Sashe 151
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sanyinta ta ce "Anty Nusaiba, maganar ce bana so in general, bana jin daÉ—i sam"
"Amma duk da haka bai kamata ya yi ta magana ki yi masa shiru ba"
Ta É—an kalleshi ta ce "Am sorry".
"To ya zan yi da ke jarumata, bana son yadda ki ke yi mini wulaƙanci, idan wani abun na yi miki am so sorry for it"
Ta girgiza kai ta ce "A'a babu komai"
"Shikenan, na ga kamar ina takura miki, bari na je gida, Nusaiba take a good care of her please"
Nusaiba ta ce "To uncle J, but you have pay for the service"
Yayi murmushi ya ce "Biyoni mu yi ciniki, za a biyaki ko nawa ne" ta yi murmushi ta tashi ta bi bayansa suka fita.
A hankali iman ta furta "Ohh Allah, ka iya mini, Allah ka yi mini zaɓi na alkhairi, Allah kar ka saka Jabir ya gayawa wani yana sona, he has no space in my heart. Ni ba kowan kowa ba ce, duk zaɓin da ka yi mini ina so Allah, Allah ka iya mini" ta ƙarasa maganar tana kwanciya a kan pillowanta.
Sai dai tana kwanciyar, ta ji tamkar an sanys igiyar ƙarfe, an ɗaɗɗaure mata jijiyoyin kanta, ta sanya hannu ta dafe kan ta fashe da wani marayan kuka, ta rasa me ma za ta yi, lamarin nan ya fara bata tsoro, dan kuwa ji take tamkar zata haukace.
Jabir ya kalli Nusaiba ya ce "Nussy, see how your sister is behaving towards me, just because i have feelings on jer, me yasa ba ta so na, meye aibu na?"
"Uncle J, yakamata ka yi mata uzuri, this girl suffer alot in this family, kalli yadda take samun manema, suna tafiya saboda abun da mutane basu da tabbas a kan sa, kalli saboda yarima ya ce yana son ta, kalli wulaƙncin da fulanin yola ta yi mata da cin mutunci, har a gidan nan ma ba ta tsira ba, na waje ma idan sun biyota suna so, sai a samu mai zigasu su daina zuwa. A yanzu ta riga ta ce ba ta son kowa ya raɓeta da sunan soyaya, ba ta son kowa, ka san abu na ƙarshe da ya faru a gidan nan ai, ba wanda bai ji ba, shi ma aka din ga surutu a kai. Dan haka ta ce idan har mijin aurenta ya zo ko ba soyayya, ta ce za ta yi, amma for now, tana buƙatar hutu ne".
"Nusaiba, babu ɗan adam ɗin da baya faɗi tashi da gwagwarmaya da ƙaddara, amma hakan ba ya sanya wa a sare, this is not an excuse da za ta yi denying kowa ya ce yana son ta, ni da gaske ina son iman, amma wace shawara zaki bani a kan ta?"
Nusaiba ta numfasa ta ce "Uncle J, ga ka da takawa, ga ka da Ammi, ai a duniya babu abun da za su ce ta yi, ta ƙi yi muddin bai saɓawa shari'a ba, ka bi ta wurinsu kawai, ina fatan idan komai yayi daidai, zaka kula mini da iman, ka kuma ji tsoron Allah a kan riƙon ta".
"Nusaiba da zan cutar da iman, ba zan aureta ba, ina son ta so na gaskiya ne, abu na gaba ina ga ammi zan samu kawai, takawa zai iya yi mini wasa da hankali, kin san halinsa, bari na je kawai na gode, ki yi mata sannu"
"Za ta ji, ka gaida gida" suka yi sallama ya tafi, ita kuma ta koma.
***
Aiki ya samu ƴan maza fa, domin kuwa su Usman ne suka zaɓowa rumaisa kayan da za ta saka, sai cika take tana batsewa, wannan ya dungure mata ya ce "Ki yi dariya dan ubanki".
Wannan ya ce "Ki ka yi mana shirme dakuwa zaki yi".
Suka shiryata cikin doguwar rigar atamfa, ta sanya dogon hijjabi, Abdallah ya ce "Ina hoda a shafa miki?"
"Ni bani da hoda" ta amsa masa tana É—an hararsa.
Usman ya ce "Jambaki fa?"
Ta ɓata fuska ta ce "Ni fa kun san mai kawai nake shafawa, shi ma ba kullum ba, bani da komai ni".
Usman ya ce "Ikon Allah, lallai kin cika deluwa, kina mace amma ba hoda ba Jambaki, kamar gardi, wallahi ki ka je gidan miji ba kya kwalliya, wahala zaki sha, to yaushe mutum zai ajiye mace, amma shi da ita ba maraba? Ai na ga mama tana da kwalli, shi zaki saka"
Rumaisa ta ce "Yaya usman, idona fa yaji yake idan na saka kwalli".
"Ai ko tsiyayowa zai yi sai kin saka, Abdallah ya riƙeta, Usman ya saka mata kwalli, tana kuka sai ka ce dole"
Mama ta riƙe haɓa tana "Yau nake ganin ikon Allah"
Abdallah har da lakato Vaseline, ya shafa mata a leɓenta.
Huzaifa ya ce "Ai dole idan ya tafi, a yau ba sai gobe ba, a sayo kayan kwalliya ta din ga yaɓawa"
Usman ya ce "Dolenta ma kuwaa"
Aka ɗauko turare aka fesa mata, Usman ya ce "Ranar kamu ni zan kamaki, an ce da turare ake yi ko? Idan na din ga fesa miki, sai kin fara hayaƙi"
"Sai ka ce wata ita ce"
"Koma dai menene, ina sake jaddada miki, ki ka yi mini kwaɓa, da takalmi zan ladabtar da ke".
Ta kalli kanta a mudubi, ta ce "Kalli yadda ku ka mayar mini da ido, kamar wata sheÉ—aniya"
Yasir da yake zaune yana kallonsu yayi dariya ya ce "Koma dai wacece, idan ya zo, baby ka zo, you are welcome ya aiki? Ya family, kamar dai yadda ki ke gani a film, mussaman bollywood".
Ta buɗe baki ta ce "Taɓ, Allah ya tsareni, Bollywood ba taɓa mata suke yi da maza ba, wallahi ya taɓa ni, sai na gantsara masa cizo, babu namijin da zai taɓa jikina in tsaya ina kallonsa, ko a wurin ƴan bindiga, bana yadda, wallahi faɗa ake da ni" ga mamakinta sai ta ga gaba ɗaya sun tuntsure da dariya, Usman ya ce "Wannan bawan Allah yana ruwa, mama akwai buƙatar ilimantar da yarinyar nan kan aure"
Mama ta yi masa shiru, kamar ba ta ji ba, wanda a ranta tunani take yi, ta yaya za ta yi wa rumaisa bayanin wannan al'amari mai girma, yarinyar da ta tashi a kan iya abun da aka nuna mata shine dai-dai a gida, kome za ayi ba zata yadda ta canza ba, yanzu da an ce mata wani abu, tsaf za ta ce kenan da ƙarya ake yi mata.
Wata zuciyar ta ce "Ko da yake, ai ina ga zai ɗan ƙyaleta ta ƙara wayo, tun da saboda karatunta ma mamansa ta ce ayi auren'
'Namiji ne fa' wata zuciyar ta tunatar da ita.
Ta É—an dafe kai ta ce "Yarinya ce, lokacin da aka yi mini aure, shekara sha biyar, na fi rumaisa girma sosai da sosai, amma lamarin aure abu ne mai faÉ—i"
Yasir ya ce "Mama magana ki ke yi ne?"
Ta ce "A'a kallonku nake yi dai".
Mai sunan baba ya shigo, hakan ya sanya duk suka yi shiru suka nutsu.
"Ke ki zo, ga mutumin can yazo, ki É—au abun zama ki saka muku a soro, kar ki sake ki tsaya a waje, balle wannan iyayen saka idon su ganki".
Cikin rawar murya ta ce "Mama ni fa tsoro nake ji, gabana faÉ—uwa yake yi"
Mama ta buÉ—e baki tana kallonta, har idonta ya ciko da hawaye.
"To cinyeki zai yi?" Mai sunan baba yayi maganar yana tsareta da ido. Ta girgiza kai alamar a'a.
"To kukan uban me zaki yi? Wuce dalla, sai kin tayar mata da hankali haka kurum".
Huzaifa ya É—au turare da darduma, ya ce "Bari na yi maza, na je shimfiÉ—a dardumar na fesa turare a soron, sai taho kina taku kamar gimbiya, dan gidan sarauta ba sa son hauma-hauma" ya ruga yayi soron da gudu.
Ya shimfiÉ—a, ya feffesa turare, ya dawo da sauri ya ce "To fito, ki ce masa ya shigo".
Ta fito tsakar gida zari silifas, za ta yi waje, Usman ya riƙeta "Wai ke rumaisa wace irin ƴar baƙin ciki ce? Yasin gidan sarautar nan sai kin je shi, ba zaki mana buƙulun zuwa gida mai kyau ba, canza wannan ɗan iskan takalmin, ko na cire shi, na tsinke ki da mari da shi, kuma idan ya shigo mintuna biyar, ki zo ki ɗauki kayan abincin nan ki kai masa, dole mu koya miki soyayya, dan ba zaki yi aure ayi miki kishiya ba"
Tana cusa baki, ta sauya wani ta fita, bagazan-bagazan ta leƙa wajen, ta ganshi a tsaye a jikin motarsa yana amsa waya.
"In ka gama wayar, ka shigo" ta faɗa tana riƙe ƙugu. Kamar bai san ta yi maganar ba, ya cigaba da wayar, ita kuwa ta koma soron, ta zauna ta mimmiƙe ƙafafuwanta.
Ya kai mintuna goma, kan ƙamshin turaren sa ya mamaye ilahirin soron, brown ɗin yadi ne a jikinsa, kansa babu hula, sai zuba ƙamshi yake, ta ɗaga kai ta kalleshi, kamarsa da Sabir ta sake fitowa sosai da sosai.
Ya nemi wuri ya zauna a kusa da ita, ta matsa can ƙarshen sallayar, tana kaɗa ƙafa.
Jin shirun yayi yawa, ba shi da niyyar magana, ya sanya ta ce "Ina wuni?" Ya kalleta ya yi shiru bai amsa ba.
"Ai dama na san ba amsawa zaka yi ba, dan a gida an ce in gaisheka ne, amma idan na gaishe ka, ba amsawa kake yi ba, ai ni na riga na gama sanin halinka kaf, daga A har Z"
Nan ma shiru bai amsa mata ba.
"Taɓ kana da aiki wallahi" ta juya masa baya, ta kalli wani wurin. Ya kalli bayanta, yana jinjinawa tsiwa da rashin jin ta, wai ta san halin sa daga A har Z. Can aka kwashi wasu mintuna, sai ta tuna abun da Usman ya ce mata ta tashi da sauri ta ɗauko kayan abinci nan.
Gaba É—aya suka taso suna tambayarta yaya aka yi?
Ta ce "ba komai"