Sashe 118
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka ga, kashedi zan yi maka, kar ka kuskura ka sanya Mahmud cikin shirmenka, na san ba zai wuce an ce maka baya shiri da shi da adam ba, amma ka sani har abada jini ya fi ruwa kauri, adam jininsa ne kuma ko ba jininsa bane ba, Mahmud ba irin wanda zaka yi wasa da su ba ne ka cimma burinka".
Khalifa ya yi dariya ya ce "Jini ya fi ruwa kauri, wane irin jini ne tsakanin ki adam da har ke ake wasan da ke? Ko daa yake wata kusan ta fi wata ai, and ba ke zaki gaya mini abun da yakamata na yi ba da wands ba zan yi ba, ina da abun yi yanzu, see you later" ya kashe wayar sa.
Ajiyar zuciya Samha ta yi ajiyar zuciya cike da takaicin biye wa Khalifa tun a farko.
***
Rumaisa ce zaune da wandon uniform É—in islamiyya a jikinta, sai vest tana suyar wainar fulawa ita da Abdallah.
Ta ce "Yaya Abdallah ka san me nake sha'awa?".
"A'a sai kin faɗa" yayi maganar yana zuba ƙullin wainar a kasko.
"Ina so in ji na ce basir ne da ni, ya tayar mini"
Tsaki ya ja ya ce "Mahaukaciya ba zaki yi hankali ba, kin san meye basir ciwo ne fa".
"Eh, kawai dai burgeni yake yi, idan na ji an ce ina da basir"
"Sai ki yi ta yi ai, ba ki san masifar da ke cikin sa ba, ki je ki ji da yawon gudawarki da ki ka saba ba yau ba gobe, ya fiye miki alkhairi a kan ace basir ne da ke"
Tura baki ta yi, ta saka hannu ta gutsuri gefen wainar fulawa ta saka a baki, Abdallah ya ce "Kin ci a taki"
"Ƴar wannan ɗin?"
"Eh, uban wa ya ce ki ci ba a raba ba?"
Ta miƙa hannu ta ce"To bari na cinye guda ɗayan na ci a tawa" ya buge mata hannu ya ce "Baki isa ba uwar son zuciya"
Sallama suka ji, suka amsa gaba É—aya, maman habiba ce, rumaisa ta gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska, tare da tambayarta ina mama.
Rumaisa ta ce "Mama tana cikin É—aki ki shiga"
Bayan ta shige, Abdallah ya kalli rumaisa ya ce "Ina fatan ba wani laifin ki ka aikata ba?"
"Ni ba abun da na yi".
"Wallahi idan ƙararki ta kawo sai kin daku?"
Shiru ta yi masa ta hau lasar yaji.
Maman su habiba ta ɗan daɗe, sannan ta fito, mama ta rakota sai dai fuskar mama babu walwala, ruma sai da ta ɗan tsorata ta yi zaton ko ƙarar ta ta maman su habiba ta kawo, amma bayan tafiyarta ta ji shiru mama ba ta yi mata faɗa ba.
Amma gaba É—aya maman ta sauya, damuwa sosai ta bayyana a kan fuskarta.
Rumaisa ta ce "Mama ƙarata a ka kawo miki ne? Wallahi ban yi wa kowa komai ba"
Mama ta ce "A'a ba ƙararki aka kawo ba"
"To menene, na ga ba kya son yin magana"
"Bakomai".
Gaba É—aya suka lura da yadda mama ba ta walwala, duk wanda ya tambayeta menene sai ta ce bakomai, mai sunan baba kawai ta iya gayawa abun da yake damunta.
Washegari da safe, bayan tafiyar rumaisa makaranta, jikin mama ya tashi, sai da aka kai ta asibiti likita ya dubata, sannan suka dawo gida.
Kusan kwanaki biyu kenan mama babu lafiya, babu walwala har rumaisa ta fara koke-koke.
Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ba zaki yi mini Addu'a ba sai ki sakani a gaba kina kuka?"
"To ba kin ƙi gaya mini abun da ya same ki ba?"
Mama ta ce "Ai na ce miki bakomai, amma shikenan tun da ba zaki yi mini Addu'a ba".
Rumaisa ta cigaba da kukanta, yayin da mama ta samu bacci. Wayar mama ce ta fara ringing rumaisa ta É—aga sai ta ji muryar ammi.
Suka gaisa ammi ta ce "Rumaisa ina maman taki?"
"Bacci take ba ta da lafiya"
"Subhanallah, meya sameta?"
"Taƙi gaya mini" Rumaisa ta yi maganar tana fashewa da kuka.
"Ya salam, yi haƙuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah za ta ji sauƙi, ki daina kuka kin ji ko?"
Rumaisa ta amsa da "To".
Lokacin islamiyya ya yi aka gama girki, rumaisa ta ga abincin ba nama ba kifi, ba salak, ta ƙi ci, ta je ta shanye youghurt ɗin da aka sai wa mama ta kasa sha. Ta saka uniform ta tafi islamiyya.
Da yamma ta yi suka dawo daga islamiyya, mai wanke-wanke ya kama, mai É—ora girki ya É—ora.
Rumaisa na yin sallama ta tsaya a tsakar gida ta ce "Me nake ji haka kamar warin daddawa?"
Huzaifa ya ce "Mama ce ta ce tuwo take sha'awa, shi za ayi yau".
"Taɓ mama ba ta da lafiya amma ta rasa mai za ta ci sai tuwo?"
Abdallah ya fito daga kitchen ya ce "Uban me ya hana ki cin abincin rana?"
"Abinci ba kifi ba nama, ba salak kawai tsuransa ni ba na ci"
"Iyeee ashe da gaske Huzaifa yake, É—azu mai sunan baba ya tambayi abincin waye Huzaifa ya ce naki ne kin ce ba zaki ci ba ba kifi ba nama, ya ce zai gamu da ke idan ya dawo"
"Ku dai kullum burinku ku ga mai sunan baba yana tagayyara ni, ai shikenan"
Ta shiga É—akin mama da sallama, "Mama ya jikin?"
"Da sauƙi, shi ne ki ka ƙi cin abinci ko ruma, ke idan baki samu abun da ki ke so ba ba zaki ci ba ko?"
Rumaisa ta girgiza kai ta fara cire kayanta.
Sallama aka yi mama ta amsa, rumaisa ta shiga uwar ɗakin mama da gudu, dan ta tuɓe daga ita sai phant za ta canza kaya.
Ammi ce ita da iman da Nusaiba, iman na rungume da Sabir.
A gurguje rumaisa ta canza kayan ta fito tana tsalle.
"Oyoyo yau ammi ta zo gidanmu"
Murmushi ammi ta yi tana faɗin "Ƴar gidan ammi, maman sabir"
Ta durƙusa ta gaida ammi, ta amsa mata cikin sakin fuska.
Mama ta ce "Bisimillah ku zauna"
Suka zauna su Nusaiba suka gaida mama, mama ta amsa musu cikin sakin fuska.
Ruma ta ce "Ammi ya aka yi ki ka san gidan nan?"
"Baban sabir ne ya saka yaronsa ya kawo mu, na ce bari mu zo duba mara lafiya"
Ruma ta fita da sauri, ta samu plate ta zubo musu ruwa, ta kawo musu tana ta murna.
Mama ta bi ta da kallo, ta tuna iskancin da ta yi da adam ya zo gidan.
Ammi ta ce "Ke maman sabir ya ki ka bar Æ´an maza da aikin gida?"
Ruma ta ce "Idan na yi gwaleni za su yi su ce bai fita ba, shiyasa nake bar musu aikin su. Ammi wannan wacece?" Ta yi maganar tana nuna iman.
"Ƙanwar takawa ce, ita ce ƴar autana"
"Tubarkallah mai kyau da ita" iman ta yi murmushi ta ce wa ruma "Ina wuni?"
Ruma ta zaro ido ta ce "Kai ki ka gaishe ni, ni fa yarinya ce, kin ma fini tsawo". Dariya suka yi mata ammi ta ce "Ki daina gaya musu kar su raina ki, ai kin girma tun da ke maman sabir ce" ruma ta yi dariya ta ce "Eh kuma haka ne, ai kunya na ji da ta gaishe ni".
Ammi ta ce "Yau ba zaki É—au sabir É—in ba?"
"Hmm, ai da ni na yi zuciya na ce ba zan sake É—aukar sabir ba, baki san me babansa ya yi mini ba ne"
Ammi ta ce "Subhanallah, me ya yi miki?"
"Ƙyaleshi kawai ammi, ai ba zan iya zuciya da sabir ba, a bani masoyina na ganshi" ta ɗauke shi a hannun iman, ya cika hannu, suma baƙa ƙirin ta cika masa kai. Suna cikin magana mai sunan baba ya yi sallama.
Wata irin razana iman ta yi da ya shigo É—akin, wanda ita kanta ba ta san dalilin razanar ba.
Ya risuna ya gaida ammi, sannan ya tunkari rumaisa, ya durƙusa ya riƙe mata kunne ya ce "Abinci ba kifi ba nama ba zaki ci ba ko?" Ya ajiye mata leda a gabanta ya ce "Ki kai musu su dafa miki wani abun, dan yanzu ma sai ki ce yayi sanyi ba zaki ci ba, tuwo ma ki ce ba zaki ci ba, ki yi ta wahalar da mutane babu dalili". Ta sunkuyar da kai ta ƙi magana. Ya dungurar mata da ledar ya sanya hannu ya ɗau sabir a kan cinyarta ya yi waje.
Ammi ta din ga murmushi, gaba É—aya rayuwar rumaisa burge ammi take yi.
Kifi ne manya ya kai na dubu, mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, ta tashi cikin murna ta tafi kai wa su yasir su yi mata wani girkin bisa umarnin mai sunan baba.
Ammi ta dubi mama ta ce "Amma dai kamar akwai wani abu da yake damunki, bayan rashin lafiya ma"
Mama ta ce "A'a, jinina ne ya hau"
"A tunanina zuwa yanzu mun zama ɗaya, dukkanninmu iyayene, masu fuskantar matsalar iyali kala-kala, dan Allah idan wani abu ne ke faruwa kar ki ɓoye mini ko ba zan yi wani abu a kai na yi addu'a"
Mama ta nisa ta ce "Babar ƙawar rumaisa ce ta zo, take gaya mini maƙwabtana na ta yaɗa jita-jita, wai rumaisa ciki ta yi, na kaita garinmu ta haihu, muka ce wai saceta aka yi, wai Allah ne kaɗai ya san yadda muka yi da ɗan"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, maƙwabta kuma?"
"Wallahi kuwa shi ne abun ya dameni, wai abun ya cika unguwa, sun ɓata mini sunan ƴa, na san rumaisa ba ta ji, amma ko kusa komai zaki yi wa rumaisa ba ta san hanyar lalacewa ba, balle ta yi ciki".
Ammi ta ce "Wallahi ba sai kin faɗa ba, duk wanda ya ji maganar nan ya san son rai ce, ki yi haƙuri basu isa su ɓata mata suna ba, duk wanda yake son ta da gaske jita-jita ba zata hana shi aurenta ba, ki kwantar da hankalinki kuma kar ki bari ta sani, tun da da bakinta ta ce mini duk wanda yayi mata abu sai ta rama" shigowar rumaisa ɗakin ce ya sanya ammi sauya maganar.