← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 174

Sashe 74

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin*

*5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14.  Supplement na whitening/glowing skin*

*15.  Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*

Gaba É—aya jikin ruma yayi sanyi, bayan ta gama gaya mata abin da zata gaya mata, sai da ruma ta yi shiru ba ta ce komai ba, tana nazarin abun da ta gaya mata.
Haka suka wanzu, ba su rintsa ba a daren, sauran mutane sai dai wanda yayi juyi ya yi wa Aisha sannu. Lokaci lokaci kuma sai ta danƙi hannun ruma tana wani irin yinƙuri da kakari, ita kaɗai ta san abun da take ji, ruma kuwa sai dai tayi ta mata sannu da addu'a Allah ya bata lafiya. A haka har gari ya waye, ta ɗaga ruma ta ce ta je ta yi salla.

Da ƙyar ruma ta iya tashi, jikinta da jinin nan ta yi salla, dan ba ta da wasu kayan, kuma ba ta da ruwan wankewa, jikin ruma duk a sanyaye yake.

Tana idarwa ta nufo in da Aisha take, amma ta ga wasu daga cikin matan wurin sun kakkare Aisha, suka hana ruma ƙarasawa, sun kewayeta.

Ruma ta ɗan ƙare musu kallo ta ce "Wai me ku ke yi haka ne?, da can baku kulata ba ta kwana babu bacci, sai yanzu, ku bari na ganta mana meyasameta?" ɗayar ta ce 'yi haƙuri, zaki ganta ne haihuwa za ta  yi "

"To shine zaku wani kareta, ba amayo shi kawai za ta yi ta bakinta ba, ku matsa dan Allah"

Kakarin Aisha ta jiyo tana salati, tana kiran sunaye daban-daban, ta shiga kiran sunan ruma.

Ruma ta gigice, sai dai matan suka cika mata ido ta kasa yi musu rashin kunya, dan duk da girmansu.

"Anty Aisha, kin ganni a nan sun hanani zuwa wurinki, meya same ki?"

Jin kukan jariri ruma ta yi ya karaÉ—e ko ina, sai hamdala Aisha take tana nishi sama-sama. Ba su farga ba, sai ganin ruma suka yi a tsakiyar su.

"Anty Aisha kin haihu? Sannu"

"Yauwwa ruma, kin gani ashe babyna bai mutu ba"

Sam hankalin ruma bai kai daga ina ɗan nan ya fito ba, ita dai ta ga jaririn a kan Aisha ta ce "Ai dama na gaya miki yana motsi, yana nan da ransa bai mutu ba" ruma ta mayar da hankalinta kan jagwalon da yaron yake ciki, ga jini face-face abun babu kyawun gani, yaron ƙato da shi sai tsala ihu yake, bakinsa yana karkarwa saboda sanyi.
Matan suka shiga laliben abin da za a yanke cibiya da shi.

Aisha kuwa ta riƙe hannun ruma sai murzawa take tana cigaba da salati.

Su kansu 'yan bindigar rasa abun yi suka yi, tausayawa Aisha za su yi, ko yaya za su yi mata, basu taɓa kamo wadda ta haife musu a wuri ba, sai a wannan karon.

Ruma hijjabinta ta bayar, aka nannaÉ—e jaririn, sannan aka saka shi a mayafin Aisha, aka É—ora mata shi a jikinta.

Haka ta yi ƙoƙarin rungumeshi, amma ta kasa ɗaga hannunta, sai ruma ce ta riƙe mata shi, ta din ga kwarara masa Addu'a, tana saka masa albarka daga baya ta koma yi wa rumaisa Addu'a.

"Anty Aisha, to ki tashi zaune mana, idan barde ya zo ya kawo abinci sai ki ci, ki ba shi ya sha kuka yake"

"A'a ruma, ba zan iya tashi ba, ki yi masa addu'a kawai, na bar miki shi halak malak, na bar miki shi har abada, daga yau ke ce ummansa, ubangiji Allah ya raya miki shi da imani, ki saka masa duk sunan da ki ke so"

"Kar dai zafin ciwo ya sa ki ce kin bar mini shi, daga baya ki zo ki ce ba haka ba"

Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, É—aga kai ta kalli yadda jaririn yake ta motsi a cikin zani, ko arzikin wando bai samu ba.

Hawaye ya zubo daga idonta  ta ce "Allah ya rayaka, ka kula mini da baby rumaisa na".

"Dan Allah anty aisha ki daina wannan maganganun, ni bana jin daÉ—i, tsigar jikina ma duk tashi take yi. Sun ce za su kai ki asibiti, yanzu jira zan in ga gudun ruwansu, idan basu zo sun kai ki ba, in je in tayar da tarzoma, in tayar wa da kowa hankali".

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki canza hali ba ai" tayi maganar cikin ƙarfin hali tare da murmushi.

A hankali take salati tana juya kanta, ruma ta miƙe da jaririn ta bawa wata mata ta ce "Goya mini shi". Matar ba ta yi wa ruma musu ba ta goya mata shi, dan kamar tsoron ruma suke ji, sun ga yadda su kansu mutanen ke lallaɓata, sun tsoron su ɓata mata rai, a kashe su.

Ta juya wa aisha bayanta ta ce "Ya ki ka ganshi a bayana?"

"Yayi miki kyau sosai, Allah ya raya miki, amma baki gaya mini sunan sa ba"

Ruma ta yi murmushi ta ce "Zan gaya miki, sai an kai ki asibiti tukuna".

Ta ja numfashi ta ce "Dan Allah samo mini ruwa na sha ruma".

Ruma ta tafi da sauri ta karɓo ruwa a wurin su sha tara, sai buga waya suke suna magana a kan Aisha".

"Wai dan Allah yaushe za a kaita asibitin ne, tana shan wahala fa sosai ".

"Za'a kaita, mota muke jira a kawo" suka faÉ—a dan kwantar mata da hankali.

Ta dawo ta sake kallon jikin Aisha, tamkar an tsomata a bokitin jini, ta yi jalaf kamar an zuba mata.

Ruma ta ɗagota ta fara bata ruwan, maƙwarwa biyu kawai ta yi ta ce "Alhamdilillah" daga nan bata kuma magana ba.

Ruma ta ce "Masha Allah, ai gara ki yi baccin sai ki huta, Allah ya sa motar ta zo da wuri.

Ta ƙulle bakin ledar pure water, ta ajiye, ta gyara wa aisha kwanciyar kanta.

Ta koma tana ta zagayawa tana jijjiga jaririn da yake bayanta, sai dai yaron ya din ga tsala ihu, kamar ana tsoma shi a wuta.

Ruma ta koma wurin Aisha ta tattaɓata ta ce "Anty Aisha, ki tashi ki gwada shayar da shi, kin ga sai kuka yake yi" shiru Aisha ba ta motasa ba.

"Anty Aisha, har baccin naki yayi nauyi haka? Ki tashi kuka yake" taga matan da suka karɓi haihuwar suna kallon kallo, suna kallon ruma.

"Dan Allah ku zo ku tasheta mana" tayi maganar tana sake jijjiga Aisha.

Ɗaya daga cikinsu ta zo ta tattaɓa aisha, suka haɗa ido da ɗaya daga cikin 'yan bindigar, mai dukan ruma wato sule, ta girgiza masa kai, yayi mata alamar ta yi shiru.

Ta kalli ruma ta ce "Ki ƙyaleta, bacci ne a kanta, ki bari ta huta kin ga haihuwa ta yi".
Chapter 74 · 0% Book details