← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 174

Sashe 144

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lambar mama ya kira, ya tambayeta wani É—akin ne, ta sanar masa, yayi gaba rumaisa ta bishi a baya.
Sai da suka je ƙofar ɗakin sannan ya tsaya, ya kalleta ya ce "Ƙwanƙwasa ki fara shiga"

Ta matsa gaban ƙofar, ta ƙwanƙwasa sannan ta buɗe ta shiga da sallama babu kowa a ɗakin, sai iman da ke kwance, hannunta ɗauke da cannula, an rataye robar ruwan da aka gama saka mata a drip stand.

Shiga ya yi shima, sai dai babu kowa a É—akin sai ita kaÉ—ai.

Da sauri rumaisa ta ƙarasa gaban gadon tan faɗin "Subhanallah, Anty Iman, baki da lafiya ne?" Sai dai ta tarar bacci take yi.

Ta kalli mai sunan baba ta ce "Amma ya naga babu kowa a wurinta" shirun da yayi mata ya sanya, ta tuna ta yi tambaya ba a gurbinta ba.

Da sauri ta ce "Bari na duba waje, ko zan ga wanda yake zaune tare da ita". Ta juya ta fita da sauri, shi kuma ya tsaya a tsaye, ya sake kallonta tana kwance cikin doguwar rigar material, dogon gashin nan ya sha ribbon, duk da ya ɗan hargitse, ga farar fatarta gwanin sha'awa, babban abun burgewa da jikinta, bai wuce wuyanta ba, duk da ba ta da ƙiba, amma tana da irin wuyan nan, mai guru-guru.

Da sauri ya sunkuyar da kansa yana a'uzubil'ahi.

Zagayawa rumaisa ta shiga yi a cikin asibitin, tana mamakin waye yake zaune da iman a asibiti, ya bar ta ita kaÉ—ai babu kowa?

A hankali Iman take furta "Ammi, Ammi ruwa, ƙishirwa nake ji" yana jin ta, yayi shiru, kamar babu kowa a ɗakin.

Tun bayan farfaÉ—owarta, kasancewar ciwon kan baya sauka, ya sanya likitocin, suka yi ta yi mata allurar barci, da sai yanzu ta saketa ta tashi.

Duk da tana cikin ciwo, sai da ta razana da ta ganshi, a tsaye yana danna wayarsa.

Tunani take yi ko a mafarki take, ta miƙa hannu jikinta yana rawa, tana ƙoƙarin ɗaukko robar ruwan da ke kan side bed.

Sai a lokacin ya motsa, ya ƙarsa, ya ɗau kofi, ya zuba ruwan ba tare da ya kalleta ba ya ce "Tashi ki sha"

Cikin tsananin tsoro ta ce "Bani in sha a kwance, ba zan iya tashi ba"

Miƙa mata ruwan yayi, ya ga iya gudun ruwan ta, ta fara ƙoƙarin sha a kwance, ya karɓa kofin ya ce "Tashi!"

Kamar zata fashe da kuka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri kaina ciwo yake yi"

Haushi ne ya kama shi, gani yake kawai tsabar langwai ne, da iskanci. Ya saka hannu ya É—agota gaba É—aya, hakan yayi dai-dai da shigowar nusaiba.

Wani irin ihu ta saki, ta riƙe hannunsa, hawaye na bin fuskarta, sabodaa ji ta yi, kamar kanta ya rabe biyu.

Da gudu Nusaiba ta ƙaraso tana faɗin, "Wanene wannan, bawan Allah lafiya?" Tayi maganar tana yi masa kallon sani, amma ta manta a ina ta san shi.

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Wane irin shirme ne zaki tafi ki bar mara lafiya ita kaÉ—ai, wace irin jinya ce haka?"

Gaba ɗaya ruɗewa nusaiba ta yi, ba ta san waye ba, amma kwarjinin sa ya razanata, ta ce "Likita ne ya ce a bani jininta na kai gwaji yana buƙatar result yanzu, ammi kuma ta riga ta tafi gida ta je ta huta, shine na je lap ɗin asibiti, suka ce ba sa yi, shi ne na fita waje, da takawa nake jira ya zo ya kai, likita ya ce lallai yanzu yake so"

Tsaki yayi, ya kalli iman ya ce "Ke kuma cikani" wata irin kunya ce ta kamata, dan ba ta san ta riƙe shi haka ba.
Ta sakar masa riga, ta karɓi ruwan ta fara sha.

"Ita kuma wannan ma shiririciyar ko ina ta tafi oho mata".

Rumaisa kuwa lungu da saƙo na asibitin take ta bi, har ta gaji ta kama hanyar komawa ɗakin, kawai ta hango motar takawa, yayi parking ya fito daga motar, hannunsa riƙe da leda.

Aikuwa ta nufe shi, babu tsammani ya ganta a gabansa.

"Dama kai ne a wurin Anty Iman? Haka ake jinyar mutum dama, ka yi tafiyarka ka barta? Kai idan aka yi maka haka zaka ji daÉ—i ne?"

Sororo yake bin ta da kallo, yadda take yi masa haƙilon masifa kamar babarsa.

"Ya ina magana kana kallona, sai wani abun ya sameta? Kawai ka É—au mota ka tafi yawonka, ka bar mara lafiya ita kaÉ—ai? To wallahi sai na gaya wa ammi" banza yayi mata, ya nufi cikin asibitin, rumaisa kuma ta bishi tana cigaba da mita.

Cike da shiga taitayi, Nusaiba ta bawa mai sunan baba haƙuri, ita dai ba ta san waye ba, amma ta tsinci kanta da shakkarsa.

Ta kalli iman ta ce "Iman, me zan baki ki ci to, tun jiya baki ci komai ba, an ce lallai ki samu ki ci wani abun, ga abinci ga fruit wanne zaki ci?"

Iman ta girgiza kai ta ce "Na ƙoshi, bana son cin komai" mai sunan baba a ransa yake jinjina halin mata, su a rayuwarsu ta duniya komai sai an lallaɓasu? Abincin ne ba zata ci ba, sai an yi ta rarrashinta, alhalin ta san kanta zata cuta idan ba ta ci ba.

Takawa ne yayi sallama, ya shigo hankalinsa a kan iman, ya ƙarasa gaban gadon ta.

Nusaiba ta ce "Maman sabir, yaushe ki ka zo?"

"Tun É—azu muka zo ni da mai sunan baba, ashe wannan ne yake jinyarta, ya tafi ya barta ita kaÉ—ai" tayi maganar tana nuna Adam.

Nusaiba ta ce "Eyya, ni ce tare da ita, jininta na tafi kai wa a gwada, ba yadda zan yi ne shiyasa na tafi na bar ta".

Rumaisa ta ce "Au na zata shi ne ai".

Ta ƙarasa ta leƙa fuskar iman ta ce "Anty Iman ya jiki?".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Da sauƙi Alhamdilillah ".

Adam ma lallaɓata yake yi, ko za ta ci wani abun, amma ta ce ita ba ta cin komai, ya din ga rarrashin ta, ta ce tuffa take so, takawa ya tashi ya ce bari ya je ya duba, ya sayo mata.
Daga mai sunan baba har Adam babu wanda ya kula wani, takawa na tafiya, iman ta fara ƙoƙarin kwanciya, mai sunan baba ya kalli Nusaiba ya ce "Ke, zuba mata abincin nan" gaba ɗaya suka tsaya suna kallonsa.

Rumaisa ta jinjinawa Nusaiba kai, dan ba ruwansa da baƙunta yanzu sai ya balebalesu da masifa.

Romon kifi ne da dankalin turawa, sai ƙamshi yake yi, idon iman ya cika da hawaye, dan ko ƙamshin abinci ba ta so, ya karɓa ya je gaban iman ya ajiye shi, ya tsaya mata ƙiƙam a ka, ba tare da ya furta komai ba, ta kama cokali, ta fara cin abincin nan, jikinta yana rawa, saboda tsoro da fargaba, ga wata irin Muguwar kunya, dan ba ta saba cin abinci a gaban maza ba, ko a taron mata ba iya ci take ba.

Sai da ta ci sosai sannan cikin faɗa  ya ce "Kuna sane kuke wahalar da iyayenku, dan kun ga suna ta taku. Ke kuma tashi mu tafi" yayi maganar yana kallon rumaisa.

Ta tashi, kamar ta tuntsire da dariya, daga Nusaiban har iman É—in kamar ka ce kyet su zura da gudu, saboda tsoro.

Ruma ta ce "Anty iman, Allah ya ƙara afuwa".

Cikin sanyin jiki ta ce "Amin maman sabir na gode".

Bayan tafiyarsu Nusaiba ta ce "Ke iman, wannan jarabbaben mutumin fa?"

"Yayan rumaisa ne" ta bata amsa.

"Kam bala'i, yau na ga wanda ya taka takawa iya tsare gida, daga zuwa ya hau ni da masifa"

Iman ta sunkuyar da kai ta ce "Mhmm, baki ga komai ba"

Babu daÉ—ewa takawa ya dawo da tuffa, Nusaiba ta bashi labarin abun da ya faru, bai ce komai ba yayi shiru, dan shi kansa jin kan mai sunan baba yana bashi mamaki.

***
Iman jikinta yayi sauƙi, mama ma ta je asibitin ta dubata, ta warware, sai dai lokaci lokaci, kan ya kan matsa mata da ciwo, aka sallameta daga asibiti. Sai dai tun da ta koma gida, washegari ta sake tashi da ciwon kan, sai dai ta yi ƙoƙari ta jure, saboda ba ta san sanya ammi a damuwa.
A ranar da aka sallameta daga asibiti ranar Jabir ya dira Nigeria, daga wurin duba mahaifinsa.
Hajiya Lubabatu ta yi mamakin ganinsa ya dawo, dan sun yi da shi zai yi sati uku a can kan ya dawo.

"Wai kai Jabir, menene ya dawo da kai tun a yanzu?"

"Bakomai, ji na yi an ce iman babu lafiya, shiyasa na dawo ita ma na dubata".

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Iman É—in, kai a wa? Meye haÉ—inka da ita?"

"Bakomai zumunci kawai".

"Ban gane zumunci ba? Jabir kar na zo na ji wata magana saɓanin wadda nake son ji, ka san halina dai ban da kyau"

"Babu wata magana da zaki ji, kawai dai ina yi ne saboda Adam" tsaki tayi, ta shiga wata sabgar daban ta ƙyaleshi.

***
Yau tun da safe ammi ta kira mama, ta sanar mata da Adam zai zo wurin rumaisa, domin idan da wani abu da take buƙata ta gaya masa na game da shirin biki.
Amma mama ta ce "A'a hajiya, a ƙyaleta kawai, duk abun da aka yi Allah ya amfana"
Ammi ta ce "Ai da ni da ke, babu ruwanmu, namu ido abu ne na ma'aurata, dan haka yakamata su din ga tattaunawa domin su fahimci junansu!.

Ayshercool.
08081012143
*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
Chapter 144 · 0% Book details