← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 174

Sashe 165

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To, idan kin gama, ki kwashe abincin ki je ki san yadda za ki yi da shi"

Ba ban haƙuri, ta kwashe ta fice abun ta

Ya dafe kansa, rumaisa gaba ɗayanta danger ce, yana duba nasihar ammi ne a kan yayi haƙuri da ita, duk abun da za ta yi masa, y din ga duba girman sadaukarwar, da ta yi masa. Gefe ga shawarar da bashir ya bashi kan Ya aure ta, a kan ya bi ta a hankali su saba, dan ya samu bayanan da yake son samu a wurinta, idan ya tsananta ba zai samu ba.

"Allah ka shiga lamarina" ya furta a hankali ya tashi ya bi bayanta.

Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce "Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da safe, zan kai ki makaranta"

Ɓata fuska ta yi, dan sam ko zancen makaranta ba ta so. Ya juya ya koma ɗakinsa.

Da asuba ta yi wanka, ta yi salla, tana tantama dai-dai ma ta yi wankan, ko ba daidai ba, dan ba za ta iya tunawa complete yadda mama ta koya mata ba, kuma ita ba za ta tambayi takawa ba.

Haryanzu rumaisa tana É—okin sababbin kayan kitchen, dan haka haryanzu ba ta gaji da shiga kitchen ta yi girki ba.

Ta dafa tea, ta fito da biscuit, ta nufo falo, takawa ta gani a kan dining, ga kayan karyawarsa a kan dining, baba uwani kuma durƙushe a gabansa, ba ta san me take ce masa ba.

Kai tsaye ta nufi dining ɗin, ba ta kula su ba, ta je ta hau saman dining table abun ta, ta fara ƙoƙarin haɗa tea.

Baba uwani ta yi shiru, ta daina maganar da take yi.

"Barka da safiya ranki ya daÉ—e".

Rumaisa ta ce "Yauwwa sannu".

"Meye haka, zaki hau saman dining?".

"Idan na zauna a kan kujera, bana jin daÉ—in zama a kan tebur É—in, gara na hau sama, ya fi daÉ—i, ka san babu a house".

Ya girgiza kai ya ce wa baba uwani, "Je ki kawai, ma ƙarasa maganar".

Tunani rumaisa take yi, me baba uwani take gaya masa, da ba za a faÉ—a a gabanta ba.

"HaÉ—a mini tea zan karya, ki je ki É—auki jakarki mu tafi"

"Ni na kawo maka da zan haÉ—a maka, ita wadda ta kawo makan ta haÉ—a maka mana"

Hannu ya saka ya janyo ta ta baya, ya jawota ta ƙeya tana kallo fuskarsa.

Ya ce "Da ni ki ke?".

"A'a da kaina nake" ya hankaɗata ta tashi zaune, tana ƙiƙƙifta id.

Ta janyo kayan tean, ta fara haɗa masa, tana yi tana tura baki ta miƙa masa.

Ita kuma ta yi ƙerere a kan table, tana karyawa.

Ba ta gama na ta ciye-ciyen ba, ta ji ta ƙoshi, ta tashi ta kwashe kayan.

Sai wurin ƙarfe tara da rabi, sannan suka fita, ya tafi kaita makaranta.

Tsari da ginin makarantar, ba ƙaramin burge rumaisa ya yi ba, ta tabattar wa da kanta, akwai banbanci a tsakanin makarantarsu, da wannan, hatta ajinsu, basu da yawa, ga kujeru masu kyau, ga fankoki ko ina ga kayan wasa, ajinsu har da projector, da ake haska musu komai, duk wani abu na koyo da koyarwa akwai makarantar nan, makarantar ta burge rumaisa.

Kan takawa ya tafi, sai da aka kai shi har ajin su rumaisa, ya kalli ruma ya ce "Yau ga ki a makarantar ƴaƴan ɓarayi da suke sace muku kuɗi suna karatu. Sannan ba zan lamunci ina biyan kuɗin makaranta in tarar ba kya karatu ba, kullum zan din ga tambayarki me aka koya muku. Ban da surutun banza, da ciye-ciye. Na bayar da ordern abinci a wani restaurant, za su kawo miki abincin break, tun da kin ce ke ba za a dafa a gida ki ci ba".

"To, kai zaka zo ka É—aukeni, ko gida zan tafi?".

"Dama ke ki ka kawo kanki?"

"Ahh na san hali ne, kar ka tafi ka barni, ka ga kayan wasa a makarantar nan, zan sha lilo, idan na din ga hawa ina sufa...."

"Ba shi na kawo ki yi ba, karatu zaki yi, wuce ki shiga aji"

Rumaisa ta shiga ajin, tana ƙarewa ajin na su kallo.

***
Takawa kuwa da ya tafi hanya, Bashir ya kira a waya, ya ce masa zai shiga bamfai su haÉ—u su yi magana.

Haka kuwa aka yi, ya haÉ—u da Bashir, sai dai bai shiga ciki ba, a shiya fito haraba, suka haÉ—u.

"Allah ya taimake ka, ya amarya yaushe za a gayyaceni cin abincin amarya ne?" Yayi maganar cikin zolaya.

Adam ya ce "Idan ma da wasa ka ke yi, to ta iya girki".

"Ahha haba dai?"

"Ka bari kawai bashir, yarinyar nan caza mini kai kawai take yi, Ammi ta bata masu aiki, amma ta ce kar su kuma dafa abinci su kai mata, wai kar ayi mata asiri. Jiya fa horon yunwa ta yi mini, mun samu saɓani da safe, na fita aiki ta hana ayi girki, wai ta dafa mai da yaji ta bani, na yi magana, wai ramawa ta yi. Wallahi haƙurina na daf da ƙarewa, duk maganar da ta zo bakinta, idan zan mutu haka za ta faɗa mini"

"Adam, sai ka yi haƙuri, ka san yadda yarinyar nan take tun farko, kuma ka san ba shiri ku ke yi ba, dole ka yi haƙuri da ita, idan ka nuna mata halin muzurai, ba zaka samu abun da ka ke so ba".

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gaji ne, gashi familynmu, sun fara yar mata da maganganu, ka san ba ta da kunya ba za ta yi shiru ba. Ga matar da take tare da ita tana yi mana aiki, baba Uwani na san zaka santa, ita ma sun fara faÉ—a, ita duk abun da yake dama to ita hagu za ta yi".

Bashir ya yi dariya ya ce "A dai ƙara haƙuri, zai wuce in sha Allah".

"To, Allah ya sa, gata can dai na kaita makaranta. Jabir ya gaya wa Jamil rumaisa ce yarinyar da ta tsinci sabir, ya kuma tayar da jijiyoyin wuya a kan, dan me na ɓoye masa yana jami'in tsaro kuma yayanta. Abun da nake so da kai shi ne, ko da zance zai zo, ya san tare da kai mu ke bincike, kar ka gaya masa komai".

Bashir ya ce "In sha Allah, ba zan bayar da wata ƙofa na kowane bayani ba, sai mun yi nasara in sha Allah".

"Allah ya amince, na gode sosai " suka yi sallama Adam ya tafi.

Da daddare bayan ta dawo, tana ta murna, ta sha lilo har ta gaji, sai dai ba ta gane turancin da ake yi, dan malamansu har da turawa.

Tana ɗakinta, ta baje textbooks ɗin aka bata tana kallon hotuna, Adam ya shigo hannunsa riƙe da wayarsa, rumaisa na ɗaga kai ta kalli takawa, ta yi sauri ta rufe idonta, da hannunta, saboda daga shi sai dogon wando babu ko riga a jikinsa.

"Gaskiya ka daina shigo mini É—aki tsirara"

"Dalla karɓi" yayi maganar a kausashe, ta ɗan zame hannunta ɗaya ta karɓi wayar, ta duba ta ga kira ne, ta saka a kunnenta.

"Ƙanwar maza, ƙanwar maza".

"Yaya Aliyu, ashe baku manta da ni ba, tun ina kuka har na daina".

"Saboda kin samu duniya ko?".

Ruma ta ce "Ba wata duniya, ina mama? Ba za ta zo ba ko?".

"Mijinki sun yi waya da mama, ta ce kar a kawo ki"

"To Meyasa, bani ita".

Mama ta karɓi wayar ta yi sallama ta ce "Ƴar auta".

"Mama shi ne ki ka ƙi zuwa, kuma ki ka ce kar a kawoni".

Mama ta ce "Ke tafi can, ba gaki nan ba abun da ya same ki ba".

"Ni dai dan Allah ki zo, ko in ta yi masa kuka, tun da kin fi son sa"

Mama ta ce "Shi wa?".

"Mijina" ta bata amsa kai tsaye.

"Sannu mara kunya, ai dama ban ce nawa ba ne naki ne".

Ruma ta ce "Mama albishirinki".

"Goro"

"Kin ga haɗaɗiyar makarantar da ya kaini, kamar a turai, kin ga liluka kuwa? Ga fankoki har da malamai turawa, baki gani ba, baki taɓa zuwa gidana ba ma, gidana haɗaɗɗe, duk ya sai kayan daɗi ya zuba mini"

Mama ta ce "Sai ki je ki same shi, ki yi masa godiya, dan na san baki yi ba"

"Taɓ, mama yaushe zaki zo to?"

"A'a ni ba zan zo gidanki ba, amma dai idan ya kawo ki shikenan". Za ta yi wa mama taɓara, mama ta kashe wayar.

Rumasai ta share hawayenta, ta bishi É—akinsa, ta tarar yana banÉ—akin, ta ajiye masa wayarsa ta fice.

Kwanci tashi asarar mai rai, yau juma'a rumaisa kwana biyar da fara zuwanta makaranta, kuma wata guda cif, da É—aura mata aure.

Takawa ya É—aukota daga makaranta, ta ga ya canza hanya, maimakon su tafi gida.

"Ina kuma zamu je?".

"Sayar da ke, na yi tsafi da ke, kamar yadda aka ce na yi da aisha" ya bata amsa.

"To ai dai bani na faÉ—a ba ko?"

Tana gane gidansu zai kaita ta ce "Yeee zan ga Ammi zan ga Sabir da Anty Iman".

Da haka suka ƙarasa, cikin murna ta riga shi shiga sashin Ammi.

"Oyoyo ga ruma"

"Ammi, kin ga na fara zuwa makaranta, kin ga jakata"

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya sanya albarka"

Iman ta ce "Congratulations Anty rumaisa".

"Thank you anty iman"

Takawa ya shigo, ya tarar da rumaisa a kusa da ammi tana nuna mata litattafanta.

Wato rumaisa ko kumyar nan ta sirka ba ta da ita.

"Ammi ina Sabir?".

Ammi ta ce "Yayi bacci"

"To bari in gama nuna miki litattafaina, sai na je na ganshi".

Ammi ta dubi Adam ta ga yanayinsa, kamar mara lafiya, ta ce "Takawarka lafiya, ya aka yi ne? Na ga yanayin ka kamar akwai damuwa"

Ya ce "Bakomai" tare da kashingiÉ—a.

Ta kalli rumaisa ta ce "Rumaisa, ko akwai matsala ne?".

Ruma ta gyara zamanta ta ce "Eh, dama ƙararsa zan kawo miki tun rannan, dan dai bamu zo ba ne, na ce sai na gaya miki, kin ce duk abun da yayi mini na gaya miki".

Ammi ta ce "Subhanallah, meyafaru?"
Chapter 165 · 0% Book details