← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 174

Sashe 154

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi a wani event center, ta shirya taron wunin bikin, sai dai abu ya so ya zama rigima, in da facalolinta da masu goya wa mummy baya, suka din ga ci mata mutunci, wai saboda Aisha ba Æ´ar ta ba ce, ta shirya irin wannan biki haka, kuma aka samo yarinya mara galihu ta aurawa mahaukacin É—an ta.
Duk yadda ammi ta so jurewa sai da ta kusa zubar da hawaye, Nusaiba ba ta da hayaniya, balle iman, Laila ce masifaffiya dama, kuma ba ta ƙasar da ita kaɗai ta ishi duk wani mai bakin magana.

Da la'asar mama ta kira ammi, ta ce mata za a kawo rumaisa nan wurinta, ta gaisheta ta yi mata faÉ—a, sannan a wuce da ita gidanta, ammi ta ce ba sai an kawota ba, saboda wasu dalilai, zuwa magariba zata turo da waÉ—anda zasu É—auki rumaisa.

A yammacin aka yi kilisar dawakai, takawa ya haÉ—e cikin kayan sarauta, rumaisa ma aka yi mata ado da alkyabba, aka yi ta musu hotuna.

Da magariba rumaisa ta yi wanka, ido duk ya kumbura saboda kuka, Yasir da ya shiga ya fita ya ga tana kuka, shi ma sai ya fashe da kuka, ta tashi ta saka kaya ma abu ya gagara mama sai daurewa take yi, amma hawaye ya cika mata ido.

Jiki a sanyaye mai sunan baba ya shiga ɗakin, ya tarar da ita a zaune, tana kuka mai taɓa zuciya.

"Rumaisa" ya kira sunanta, ta É—aga kai ta kalleshi.

"Tashi ki saka kayanki, kar dare yayi sosai".

"Dan Allah mai sunan baba ku yi haƙuri, wallahi na fasa ni ba zan tafi na barku ba, mama dan Allah ku yafe mini ku barni na zauna a gida, ni ba zan iya rayuwa babu ku ba" tayi maganar cikin kuka.

"Tom, mun ji, amma fara saka kayan" da ƙyar ya saka kaya, ya ciro turare a aljihunsa ya fesheta da shi, mata sai rangaɗa guɗa ake yi.

Ta riƙe mama tana wani irin kuka.

Ya saka hannu ya cire nata daga jikin mama, ya ja hannunta yayi waje da ita.

Suna fita mama ta shiga É—aki, ta fashe da kuka, dan an kai in da ba zata iya jurewa ba.

Suna tafe a mota tana kwamce a jikin mai sunan baba, tana ta kuka, kamar ta shiÉ—e.

"Am sorry, kiyi haƙuri haka lamarin aure yake, da haka kowace mace take tara nata iyalin, Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya, ya sanya alkhairi. Ban da rashin kunya da raina miji, mijinki ne ibada zaki je ki yi, ki nemi aljanna na san duk an gaya miki, ki girmama mahaifiyarsa, matar nan ina ganin mutuncinta saboda son da take yi miki. Sannan kuma Sabir ko Allah ya baki naki ɗan, kar ki canza soyayyar da ki ke yi masa, ki yi haƙuri ki saka a ranki, ƙofar sabon ƙalubale zaki buɗe ki shiga. Duk da ƙanƙantarki nauyin aure ya hau kanki sai haƙuri, kiyi haƙuri, ki yi haƙuri, ki jure ki daure duk ƙalubalen da zaki fuskanta wataran sai labari, ina yi miki addu'a Allah ya sassauta miki jarrabawar gidan aure, don babu auren da babu jarrabawa"
Haka ya din ga yi mata nasiha, har suka je gidan, gida ya tsaru kamar ba na rumaisa ba, ko ina ya ji kaya.

Ana kai rumaisa wata ƙanwar ammi, ta sake saka mata alkyabba a kan kayanta, suka din ga yi mata guɗa a ka, amarya ƙanwar maza, dan su suka kawota ɗakin ma.

Sun daɗe tare da rumaisa, kowa da irin faɗan da yake yi mata. Sai da kowa ya watse, Tawagar angwaye suka ƙaraso, gida ba kowa sai tsirarin mutane da zabga-zabgan ƙarti.

Suna zuwa mai sunan baba ya tashi ya ce su tafi.
Rumaisa ta riƙe rigarsa ta tashi tana kuka "Dan Allah yaya umar, kar ku tafi ku barni, ku tafi da ni, ko ku zauna da ni a nan ɗin, dan Allah yaya. Yaya usy, yaya Abubakar, dan Allah duk ku zauna, Abdallah kar ku tafi, Yasir dan Allah" mai sunan baba duk ya kaɗa musu kai alamar su tafi.

Iman tana cikin waÉ—anda suka rage, gaba É—aya tausayin rumaisa ya cika mata zuciya.

A hankali ya fincike rigarsa daga hannunta, ya juya, ta sake riƙo rigarsa.

Ya juya a kausashe ya ce "Wuce ki je ki zauna" a razane ta saki rigar ta sa tana kuka.
Yana juyawa sai hawaye, karo na farko da abu ya daki zuciyarsa ya saka shi kuka. Ya saka hanky ya goge, ya kalli Adam ya ce "Ga ta nan amana ce, marainiya ce, ko ka ci, ko kula da ita" yayi maganar wasu hawayen na cika masa ido.

Adam har mamaki yake, wace irin soyayya suke nuna wa rumaisa haka.

Bashir ya ce "Za a riƙe amana in sha Allah. Yallaɓai aje a rarrasheta dan Allah, tana cikin damuwa".

Adam ya ce "Sai ma ka faÉ—a? Ba daga ni sai ita zaku tafi ku bari, wannan kuma ya rage nawa" dariya abokansa suka yi, suka yi musu addu'a sannan suka watse.

Ya koma ya shiga ɗakin na ta, tana tsaye tana ta kuka, ya ƙare mata kallo sannan ya ce
"Yau sarki mai koriyar alkyabba, ya baki alkyabba saura ɗana ki a kan doki. Sannan ke kuma ki cika alƙawarin sanya shi durƙusa miki a kan gwiwoyinsa".

What's app only please 🙏
Ayshercool.
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

Rumaisa kasa cewa komai ta yi sai jinjinawa ammi kai, baba uwani kuwa har da shewa tana juyi, tana yi wa ammi godiya da karamcin da ta yi mata, a matsayin wadda za ta je ta yi guiding É—in ma'aikatan gidan takawa.

Ammi ta yi wa Adam alamar ya bi ta, ya tashi ya bi bayanta ɗakinta, ta kalleshi ta ce "Takawa, na san auren nan ba son ka bane, zaɓina ne amma dan Allah ina sake roƙon alfarmarka, ka yi haƙuri da yarinyar nan, komai zai wuce zaka yi alfahari da auren nan, ka ga yarinya ce ƙarama, dole za ta yi ta koke-koke na rabata da gida da ka yi, dan Allah ka yi haƙuri da ita. Ko dai wani abun ka yi mata?"

Ware ido ya yi ya ce "Ba abun da na yi mata wallahi".

"A'a takawa, dan Allah ayi haƙuri a bata lokaci, yarinya ce sosai sai ka yi haƙuri"

Adam wata irin kunya ce ta kama shi, ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya nutse don kunya, ya girgiza kai ya ce "Ban yi mata komai ba"

"Na ji ba wai ina son jin sirrin aurenku ba ne, amma dan Allah ka kula da ita, next week idan Allah ya kai mu za a koma makaranta ko?"

Ya ce "Eh, na biya komai ma, ana komawa zan kaita sai kuma na samo direban da zai din ga É—aukota idan bana nan"

Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya ƙara buɗi"

Suka fito, Ammi ta ce a zubawa su takawa abinci su tafi da shi.

Ammi dai ta lura gaba É—aya jikin rumaisa a sanyaye yake, har ta fara tunanin ko takawa dai yayi mata wani abun ne.

Ammi ta zauna a kusa da ita, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Rumaisa, ko akwai wata matsala ne?"

Ruma ta girgiza kai alamar a'a.

"To ki yi haƙuri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi haƙuri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi haƙuri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ƙalubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ƙaunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ƙannensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi haƙuri kin ji rumaisana".

Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah "

Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi.

Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taɓata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba ɗaukar ki zan yi ba" da haka suka ƙarasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta.

Washegari da safe, ta tashi tana É—an goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles É—in.

Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ƙuri da ido, ba ta yi magana ba.

"Baki iya gaisuwa bane?"

Ta É—auke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba"

"Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki.
Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina buƙatar wani abu?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki zauna wuri ɗaya, banda taɓe-taɓen abun da ban saka ki ba".

"To sai yaushe zaka dawo?".

"Lokacin da Allah ya yi".

"Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji"

***
Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan.
Chapter 154 · 0% Book details