← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 174

Sashe 164

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wani abu, ko wani abun za ayi mikk?"

Ruma ta ce "A'a, girkin rana zan yi, kar ku dafa abinci da mu, ku yi daga naku, sai na sauran masu aikin".

Barira ta ce "To, amma ba abun da zamu tayaki?".

Rumaisa ta ce "Bakomai, Anty Asiya, dan Allah É—auko mini mai, ki tayani na kai sama, bari na tafi da wannan kayan".

Asiya ta ce to.

Rumaisa na shirin fita, baba Uwani ta shigo tana tsuma, ta ce wa rumaisa "Amarya ba kya laifi, har mai gidan ya fita ne?".

"Eh, ya fita".

"Ina fatan dai ba wata matsala ko? Idan da wata matsalar zaki iya gaya mini, ni uwa ce a wurinki, kuma kin bar shi ya saukko shikaÉ—ai, ai kamata ya yi ace ki na raka shi har mota"

Murmushin gefen baki rumaisa ta yi, ta wuce ta bar baba uwani.

A kitchen É—in ta, Asiya ta sameta, ta ajiye mata man, har za ta tafi rumaisa ta ce "Anty Asiya, bari na baki hijjabi, da ke da Barira, a cikin kayan lefena suke, sun yi mini tsawo sosai".
Asiya ta buÉ—e baki ta ce "Wane mu ranki ya daÉ—e, kayan lefenki fa".

Ruma ta ce "menene a ciki, kyauta zan baku, sun yi mini tsawo".  Ta tafi ɗakinta, ta ɗaukko hijjabai a akwati ta kawowa Asiya.

Asiya ta din ga godiya, ruma ta ce "Dan Allah ki daina yi mini godiya, har kin saka na ji kunya, ba fa ni na saya ba, nima bani aka yi".

Asiya ta ce "Haka ne, duk da haka dole na yi godiya, sannan dan Allah ranki ya daÉ—e, ki din ga É—abi'ar matan sarakuna, girmanki ne dole a biki, kuma duk hukuncin da ki ka yanke a gidan nan dole a bi shi, amma wani abu nake son gaya miki, ban san ya zaki ji ba".

Rumaisa ta ce "Gaya mini bakomai".

"Ki yi hankali da taka tsantsan da baba uwani, amma kar ki ce na gaya miki dan Allah".

Ruma ta ce "Ai ni dama ba ruwana da ita, bana son dariyar da take yi mini, bakomai in sha Allah na gode" Asiya ta juya ta sauka tana murna, yarinya ƙarama mai halin manya, ta san ta yi kyauta.

***
"Amma Jabir kana ganin abun da Adam ya yi ya kyauta, idan Fulani matarsa ce, mu kuma ƴan uwanta ne, shi jami'in tsaro ne nima haka? Dan meyasa bai ɗauki wani mataki a kan ɓatanta ba, meyasa bai gaya ba? Daga yin garkuwa da ita ya aka yi ya ɓoye wa duniya? Ya yi wa kansa adalci kenan, idan yana da gaskiya, ai tuntuni yakamata ya bayyana Yarinyar nan, ayi bincike a kanta, ko za a samu wani information ɗin".

Jabir ya ce "Easy mana, haba Jamil, ina ga mun fi kowa sanin Adam, a ɓangaren taurin kai da zurfin ciki, duk familyn nan albarka, kowa ya san shi a kan haka, kai waye ya ce maka a zaune yake tun da ta ɓata? Adam ya shiga cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, tun bayan ɓatanta, kuma ba wai yana zaune ne kawai ba, da shi da gayen nan Bashir, da wasu daga ƴan sandan garin katsina, suka yi ta ƙoƙari a kan lamarin".

"Amma ya aka yi kai ka sani, ni ban sani ba? Ina yayanta kuma jami'in tsaro kamar shi?"

"Saboda na fi ka kusanci da shi, na san halinsa tsaf, dan haka na fika iya zama da shi, shiyasa nake sanin abun da ba ka sani ba, yanzu abun da ya kamata shi ne, kamar yadda ya ce ka tamabyai mai girma turaki, ka yi masa zancen ka ji mai zai ce?".

Jamil ya ce "Ai gaba É—aya ma kaina ya kulle ne ma, amma zan zurafafa bincike a kan lamarin nima".

Jabir ya ce "Better".

***
Ta window rumaisa ta leƙa, ta hango motar Adam, kusan biyar da rabi lokacin, Murmushin mugunta ta yi, ta koma ɗakinta ta yi zamanta, a sababbin litattafan da ya saya mata, na makaranta da za ta fara zuwa, ta ɗauki ɗaya da fensir, tana zane-zanenta.

A gajiye yake sosai, ya tarar da abincinsa a É—akinsa, yanayin yadda aka ajiye abincin ya bashi mamaki, har da jug, jikinsa gaba É—aya babu daÉ—i, dan haka ya yanke shawarar fara yin wanka, sannan ya ci Abincin.

Yayi wanka, ya sauya kaya, ya zo ya zauna, ya fara buɗe jug ɗin, yayi arba da ruwan famfo a ciki, shi da yake ajiye cartons na ruwa, da lemuka, ya buɗe abinci ya ga shinkafa fara ƙal, ga man ƙuli ga dunƙule da yaji.

Wani irin ƙululun takaici, ya ƙule masa wuya, ba ƙaramar yunwa yake ji ba, kuma ba ya cin abinci da mai da yaji. A fusace ya tashi ya fita, ya sauka ƙasa yana kiran baba uwani.

Ta fito a rikice tana tambayar ko lafiya?.

"Meyasa za a dafa mini abinci mai da yaji a gida? Idan akwai abun da babu, ba na ce a din ga gaya mini ba, dan me za a dafa mini mai da yaji?".

Ta shiga tafa hannu ta ce "Wallahi ranka ya daɗe laifin matarka ne, babu yadda ban yi da ita ba, ta ce ita za ta yi maka girki, na ce mata ba ka cin abinci da mai da yaji, amma yarinyar nan ta ƙi yarda".
Asiya ta kalli baba uwani, suna ƙasa basu san ma me ruma ta girka ba, balle baba uwani ta hanata, amma ta ce ta hanata ba ta hanu ba.

A fusace ya koma saman benen, baba uwani ta lallaɓa ta bi bayansa, tana cigaba da salallami.

A falo ya tarar da rumaisa ta fito, cikin fushi ya kalleta ya ce "Muzuru ne ni da zaki dafa abinci da mai da yaji ki ajiye mini?".

"Papa meye a ciki, abinci ne fa?".

"Shut up! Na yi kama da wanda zai ci abinci da mai da yaji ne?".

Baba uwani ta ce "Ayi haƙuri mai gida, ba za ta sake ba, rashin sani ne, in sha Allah zan nunnuna mata abubuwan da yakamata ta sani, duk laifina ne, yarinta ce take damunta"

"Ba wani yarinta baba uwani, ai na ce girki ba huruminta bane ba, ta bari a din ga yi amma kasancewar, kunnen ƙashi ne da ita, ba za ta ji ba".

Kuka rumaisa ta saka ta ce "Kuma sai na gaya wa ammi kana yi mini faÉ—a, idan na yi abu gwaleni ka ke yi".

Taski ya yi ya , tafi É—akinsa, yana barin falon rumaisa ta yi wa bayansa gwalo.

Ya fito da mukullin motarsa, ruma ta ce "Papa ina zaka?" Banza yayi mata ya sauka, baba uwani sai bashi haƙuri take yi.

Bayan ya sauka baba Uwani ta kalli rumaisa ta ce "Ranki ya daÉ—e, ai ba a...."

Rumaisa ta kasteta ta hanyar cewa "Idan mun yi faÉ—a, ba sai kin nema mini afuwa ba, yarinya ce ni ba mahaukaciya ba, kuma ina sane na yi hakan, na san ba ya cin abinci da mai, an gaya mini" galala baba uwani ta bi rumaisa da kallo, dama baki ne da ita haka? Kamar ba daga bakinta maganganun suka fito ba.

"Amma Æ´ar nan idan ki ka fusata shi, yana da larura fa".

Rumaisa ta kalleta ta ce "Wace larurar?" Sai kuma ta tuna katoɓarar da ta yi ta ce "A'a bakomai".

"Shikenan tun da ba zaki gaya mini ba , idan ya dawo sai na tambaye shi wace larurar ce da shi?".
Baba uwani ta ce "Na shiga uku, da wasa nake yi miki, ba ya son ɓacin rai ne dai, dan Allah kar ki gaya masa".

Rumaisa ta ce "Aini duk abun da aka gaya mini sai na bi diddigi, bana mantuwa" ta wuce ta bar baba uwani tana gumi da dana sanin maganar da ta yi.

***
Ƙishirwar son ganin Umar faruk, ta din ga damun zuciyar iman, hotunan biki din ga shiga, tana kallon hotunan duk da ya fito a ciki. Cikakken namiji mai cikar zati kamala, duk da ba fara'a yake yi ba, son kowa ne ƙin wanda ya rasa, namiji mai matuƙar jan ajinsa da tsare gida.
'Na shigesu, me yake damuna ne?'

'son wanda bai san kina yi ba, wanda ba ki da damar ki nuna masa hakan, wands tsantseninss da kamewarsa, da matsanancin kwarjininsa ba za su bari ma ya gane hakan ba' wata zuciyar ta bata amsa.

Tashi zaune ta yi ta ajiye wayar, tare da furta 'Allah ka iya mini" ga gefe guda Jabir yana ta hura wuta, wanda har Ammi ta fara ganewa.

Ta sake É—aukar wayar, ta shiga what's app É—in ta, da ta yi saving number sa, da Yaya Omar, ta shiga chat, sai dai ta rasa mai za ta rubuta, ta buÉ—e hoton ka dp É—in sa, hotonsa ne shi da hassan É—in sa, wato yaya Abubakar.

Ta sake ajiye wayar, tana ajiyar zuciya.

***
Baba uwani addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar rumaisa, ta tambayi Adam, dan sai yanzu ta fara lura, yarinyar a tsaye take, gata dai yarinya amma alamu sun nuna ba ta ji.

Sai da aka yi sallar isha'i, Adam ya dawo, sai dai abun mamaki, ya tarar da abincin a É—akinsa, amma a wannan karon har da miya, da salad da komai aka shirya masa.

Bai kula abincin ba, dan ya ciko cikinsa a gidan ammi.

Ya zauna babu jimawa, sai ga rumaisa ta shigo da sallama.

Ya shareta, ya fara ƙoƙarin buɗe laptop.

"Sannu da zuwa"

"Zo ki kwashe abincin nan, ki fita da shi".

"Da miya ce fa yanzu".

"Ba na ci"

Ta yi dariya ta ce "Na sha gaya maka, ka daina yanke hukunci da zuciyarka, ka din ga yi da ƙwaƙwalwarka, na san ba ka cin abinci da mai da yaji, Iman ta gaya mini, to in gaya maka na yi miya, ina sane na baka da mai da yaji, na san faɗa za ka yi, ka yi zuciya, na san halinka ai tas, to ranawa na yi, soyanin da ka yi da ruwan zafi da safe" ta yi maganar tana haƙiƙancewa.

Yayi mata shiru, bai ce uffan ba.

"Kuma saura abubuwan da ka ke yi mini, duk sai na rama".
Chapter 164 · 0% Book details