← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 174

Sashe 156

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ƙarya nake ba, zuwa ta yi wai za ta gyara mini ɗaki, ni kuma daga wanka na fito ban saka kaya ba, kawai cewa na yi ta bar shi zan gyara da kaina shikenan fa"

"Ba ta haifeki ba, me za ta gani?"

Da sauri ta kalleshi ta ce "Taɓ, ni wallahi ba zata ganni ba".

"To me za ta gani?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba.

Ya girgiza kai ya ce "Kasancewar ta na yi miki aiki, ba ya na nufin ki rainata bane, ita ce babbar hadimar ammi, muma muna girmamata. Ga abinci can sun girka, ki je ki karya".

"Na ƙoshi" ta faɗa cikin jin haushi, dan ita ba ta ga abun da ta yi wa baba uwani ba.

"Kin ƙoshi saboda me?"

"Ni so nake na din ga girka abincina da kaina, ammi ta ce kar na yarda da kowa, kar na je ayi mini aisiri a cikin abincin"

Tattara hankalinsa ya yi a kan rumaisa sanannan ya ce "Waye zai yi miki asirin?"

Ta ce "An ce a gidan sarauta ana asiri, dan haka ni ba zan ci wannan abincin ba".

"Ai dama me hali baya fasa halinsa, kin huta, sai dai idan ba zaki ci abinci a gidan nan ba, idan ki ka sake na ganki a kitchen da sunan zaki yi girki, sai na saɓa miki, ba zaki haɗa mini gobara a gida ba, kuma ki cigaba da ina magana ki na yi mini gatsali, zaki ga yadda zamu yi da ke"

Ya mayar da hankali a kan system É—in sa.

Jin sa kawai take yi, amma ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta ci abincin nan ba.

Ya tashi ya shiga É—akin sa, ya fito da mukullin motarsa, ya fice ba tare da ko kulata ya yi ba.

Yana fita ta sauka ƙasan benen, ta tarar da su baba uwani suna aikace-aikace.

Tana ganin rumaisa ta saki fuska tana faɗin "Uwar ɗakina, sannu da fitowa, kina buƙatar wani abun ne?"

Rumaisa a ran ta ta ce, ji matar nan kamar ba yanzu ya ce ta fito ranta a ɓace ba.

"Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga ɗakina ranki a ɓace, kamar baki ji daɗin abun da na yi miki ba, ki yi haƙuri dan Allah. Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai".

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar É—akina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"

Ruma ta ce "A'a na iya aiki, zan din ga yi da kaina". Baba uwani ta bi rumaisa da kallo, ta shiga cikin kitchen ɗin, ta ɗebi indomie, da abubuwan da take buƙata.

"Indomie zaki ci? Ko in turo barira ta dafa miki".

"A'a na iya girki" ta juya ta nufi stairs.

Mamaki ne ya cika baba uwani, sai a yau ta fuskanci yanayin rumaisa fetsararriya ce.

Ko da rumaisa ta je kitchen É—in ta na saman bene, babu gas a cylinder ta, dan haka a kan electric ta dafa indomie da tea ta zauna a kitchen, ta ci kayanta, ta yi wanke-wanke.

"Ke amarya kina ina ne" ta ji muryar Aliyu a bazata.

Da gudu ta fito falon, ta É—ane jikin Aliyu tana murna.

Shi da mai sunan baba ta gani, ta saki Aliyu ta nufi mai sunan baba.

Murmushi yayi ya riƙeta da hannu ɗaya ya ce "Ya kike?"

Take ta fara kuka ta ce "Yaya shi ne ku ka ƙi zuwa"

"To yanzu ba gamu ba, idan kuka zaki yi zamu koma".

Ta share hawayen ta ce "na daina"

Zama suka yi Aliyu yana ta kallonta yana "Inyee amarsu ta ango, to yanzu ma mama ba ta san zamu zo ba, wai kar mu saka ki kuka, yaya Umar ya ce mu zo mu ganki"

"Aikuwa kuka na din ga yi, yau ne kawai ban yi kuka ba".

Aliyu ya ce "Ke, na ga wasu mata a ƙasa su waye?".

Rumaisa ta ce "Wai hadimai ne, su suke aikin gidan".

"Saboda me, ke baki iya bane?".

"To ya zan yi, ammi ta ce gidan yayi mini girma ba zan iya aikin nikaÉ—ai ba".

"Ke, wannan dattijuwar za ta yi saka ido, kamar mara gaskiya kin ga yadda ta din ga binmu da kallo, wai su waye mu daga ina muke?"

Rumaisa ta ce "Ni ina ruwana, tun da ba a kaina suke ba".

Mai sunan baba ya ce "Da ruwanki mana, ki dai kula da kan ki sosai ".

Sallamar iman ce ta kaste musu hirar, rumaisa ta ce "Yeee, yau baƙina da yawa"

Idonta bai sauka a na kowa ba, sai cikin na mai sunan baba.

Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau " ya amsa yana kawar da kansa.

Ta gaida Aliyu ma, ya amsa mata cikin sakin fuska.

Rumaisa ta karɓi Sabir tana murna.

Kamar kullum, tsoro da fargaba ya mamaye iman, kasancewar, mai sunan baba a wurin.

"Anty iman, na zaci ba za a kawo shi ba fa".

"A'a za a kawo shi, amma ba bar miki za ayi ba, sai an haÉ—a masa kayansa tukuna".

Zuwan Iman ya sanya mai sunan baba tashi ya cewa Aliyu su tafi.

Kamar rumaisa ta yi kuka ta ce "Mai sunan baba baku daÉ—e ba fa".

"Eh, ai mun zo dai, tafiya zamu yi sauri muke yi "

Iman ta ce "Idan saboda ni ne, bari in tafi, takawa ya mayar da sabir É—in".

Ta yi maganar tana tashi.

"Meyasa zamu tafi dan kin zo? Nemi wuri ki zauna ba zama zamu yi ba dama" ya mayar da idonsa kan rumaisa ya ce "Take care"

Daga haka yayi wa Aliyu alamar su tafi, rumaisa ta ce zata rakasu, amma ya ce ta yi zamanta, ya ajiye mata kuÉ—i, suka fice.

Kuka rumaisa ta yi ta yi, iman tana rarrashinta, ita kan ta tana mamakin irin halina bawan Allah nan.

Kasancewar iman na nan, ga kuma Sabir, ya sanya rumaisa ta haƙura, suka shiga kitchen ita da iman suka yi girki, iman ta tayata ta ɗebo wasu daga kayan abinci daga kitchen ɗin ƙasa zuwa na sama.

Iman ta din ga mamakin yadda rumaisa ta iya girki.

Rumaisa ta ce "Hmm, tun ba a barina na yi a gida, in yi in jagwalgwala har na iya, yaya Abdallah tare muke girki, har a YouTube yake ganin girki mu gwada, daga baya na gane girkin wahala ce, na daina".

Iman har bayan la'asar tana nan, baba uwani na yi tana hawa benen, wai ko suna buƙatar wani abun.

Direba har ya zo É—aukar iman, takawa bai dawo ba, haka ita ma iman ta tafi, gidan yayi mata shiru da yawa.

Sai yanzu take jin haushin tafiyar su mai sunan baba, ko a waya basu kira mata mama ba.

Baba uwani ta shigo falon da sallama da kayan abinci, ta ce "Uwar É—akina, ga abincin mai gida, da naki na dare".

Rumaisa ta ce "A'a ai mun yi girki da iman, mun rage masa".

"To wannan É—in a koma da shi kenan?"

Rumaisa ta ce "Eh, abincin ma a daina kawowa kawai".

"Amma saboda me?".

Ruma ta ce "Saboda na daina wahalar da ku, na iya girkin nima"

'Amma ai giwa ba ta ce mana haka ba".

Ruma ta ce "Da gaske nake na iya, kar ki damu"

Baba uwani ta fara jin haushin, rashin yaddar da rumaisa take nuna wa yadda taƙi sakin jikinta da ita.

Rumaisa ba ta damu da sanin dawowa ko fitar Adam ba, idan ba wani abu take buƙata ba, dan haka har ta yi bacci ba ta san ya dawo ko be dawo ba.

A cikin bacci yake jin kuka sama-sama, ya buɗe idonsa ya ji ana taɓa shi ana kuka.

Ya tashi sosai ya ce "Waye wannan?"

Ƴar siriryar muryarta ya ji tana cewa "Ka tashi zan mutu, dan Allah ka tashi!"

A burkice ya tashi, ya kunna fitilar wayarsa ya haskata, rumaisa ce a tsaye riƙe da hannunsa, tana kuka.

Ayshercool
08081012143
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce "Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu".

"Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na É—auko ki ba".

"Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba".

Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta riƙe hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji.
Ya sake kallonta ya ce "You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini ɗaki, wancan ɗakunan zaki ɗauki ɗaya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can" ya ƙarasa maganar yana sakar mata baki.

"Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki"

"Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ƙarata" ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom ɗin.

Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banÉ—aki.
Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka.

Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa.

Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ƙyam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauke shi.

Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa, ta duƙunƙune a cikin alkyabbar ta hau bacci.
Chapter 156 · 0% Book details