Sashe 70
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Gaba ɗaya tsaya wa suka yi suna kallon su, Ammi ce kawai ta iya ƙarasawa tana ƙoƙarin ƙwace Iman "Me ka ke yi haka ne takawa, iman ce fa"
A hankali ya saki wuyan iman yana ƙare mata kallo, jikinta duk yayi ja saboda azabar wahalar da ta sha.
"Kalli fa ka gani, iman ce fa takawa"
Kamar wanda ya warke daga ciwon hauka, haka ya din ga bin Iman da kallo, kamar zai fashe da kuka ya ce "Iman yi haƙuri, ban san ke ba ce, hannunki kawai na ce zan riƙe, na ga kin koma wata mata zaki caka mini wani abu, yi haƙuri iman, Ammi ban san iman ba ce ki bata haƙuri"
Nusaiba ce ta kalli su Fauziyya da suka yi tsaye suna kallon abun da yake faruwa, ta ce "Anty Samha ba wani abu, zaku iya tafiya".
Samha ta ce "Ba zamu tafin ba, a kan ki muke ko yayanki ne ke kaÉ—ai".
Ammi ta É—ago iman tana yi mata sannu, iman ta jinjina mata kai.
Ammi ta ce "Ina maganinsa yake? shegiyar gardama irin ta sa ɗauko in shafa masa" A hankali iman ta yinƙura, ta je ta saka mukulli, ta buɗe wata drower, ta ɗauko wata jarka cike da wani mai.
Ƙurii Fauziyya ta yi, tana kallon in da iman ta ɗauko maganin.
Adam yayi zuruu da ido yana bin su da kallo, can ya sauke idonsa a kan su samha, cikin tsawa ya ce "Get out" sai da suka razana, kan su yi wani yinƙuri ya sake daka musu wata tsawar, cikin rige-rige suka yi waje da gudu.
Ammi cikin damuwa ta ce "Takawa, meye ya ɓata maka rai haka ne?"
Kamar mai shirin zaucewa ya hau surutai, "Ni na ce ina son sarautarsu ne? Su barni in ji da abin da ya dameni mana, me na yi masa? Idan ya kuma takura mini zan kashe shi, zan shanye jininsa gara ma ki gargaÉ—e shi ya fita a hanyata".
Cikin tsawa Ammi ta ce "Adam! Kar na sake jin ka furta wannan maganar, wan ubanka ne fa, ban hanaka zancen shan jinin nan ba, sai ka ce maye?"
Nusaiba ta ce "Ammi ba a hankalinsa yake faÉ—ar shan jinin nan ba, ki yi masa a hankali".
iman shammace shi, ta shafa masa maganin a fuska, a take ya yi atishawa, sai kuma a hankali ya sulale ya kwanta a ƙasa ya hau bacci.
Hawaye Ammi ta shiga zubarwa, iman da Nusaiba suka yo kanta gaba É—aya "Haba Ammi, idan ki ka yi kuka mu kuma mu yi yaya, dan Allah ammi ki daina ki yi masa addu'a" Iman tayi maganar hawaye na cika idanunta.
"Iman, ciwon da nake tunanin ya rabu da shi, yana neman ya dawo daga rai ya ɓaci sai ya hau maganganu, ya fita hayyacinsa, ina zan saka kaina, saboda tsabar neman magani na fara tsoron kar in faɗa hannun mushirikai na rasa imanina, sanadin ciwon nan har jita-jita aka din ga yaɗawa wai maye ne fa, da wanne zan ji?".
Nusaiba ta ce "Dan Allah ammi ki daina damuwa, Addu'arki fa ba ta tafiya a banza, zai warke in sha Allah "Astagfirullah, Allah ya yaye maka Adam, duk wani hope É—ina a kanka yake, ban ce wani ne ya yi maka bs, Allah ne ya É—ora maka, ina fatan ya yaye maka"
Suna tsaka da maganar ya fara surutai "Sidi, ku je ku dubo mini yarinyar nan, na gaji a kan me zata din ga zuwar mini a bacci ko in din ga jin kukan ta a kunnena, anya mutum ce? ku je ku duba mini ni bani da lokaci" kamar sun je cinema haka suka zuba masa ido, can kuma ya toshe kunne yana faɗin "Ki daina yi mini kuka, bana son kuka, meye alaƙata da ke ne?"
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin ammi da su Nusaiba.
A hankali nusaiba ta ce "Yaya maganar wa ka ke yi ne?"
Tun da Nusaiba ta yi magana bai sake cewa komai ba, yayi shiru bacci yayi awon gaba da shi.
***
Idan da sabo ruma ta saba, dan haka yanzu baccinta take cike da mafarkan su Mama da yayyenta, sai dai babban abin da yake addabarta bai wuce ganin mutumin nan da ta tsana a cikin mafarkinta ba, wanda hakan ba ƙaramin haushi yake bata.
Yanzu ma mafarki take yi, tana zaune tana kuka a cikin dajin nan, takawa ya ɓullo sanye da wasu baƙaƙen kaya, ya ratso mutanen da suke wurin, ba wanda yake iya ganinsa sai ita, ya zo ya tsaya a kanta, ya miƙa mata hannu ya ce "Taso mu tafi"
Ta waiwaya tana dubawa ko akwai wanda yake ganin sa, "ba zaki taso mu tafi ba kin tsaya kina kalle-kalle?"
Cikin tsiwa ta ce "Eh ba za'a taso ba ɗin ni na gayyace ka?" Tayi maganar a fili, tana buɗe ido, tsaki tayi tana ƙoƙarin gyara kwanciyarta ta ce "Aikin banza, ko me yake kawo shi mafarki na oho, idan na kuma ganinka a baccina, sai na yi maka rashin mutunci, dan wallahi sai na rama abin da ka yi mini"
"Ke da waye ne baby rumaisa"ta ji muryar anty aisha.
Ruma ta sake buÉ—e ido ta ce "Ba kowa".
"Haba dai ba kowa, tun ɗazu ki ke surutu fa kina masifa a cikin bacci, har wancan yake cewa zai taka ƙafarki ki tashi,"
Duk da duhu ne, Ruma ta zare ido ta ce "Haba dai, me nake cewa?"
Aisha ta ce "Ina ta fama da kaina ban riƙe ba, amma dai faɗa ki ke da wani a bacci"
Ruma tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani mara kirki ne yake zuwar mini, taimako É—aya Allah zai yi masa, shine na mutu a wurin nan, amma muddin na fita ko ni ko shi, sai ya gane bashi da wayo"
Anty Aisha ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka?".
"Baki san rashin mutuncin da yayi mini ba, nonona ya taɓa mini, kuma mama ta ce duk wanda ya taɓa nan wurin na zama 'yar iska cikin shege ne zai fito mini"
"Ya salam, ke ya aka yi ya kai hannunsa nan wurin?"
"Sa wa yayi aka ɗaukoni, wai zai yi mini warning, ya shaƙo hijjabina ya taɓa wurin, ni kuwa na din ga bin diddigi sai da na gano gidansu, na je na rubuta masa wasiƙar rashin mutunci na ce a bashi"
"Kai ruma lallai jan wuya ke ce, irin wannan ƙarfin hali haka?"
"Rabu da shi, ai wallahi ya bari na fita daga wurin nan zai gane kurensa, Anty Aisha wai ke a wani gari kike?"
"Zan gaya miki ruma, na san zuwa yanzu labari ya samu mijina da dangina abin da ya faru da ni, sai dai ban ga alamar kuɗin fansa suke so ba,. Tun da sun ƙi yin waya su faɗi abin da za s bayar idan.... Ba ta ƙarasa maganar ba ta riƙe ƙugunta ta ce "Washhh"
A ɗan rikice ruma ta ce "Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki miƙe ƙafar to".
"A'a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki".
Ruma ta ce "A'a ai ba zan iya komawa ba kwanta".
A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ƙafafuwan rumaisa, Ruma ta ce "Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya" Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.
"Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daɗi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing ɗin gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ƙaddara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki".
Tayi murmushi ta ce "Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani"
"Ɗaga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba" ruma ta faɗa rai a ɓace.
"Haba ruma, ni É—in ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada". Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce "Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba"
Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ƙila a haɗa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taɓata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.
ÆŠayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce "yau kun yi faÉ—a da uwar taki ne?"
"To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana'ar banza".
"Ni ki ke cewa sa ido sana'ar banza, dan kin ga ana ƙyaleki?"
"Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu'a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?"
"Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya".
Ruma ta ƙarasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ƙasa da muryarta ta ce"Ka san meya haɗani da anty aisha muka yi faɗa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi"
"To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?"