← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 174

Sashe 51

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruma ta jinjina kai ta ce "Sune suka baku kaza ku bani na ci?"

Ya waiwaya ya kalli wanda ya bawa ruma kazar ya ce "Tun da ki ka cewa yayanki yunwa ki ke ji, yayi wa 'yan uwanmu waya, ya ce su sayo kazar, dama zamu karɓi saƙo a wurinsu, shine ya karɓo miki ya baki"

Ta yi murmushi ta ce "Allah sarki, kuna da kirki, to ku baku da gida, 'yan uwan na ku a daji suke ba gida ba?Na ga daga daji suka fito kuma babu gida a cikin daji ai"

"Eh, bamu da gida a daji muke rayuwarmu".

Cikin mamaki ta ce "Kai sai ka ce wasu kuraye, ku wane yarene to?"

Ya haÉ—e rai ya ce "Ke kin isheni fa, bar nan gurin"

Ruma ta ce "Yi haƙuri, dama ko a gida haka ake cewa na fiye tambaya, na daina, ina son sanin abubuwan da ban sani bane".

Bayan ta yi shiru, sai ta hau tattaɓa jakar hannunsa ta ce "Wai kai ba zaka ajiye kayan nan ka huta ba, ba ka jin nauyi"
Saurin janye jakar yayi yayi mata shiru.

"Na ji kamar wasu ƙarafa, kayan gwan-gwan ne a ciki? Su kuma kna zaka kai su"

A fusace ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin kan na illata ki?" Yayi mata maganar cikin tsawa, ko girgiza ba ta yi ba, sai ma tsare shi da ta yi da ido, wata lamba ce a jikin jakar, wannan jaka dai ba za ace kaya ne a ciki ba, sai dai lambobin jikin jakar sun É—au hankalinta sosai.

Aliyu ne ya figo hannunta yana zaginta.

"Yarinya ce, ka daina dukanta mana babu kyau yarinya ce ƙarama" yayi wa Aliyu maganar yana riƙe hannun Aliyu.

Aliyu ya rasa haɗin mutumin nan da rumaisa, da ya yi mata faɗa sai ya hau ce masa ya ƙyaleta yarinya ce, ko ina ruwansa oho.

Haka ya haƙura ya ƙyale ruma, tun da mama ta kira ya ce mata haryanzu basu isa ba, ya sanya mama shiga cikin damuwa, saboda ya ci ace sun je, amma ta ji suna hanya.

A haka aka gyara motar suka hau suka cigaba da tafiya. Ruma ta durƙusa ta taɓa wata jaka da kuma buhu da ke ƙarƙashin kujerar da take kai.

"Wai dan Allah kayan waye wannan da ba za a saka masa su a ƙasan kujerarsa ba sai ta mu, ni fa sun isheni na yi kawaicin na gaji, sun addaba mini".

Mutumin nan dai ya waiwayo ya ce wa ruma "Yi haƙuri, mun kusa sauka ma, namu ne zamu ɗauke".

"Wallahi É—an uwanmu ba dan naka bane ba, sai an cire mini su, da na wannan mai jakar ne da ya hantareni sai ya kwashe kayansa ya mayar da su wurinsa, É—azu daga tambaya ya yi mini tsawa".

"To kiyi haƙuri" ɗayan ya waiwayo ya kalli ruma, ruma ta zaro masa ido kamar tana kallon yaro.

Aliyu dai ya sunkuyar da kai yana cigaba da addu'a, shi ba abin yayi wa ruma magana ba ko ya rufeta da duka ba.

Sun shiga katsina, a wani ƙaramin ƙauye suka tsaya zasu sauka, mai jakar nan ya kalli ruma ya ce "Ke sauko, zamu ɗauki bindigoginmu".

Tsit kowa ya yi, ruma ta ce "Wace irin bindigogi kuma?"

"Zaki sauko ko sai bomb É—in ciki ya tashi da ke?"

TankaÉ—ata Aliyu yayi suka sauka, aka É—aga musu kujera, aka fara fito da jaka.

"Dan Allah da gaske bindiga ce a ciki?"

Yayi murmushi, ya zugewa ruma jakar, ƙananan bindigu ne, ƙirar pistol.
Ya ce "Waccan jakar kuma da kike tambaya meye a ciki É—azu, bullet ne a ciki"

Ta É—an waro ido ta ce "Kashe mutane ku ke yi kenan, tun da dai na ga ku ba 'yan sanda bane kuma ba sojoji ba?"

Ya girgiza wa ruma kai ya ce "A'a 'ya ta, aikin Allah muke yi ake biyanmu"

"Aikin Allah ai ba a biyan mutum, Allah ne zai biya mutum da lada"

Yayi murmushi ya ce "Ba zaki gane ba, Ubangiji Allah ya yi miki albarka ya rayaki, da 'ya ta na raye da ta yi kamar ke"

"To ta na ina yanzu 'yar ta ka?"

"An kasheta ita da babarta, Allah ya rayaki" ya kalli Aliyu ya ce "A lallaɓata dan Allah, sai wataran 'ya ta" yayi maganar yana ɗagawa ruma hannu.

Wata narkekiyar mota ce ta yi parking, mai kyan gaske aka É—ora kayan bindigar a ciki, suka shiga motar aka ja suka tafi.
Ruma ta É—auko wayarta ta fara dannawa.

Aikuwa Aliyu ya dinga zaginta, har da zagin da bai san iya shi ba, dan ruma ta kai shi maƙura yau, gaba ɗaya ruma ba ta da hankali ba ta san ciwon kanta ba, shi tun da suka hau motar, suka yi nisa ya gane bindigogi ne a buhun da ke ƙasan kujerarsa, kuma yana fuskantar yaren da suke yi kaɗan-kaɗan, 'yan ta'adda ne mutanen, amma ruma sai hauka take zubawa da wauta saura ƙiris ya karɓi shegiyar wayar nan ya jefa ta ta window. Sai dai yana tsoron yin hakan dan ya ga mutumin nan ya zaƙe a kan ruma kar yayi masa wani abu idan ya taɓata.

Direban ya ce "Wallahi bawan Allah Yarinyar nan mai sa'a ce, dan ni na zaci ma da zasu sauka tasa ta zasu yi a gaba su tafi da ita, ko su kasheta surutunta yayi yawa, ba a yi wa wannan mutanen haka"

Aliyu ya ce "Eh kaima ai azzalumin ne, da ka É—auko mu mota É—aya da wannan mutanen".

"Megida ba laifina bane ba fa, kullum akwai irinsu da suke shige da fice zuwa garuruwa, ba su fiye cutarwa ba sai in kun musu rawar kai, mu ma abincinmu da rayukanmu muke karewa".

"Amma jami'an tsaro na garin nan, ga su a tasha, amma ake safarar makamai a tsakanin garuruwa suna gani?"

"Lallai ɗan samari zancen ka ke so, lamarin ƙasar nan ta mu ai sai dai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, idan ka matsa sai ka kwana a ciki amma manyanmu sun san komai"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "Allah ya kyauta".

Sai bayan la'asar sannan suka sauka, Ruma ta sha mita, kamar Aliyu ya ari baki, tayi masa shiru ta ƙi kulashi.

Sai da mama ta kira ta ji sun sauka sannan hankalinta ya kwanta.

Gidan da suka je babban gida ne, mak É—auke da part-part, galibi Ruma ta san su, dan suna zuwa gidansu dan haka ba ta ga wani abu na musamman a a wurinsu ba, sai dai yanayin garin yayi mata kyau.
A sashin Gwaggo suka sauka, Gwaggo Atine har da hawayen murna, ta rungume ruma tana yi musu maraba.
'yar autar Gwaggo lawisa, sai kallon ruma take, da yake za su yi sa'anni da ruma, sai kallon ruma take yi.
Ruma kuwa jikinta ne duk ya mutu, saboda uwar tafiyar da suka yi, ba ta taɓa tafiya mai nisan ta yau ba.

Aliyu ya yi alwala, ya ce ita ma ta tashi ta yi salla.
A kan sallayar da ta yi salla, ta nemi wuri ta kwanta, nan da nan jikokin Gwaggo suka fara zuwa ganin ruma.

Ruma a ranta ta ce "Ji bala'i, kamar an ajiye musu buranya, sai kallona suke" ta dunƙule a cikin hijjabinta ta ɓoye fuskarta.

Gwaggo tamkar zata goya ruma, su Aliyu su kan zo, shi ma sai a shekara wani daga cikinsu bai je ba.
Nan da nan ta É—orawa ruma.
"Auta taso ki zo ki yi wanka, zaki ji daÉ—in jikinki sosai"
Ruma kamar ta ce ba zata yi ba yamma ta yi, amma ta ga kar ta watsawa gwaggon ƙasa a ido, daga zuwanta, ta tashi ta je ta yi wanka da ruwan zafin.
Bayan ta fito ta tarar da lafiyayyiyar alala ta sha manja.
Ruma haryanzu a ƙoshe take da kazar da ta ci, dan haka ta ci kaɗan ta ce ta ƙoshi.

Lawisa kuwa so take ta yi wa ruma magana, amma ruman sai wani basarwa take tana haɗe rai, gaba ɗaya jikinta a ciwo yake, saboda wannan wahalalliyar tafiyar da suka yi, ga wani ɓacin rai da take ji da ba ta san dalilinsa ba.
Ganin ruma ba zata kulata bane, ya sanya ta fara ƙoƙarin yin abin da zata burge ruman, sai ƙoƙarin shishshige mata take yi.

"Ba ki ci alalar da yawa ba, zaki sha fura?"

"Na ƙoshi" ruma ta bata amsa a taƙaice.

Lawisa ta yi murmushi ta ce "To rama fa"

"Baiwar Allah cikina ne a cike fa, na ƙoshi, ko haɗama ki ke so in yi?"

"A'a, ko in É—auko miki fulo ki kwanta".

Ruma ta ce "Eh, dama na gaji sosai"

Lawisa ta je ta É—auko fulo, ta kawo wa ruma, ruma ta kwanta babu jimawa ta hau bacci.

***
Nema yake ya fita daga hayyacinsa, duk Addu'a da ta zo bakinsa yi yake yi, amma kansa kamar ana buga masa wani abu, ga wayarsa na ta ringing amma ba zai iya ɗagawa ba, ya lumshe idanunsa, ya jin yadda cikin naman jikinsa ke wani irin zafi, idanunsa kamar za su fito saboda ciwon kai, ya dafe kan yana karanta alƙur'ani a fili, a hankali wani mawuyacin bacci ya kwashe shi.

Rumaisa ya gani a kan wani dutse a zaune tana kuka. Hayaƙi na ta tashi a wurin, amma yana iya gane fuskarta.

*Wallahi sai ka yi dana sanin abin da ka yi mini, daga yau ba zaka sake yi wa wani abun da kayi mini ba, ba dai taƙamarka kuɗi ba, to ni nan Rumaisa kai da kuɗin naka da sarautar ta ka sai ka durƙusa mini a kan gwiwoyinka, kuma ka saka a ranka nice nan abokiyar gabarka* kamar yadda ta gaya masa a haɗuwarsu ta ƙarshe, haka ma a yanzu take sake maimaita masa, ya buɗe idonsa a hankali a cikin dodon kunnensa yake cigaba da jin sautin muryarta.

Ruma ma da bacci ya kwasheta, a razane ta yi wata 'yar ƙaramar ƙara ta farka, tana haki kamar wadda ta sha gudu, a lokacin duhun magariba ya rufa! Gaba daya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya?.
Chapter 51 · 0% Book details