← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 174

Sashe 23

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Allah ya kyauta, ka ma dai mayar da ni mahaukaciya, ka je ka ƙarata, tattara kayana ma zan yi na bar muku gidan ku, gobe goben nan zan bar garin nan.
A hankali yasir ya ce "Alhamdilillah, Allah ya raka taki gona"
A rikice ruma ta ce "Haba Gwaggo, ni bana son ki tafi, dan Allah ki zauna bamu gaji da ganinki ba".

Huzaifa ya yi ƙasa da murya ya cewa Abdallah"Ji munafukar 'yar nan, ko a gidan uban waye bamu gaji da ganin na ta ba, mata duk ta addabi mutane?"

Abdallah ya ce "Ashe ka manta wacece ruma, ai wannan yarinyar tsaf sai ta haɗa yaƙin duniya na uku, duk abin da ta san za ta aikata wanda ba a so shi take yi"'

Kamar wasa ruma har da kuka, wai kar Gwaggo ta tafi, ji suka yi kamar su yi wa ruma taron dangi su zaneta.

Ganin ruma na kuka, ya sanya Gwaggo ta ce ba zata tafi yanzu ba, saboda ruma.

*****
Sauri-sauri take yi, tana tafe tana duba agogon hannunta, tana daf da makara zuwa wurin da zata.
Tana ƙarasawa harabar gidan ta ɗan ɗaga murya ta ce "Gali, gani na fito zo mu je na makara"

Cikin girmamawa da murmushi Gali ya taso ya ce "Allah ya taimaki 'yar gaban goshi, Allah ya ƙara miki lafiya uwar ɗakina, ai tun ɗazu ke nake jira, tun da tun huɗu ki ka ce mini"

"Kai dai bari, na tsaya na yiwa Ammi girkin dare, kar na je ban dawo da wuri ba ka san ba komai take ci ba"

Ya ce "Haka ne, bari na fito da motar" ya yi gaba ita kuma ta tsaya.

'yan mata ne su huɗu, suka fito ta ƙofar wani sashi na cikin gidan, suka tunkaro in da take wajen harabar gidan, hakan ya yi dai-dai da fito da motar da Gali ya yi.
Kai tsaye suka tinkari motar ba tare da sun kulata ba, suna ƙoƙarin buɗewa su shiga.
Da sauri Iman ta ce "Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne"

ÆŠaya daga cikin su ta kalleta ta ce "Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?"

Iman ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tuƙi ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa"

Cikin tsawa É—aya daga cikin su ta ce "Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?"

"Me ku ke yi haka a tsatstsaye?" Gaba É—aya suka waiwaya suka kalli mai maganar.
Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

Fauziyya ta cire glass ɗin fuskarta ta ce "Bro, wannan ƙanwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita"
Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce "Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa'anninki ne su?"

Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

"Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl"

Gaba É—aya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.
"Ke zo nan" ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.
Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

"Ina zaki?"

"Napep zan je na hau"

"Wuce ki koma, ba zaki fita ba" yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan. Ba ta ce masa ƙala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta riƙe hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

"Subhanallah, abar ƙaunata ya haka? Meyafaru? ya baki tafi ba?" Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ruɗewa bayan ganinta ta na kuka.

Iman ta share hawayenta ta ce "Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi"

No ban yarda ba, gaya mini"

"Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud".

Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya É—auke gaba É—aya ta ce "Mahmud again? Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?"

Iman ta share hawayenta ta ce "Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya ɓaci, bana son ki damu"

Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Na ji, amma me suka yi miki?"

"Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi haƙuri"

Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce "Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?"

Iman ta É—aga mata kai alamar eh. Ta ja hannun Iman suka bar falon.

****

Cikin rarrashi mama take magana, "Ruma, aiken ki nake son yi, amma bana son ki je ki yi mini shirme, ko ki tsaya a in da ban aike ki ba"

"In sha Allah mama, ba zan tsaya a ko ina ba, fiii zan ware dogayen ƙafafuwana da bala'in gudu na je na dawo"
Mama ta ce "Wane irin gudu kuma? Kalen ki watasar mini da kayan aiken, ki tafi a hankali, ki yi sauri ki je ki dawo"

"In sha Allah zan yi sauri, na je na dawo"

Mama ta gaya mata in da take so ta je, tare da abin da za ta kai, ruma ta sauya kaya ta saka hijjabi, ta fita yi wa mama aike, ta ƙuduri aniyar za ta je ta yi sauri ta dawo ko dan ta farantawa maman.
Tashin farko ta bi ta cikin unguwa, tana tafe tana kalle-kallenta, duk wani lungu da saƙo idan ta bi sai an kira sunanta, dan kusan kowa ya santa.

A ƙofar wani shagon aski ta ga keken Huzaifa, hakan ya tabattar mata da yana cikin shagon.
Murmushi ta yi ta nufi ƙofar shagon askin, da sallama ta buɗe ta shiga cikin shagon.
Duk maza ne a ciki, ga Huzaifa ya zauna a kan kujera za ayi masa aski, jin sallamar mace ya sanya dukkansu suka juya suna kallonta.

"Ohh Huzaifa yau Allah ya yi zaka cire wannan sumar kenan? Kuma wallahi aka yi maka askin 'yan iska kai da mai sunan Baba"

A ƙule Huzaifa ya ce "Ke uban me ya kawo ki nan? Ba ki ga shagon aski bane?"

"To ni ina ruwana da wani shagon aski, ba dai mutane ne a ciki ba, keken ka na gani a waje na san kana nan, na ce bari na leƙo na ganka"

"To na ji na gode, fita ki bar wurin nan"

"To sai ka tsaya na gama kallon kalandar askin nan, sai na tafi " tayi maganar tana riƙe ƙugu, tare da zubawa kalandar ido.

"Ni wannan yarinyar ba ke na taɓa rabaku faɗa da wasu yara ba, kun dawo daga makaranta?" Cewar wani da yake zaune shima yana jiran askin.

"Eh nice, me na yi kuma?"

Ya ce "A'a gane ki kawai na yi"

"To yanzu da ka gane ni lada nawa aka baka?"

Mai aski ya ce "Deluwa, dan Allah ki yi haƙuri, wurin nan duk maza ne, ki je aiken da aka yi miki, ko kuma in saka a riƙe mini ke na yi miki aski"

"Aikuwa da sai ka kasa zaman ÆŠorayi, sai na saka yayyena sun kakkaryaka sun zubar, ni zaka yiwa aski?"

Huzaifa ya miƙe tsaye rai a ɓace ya ce "Bi ƙofar da ki ka shigo ki fita"

Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Huzaifa ba ayi maka gwaninta, daga ziyara?"

"Ki fita na ce, wallahi na zo in da ki ke sai na gwara kan ki" ja ta yi ta tsaya cike da taurin kai tana kallon idonsa, hakan ya ƙara tunzura shi, yayi kanta amma suka riƙe shi, ta fita da gudu daga shagon.

Tana fita ta yi ƙwafa, ta tura keken sa ta ji bai rufe ba, keken ya fi ƙarfinta, amma ta haye ta yi gaba.

Wani ya leƙa shagon askin ya ce "Huzaifa ƙanwarka ta ɗau keken ka fa ta tafi"

Da sauri ya miƙe ya leƙo, ai tuni ta kusa ƙarshen layin, ya san ko da ya bita ba zai cimma ta ba.
Kawai yayi tsaki ya koma ya zauna, zuciyarsa na tafasa, 'yan cikin shagon suka din ga dariya, kowa na tofa albarkacin sa a kan halayar ruma.

Haka nan tun da ruma ta fita, mama ta kasa nutsuwa, kawai dai gata nan ne dai, ta fara dana sanin dalilin ma da ya sanya ta aiketa.

Tun tana saka ran ta ga ta ina za ta shigo gidan, har ta fara fidda rai, yanzu ba ta fiye É—aga hankalinta ba, idan ruma ta fita makaranta ko aike ba ta dawo da wuri ba, sai dai fargabar mai za azo ace mata ruman ta aikata.

Aikuwa ilai, tana cikin wasi-wasi sai ga sallamar wata matashiyar budurwa da wata yarinya, yarinyar bakinta a fashe, jikinta duk kwata ga fasashshiyar roba, da sauran gari a cikin ta, yarinyar sai kuka take, yawu da jini yana zuba daga bakinta.

Cikin kaÉ—uwa mama suka gaisa da matashiyar yarinyar, mama ta hau tambayar ba'asi.

Babbar ta ce "Dama cewa aka yi na zo gidan su na faɗa, ruma ce ta taho a kan wani ƙaton keke kashe gardi, ta taho da gudu, ƙanwata ta karɓo niƙa, ta bugeta da keken ta faɗa kwata, ita ma ta faɗi a gefe, ta tashi ta karkaɗe jikinta ta hau keken ta gudu, kuma ba iya ƙanwata ta buge ba, tun da tana tafe tana faɗuwa a kan keken"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Allah kai ka jarrabeni, Allah ka dube ni, ka bani ikon cin wannan jarrabawa" mama ta kamo hannun yarinyar da aka jefa kwatar, ta wanke mata jiki, ta basu dubu ɗaya tare da basu haƙuri ta ce zata zo har gida ta basu haƙuri.

Gwaggo kuwa ta hau masifa "Wallahi mutanen maraya ba ku da kara a kan ɗa, yanzu saboda wannan ɗin aka wani aiko yawon kan ƙara, ai ɗa na kowa ne, kuma fitinar maraya ai daban take"
Chapter 23 · 0% Book details