai yi masa wata fassarar. Bai gama fahimtar mai Jabir ya cigaba da cewa ba, sai jin sunan Iman da yayi Jabir ya furta.

Ya ce "Me ka ce ne?"

"Ni fa matsalata da kai wulaƙanci, duk surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?"

"Sorry" ya faɗa a taƙaice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.

Jabir ya ce "Well, cewa na yi, wai me ƙaninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa"

"And so...?"

"Kana nufin ba ka damu ba kenan?"

"Kaga ni ka ƙyaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ɗaya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan ".

Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana".

Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce "Ba ka da hankali ne?"

"Ban gane ba ni da hankali ba?"

"Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?"

Jabir ya ce "Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?"

Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce "Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili".

"Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba"

A É—an hasalae takawa ya ce "A ganinka ba"

"Amma....." Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.

****

Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ƙuli-ƙuli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ƙara samun ƙwarin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar kuɗin data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ƙawayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ɗaukar ta mama.
Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.

Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar kuɗi ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ɗan abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ƙarfi.
Ga kuɗin saukar su Yasir, ga kuɗin Necon su, dan dai suma yaran suna da ƙoƙarin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar  ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.
Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu kuÉ—i kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon É—inki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.
Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.

Wata yarinya ce sa'ar ruma, sai kuma wata 'yar budurwa suka yi sallamar.

Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ƙuyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.

Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.

Zumbur ruma ta miƙe, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ƙawaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ya kawo su ba.

'yar babbar ta ce "Kuɗin da ƙanwata take bin ruma, muka zo karɓa".

Cikin mamaki Mama ta ce "wane kuÉ—i kuma?"

Yarinyar ta ce "Ranar an aiki ƙanwata, suka haɗu da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ɗari biyu ta bawa wani  tsoho almajiri, wai  ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata kuɗin kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da kuɗinta"

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita ruman? Uban waye ya ce ki karɓar musu kuɗi kiyi sadaka da su?"

"Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da kuÉ—inki zaki yi mini faÉ—a, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce"

"Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce É—auko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da kuÉ—in uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?"

Abdallah ya ce "Wallahi mama yarinyar nan da ƙyar idan ba ta da taɓin hankali".

Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ƙifta ido take kamar an kwashewa karya 'ya'ya, gefe ɗaya kuma tana hararar yaran.
Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka haÉ—u sai ta yankata.
gashi yau Mama ba ta da wani kuÉ—in kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira É—ari biyu ba dalili.

Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira É—ari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce "zo ki É—auka"

Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi É—aukar kuÉ—in, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.

Har ta durƙusa ta ɗau ɗarin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta dakata da ɗaukar kuɗin.

"Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron kuÉ—in babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci"

Jiki na rawa ta ce "Idan ban bata ba zata iya dukana"

"Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ƙarfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ƙara, da ku da ita zan haɗa na zane, ɗauki ki tashi ki bani wuri"
Kamar mai shirin ɗauko wani abu a wuta, haka ta miƙa hannu ta ɗauko kuɗin, ta tashi suka fice da sauri.

"Ke kuma zo nan" yayi ya yana kallon inda ruma take.
Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta durƙusa.

Ya ƙare mata kallo ya ce 'har kin manta sharaɗinmu ko?" Ta girgiza kai.

"Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo kuÉ—ina da na bayar ki biyani, dan ba zan É—au asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka É—auko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri" da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo kuÉ—in da zata biya shi?.

Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya jiƙa mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.

****
Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da kaɗa ƙafa.
Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta É—au wayar ta kara a kunnenta.

"Samha" ya kira sunanta a taƙaice.

"Waye?" Tayi maganar cikin ƙosawa.

"Khalifa Usman wakili"

"Wai meye haÉ—ina da kai ne? Me ka ke so kuma?"

"Easy mana, a kan maganarmu ne dai da muka fara"

Samha ta ja tsaki ta ce "Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?"
Chapter 43 · 0% Book details