Sashe 162
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ƴar tatsitsiyar ƴar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ƙarshenta ma na sha zagi".
Babban abun da ya yi wa rumaisa daÉ—i, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?"
Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daÉ—i, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka".
Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daÉ—in ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi"
"Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman".
Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karɓi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya.
Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai ɗaga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ƙaraci ringing ɗin ta, ta kaste yaƙi ɗagawa.
Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya É—aga yayi sallama.
"Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma taƙi zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma"
"Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ƙorafi?".
"Mama taƙi ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya".
Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka? Meya sameki?".
"Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba".
Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ƙyaƙyace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo".
Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi"
Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?".
"Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa".
Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki".
"To ai ba wayata ba ce ba".
"Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ƙara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar ɗaukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar.
***
"Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves É—in sa ne?".
"Ranka ya daÉ—e, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa".
"A'a fa, ka san yaron nan da wayon tsiya, kar in je lumbu-lumbu yake yi mini, yana wani binciken ta ƙarƙashin ƙasa, ko shirya wani abu da ban sani ba".
"Babu abun da yake aiwatarwa, ba tare da na san motsinsa ba, a yanzu dai haka babu ranka ya dade".
Ya juya ya kalli wakili ya ce "Khalifa, kai wurinka babu wani update É—in".
Khalifa ya ɗan sauke numfashi ya ce "Babu Daddy, sai dai ina nan ina ta bin diddigin sa fiye da yadda ka ke tsammani, babu wani abu da yake yi s kanmu, sai dai wani ƙishin-ƙishin da nake ji, wai yarinyar da ya aura, ita ta tserato da ɗan sa daga wurin masu garkuwa da mutane, amma bani da tabbas, an ce in jira a samu tabbacin hakan".
Senator wakili ya jinjina kai ya ce "Duk yadda ake ciki ka sanar mini, idan har ita É—in ce, ka samo mini tabbacin hakan, a kan lokaci".
"To shikenan, In sha Allah daddy"
***
A duk lokacin da rumaisa ta je canza pad, cikin ƙyanƙyami take yi, kuma a tsorace take da tunanin jininta zai ƙare, har sai da iman ta fuskanci wani abu, amms ba ta takura mata da son sanin menene ba, tun da ba ta gaya mata ba.
Mai sunan baba kuwa wuni yayi yana kallon missed call É—in, iman a wayarsa, yana tunanin me za ta ce masa haka, da har ta yi masa 3missed calls, ko tana nufin ta ce Haryanzu ba ta san wayarsa ba ce ba?.
Gashi dai yana sane yayi ignoring kiran, amma yana son sanin dalilin kiran.
Yau sai da takawa ya dawo, sannan iman ta fara shirin tafiya gida, rumaisa ta din ga yi mata magiya a kan ta kwana, amma ta ce ba ta gaya wa ammi ba, direba ya zo ya É—auketa ya mayar da ita.
Takawa ya dubi ruma da ta haÉ—e rai saboda Iman ta tafi ya ce "Ya jikin naki?".
"Da sauƙi"
"Kin sha magungunan ko kuwa?".
"Na sha" ta amsa masa a taƙaice, bai sake kulata ba ya ƙyaleta, dan yanayin fuskarta ya nuna masa a fusace take, idan ya biye mata rashin kunya za ta yi masa.
Mai sunan baba kuwa, missed calls ɗin nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya ƙoƙarinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku.
Babban abun da ya ɓatawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira.
Iya ƙoƙarin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar.
Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi É—akinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta É—aga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama.
Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa.
"Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin É—abi'arta ta iyayi.
"Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata.
Sai da ta É—an ruÉ—e, amma ta yi iya yin ta, ta haÉ—a nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?".
"Lafiya ƙalau".
"Dama Anty Rumaisa ce ta karɓi aron wayata ta kiraka, kuma ba ka ɗaga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi haƙuri dan Allah" ta ƙarasa maganar kamar za ta saka masa kuka.
Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata ƴa da yake keɓewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin daɗin sauran muryarta.
Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?".
"Ɗazu ne na je gidanta, ba ta jin daɗi shi ne ta karɓi wayata, ta kira ka, amma ta ji sauƙi".
"Shikenan" ya katse wayar.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin daÉ—in kasancewa da shi ta waya. Wani guntun murmushi ta yi, tana É—aga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo.
"Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale.
"Kamar yaya? Yayan Anty rumaisa ne".
"To meye alaƙarki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido.
Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai".
"Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata".
Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi É—akinta.
Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sauƙi" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice.
***
Tun da Adam ya fara hawo wa step ɗin bene, yake jin ƙauri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnuƙe da hayaƙi, kuma hayaƙin daga kitchen yake fitowa.
A sukwane ya nufi kitchen ɗin, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ƙaurin manja.
"Ke meye haka? Me ki ke yi?"
Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"
Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin kashe gas ɗin, dan tuni suka haɗa baki da iman, direbanta ya ɗuro mata.
Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"
"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Buɗe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi saƙa mai kyau, sai ƙamshin attaruhu take.
Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".
Ta ce "Eh na yadda" ya gyaÉ—a kai ya fice.
Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya leƙa falo, ya hangota tana ta suɗar baki tana cin yaji.
Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.