← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 174

Sashe 155

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewar bayan mai hoton da ɓangaren su Adam suka ɗauko, Abdallah ma ya ɗauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura su group ɗin su, na ƴan gidan.

Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan É—an shiga kasuwa, hotunan suka shigo.
Suna da yawa ya sauke su, ya fara buɗewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ƙanwarsa.
Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman É—in, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman.
Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu.

***
"Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya ɓoye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike da ƙorafi.

Adam ya ce "Koma menene bai kamata ka ji haushi ba, yanzu ba gashi ka ji ba, ko da yake gara kai a kan Jamil, ni Jamil zai ɗauki gaba da ni, yaƙi zuwa wurin ɗaurin aurena, ni na karɓi ƙaddarata dan meyasa shi ba zai ɗauka ba".

Jabir ya ce "A'a takawa, so so ne fa, amma son kai ya fi, Samha ƙanwarmu ce ga ta gida, amma ace ka auro wata a waje, wadda ba ta kaita komai ba, babu daɗi".

"Amma har ya kai ayi gaba da ni saboda hakan? Meye aibun rumaisa idan aka kamanta shi da abun da ta yi mini na sadaukarwa, bai kamata gaba É—ayanmu idonmu ya rufe ba, idan akwai rabo a gaba sai ka ga na aureta, amma a yanzu ban zaci haka daga Jamil ba, amma zan shiga wurin aiki, zamu haÉ—u da shi mu yi magana"

Jabir ya ce "To shikenan, har ka gama amarcin kenan ka fito, bai yi wuri ba komawarka aiki ba kuwa?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bai yi ba, ita ma sai a bar ta ta huta. Kai ni har mamaki nake yi yadda kai  ba a saka maka ido ba, ko auren fari ba ka yi ba, amma ba ruwan wani da kai, duk mu aka sanya wa ido"

Jabir ya yi dariya ya ce "Bayan ka ce ba zaka bani iman ba, ai ni na zaci kai zaka aureta"

Adam ya ɗan ɓata fuska ya ce "Please mu bar wannan zancen"

Jabir ya ce "Shikenan, tun da baka so"

***
Rumaisa ta rasa abun da yake yi mata daÉ—i, zaman shirun nan duk ya isheta.

Ta saman benen take kallon harabar gidan, da gidajen da ke maƙwabtaka da nata, duk manyan gidaje ne, sannan kowane gida a rufe yake, ko gilmawar mutane ba ka gani, sai dai a cikin mota.

Mai gadin ta ga ya tashi ya buɗe gate, nan da nan ta fara murna ta yi baƙi.

Ta koma É—akinta da sauri, ta saka hula a kanta, ta fito, sai dai ta yi turus lokacin da ta ga baba uwani, da wasu matasan mata guda biyu.

Jiki a sanyaye ta ce musu "Ina wuni?"

Baba uwani ta yi murmushi ta ce "Ranki ya daÉ—e ai mu zamu gaisheki, barka da wannan lokaci? Mun same ki lafiya?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan tsorace.

"To kamar yadda giwa ta yi miki bayani jiya, ga ma'aikatanki nan, sannan kuma ni ce cikon ta ukun, zamu zauna tare da su a nan, na din ga lura da yadda zasu gudanar da aikin".

Rumaisa ta ce "To sannunku".

Baba uwani ta ce "Yauwwa, wani É—akin zamu zauna, da kayanmu muka zo".

"Ku zaɓi duk wanda ku ke so" rumaisa ta yi maganar tana kallonsu.

Ta nemi wuri ta zauna a falo, baba uwani ta zaƙe ta fara dudduba ɗakunan da suke saman benen.

Ta shiga ɗakin rumaisa, ta ƙare masa kallo, ta fito tana faɗin "Allah ya taimake ki, ashe an shirya miki kayan, ko takawan ne ya shirya miki su?"

Rumaisa ta ce "A'a ni na yi"

"Masha Allah, to bari É—auki wancan É—akin, tun da na ga É—ayan kamar babu kowa a ciki"

Ita dai rumaisa ba ta ce komai ba, ta ƙare ta shiga kitchen tana dudduba kayan kitchen ɗin Rumaisa.

Ganin sun isheta da kallo, sauran mata biyun da ko sunayensu ba ta sani ba, ya sanya ta tashi ta koma É—akinta.

Ta buÉ—e window ta cigaba da kalle-kallenta, ta hango baba uwani a bayan gidan, tana waya. Ba ta jin mai baba uwani take cewa, sai dai da alama kamar wayar ta ta ta sirri ce.

Baba uwani kuwa cikin ladabi take waya da Samha.

"Ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurareni, bana son a samu kowane irin akasi a kan aikin nan, ki zuba mini ido sosai, duk abun da yake faruwa ki din ga sanar da ni, ina fatan kin gane?"

"Na gane ranki ya daÉ—e, duk abun da ki ka ce in Allah ya yarda zan yi, zan zuba ido sosai da sosai"

Samha ta ce "Yayi kyau".

Da la'asar Adam ya dawo, rumaisa ma sam ba ta san ya dawo ba, saboda wunin É—aki ta yi, ko haÉ—a hanya ba ta son yi da baba uwani.

Gyaran murya ya yi, hakan ya sa ta waiwaya ta ganshi a tsaye.

Ya shiga É—akin ya ce "Me ki ke yi ke kaÉ—ai a É—aki?".

"Bakomai"

"Ke ki ka ce wa baba uwani su zauna a É—akin saman nan?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To na ce su koma ƙasa, ba haka ake yi ba. Ga kayan abinci can na sayo, na zuba a kitchen ɗin ƙasa, zasu din ga girki suna kawo mana, sannan zasu din ga yin duk wani aiki na gidan nan, banda gyaran ɗakina, ke zaki din ga wannan ai kin iya ko?" Ta jinjina masa kai.

"Bana son body language, amsa mini zaki yi"

"Eh na iya".

"Good, ki fito zan nuna miki abu".

Ta tashi ta bishi, zuwa kitchen É—in saman benen.

Ya nuna mata kayan tea, manyan gwangwanayen madara da na milo, kayan biscuit na ciye-ciye da sauransu.
Sai cartons na lemuka, da kayan marmari ya ce "Gashi nan, wanda zaki kai É—aki ki kai, wanda za su saka miki a fridge kuma sai ki nuna musu".

"To an gode" ta faÉ—a a sanyaye.

Gani yake yi kamar an sauya rumaisa, duk wannan tsabar rashin jin da tsaurin ido, duk ta yi sanyi, sai dai a ransa ya ce ba a yabon É—an kuturu.

Kasancewar tun a yau su baba uwani suka fara gudanar da ayyukansu, sun yi abincin dare, suka kai wa su rumaisa sama.

Ruma ko kallon abincin ba ta yi ba, ta din ga cin kayan marmari, sai da ta ji ta ƙoshi.
Ta haÉ—a madara da milo, fal a kofi ta tafi da shi É—aki, ta din ga sha ta gaji ta ajiye sauran ta yi bacci.

Ba ta san ma Adam ya dawo ba, sai da asuba ta ji yana babbuga mata gefen gado ta tashi ta yi sallar asuba.

Ta buÉ—e ido ta kalleshi ya ce "Ke ba kya iya tashi salla dole sai an tasheki ne? Kuma haka ki ke kwana da fitila a kunne?"

Ba ta ce komai ba shi kuma ya fice. bayan ta yi sallar, ta ɗan yi baccin safe ta tashi, ta shiga banɗakinta, yanzu duk ta san yadda ake amfani da kayan toilet ɗin, da idan za ta yi alwala, sai ta kunna hot water ta fara, tana tsaka da yi, ta ji ruwan zafi yana ƙona ta, yanzu kuwa duk ta gane kansu.

Wankanta ta yi a nutse, ta fito tana goge jikinta da ruwa, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta.

Baba uwani ta yi sallama, da kayan mopping a hannunta.

Rumaisa ta razana tana neman hijjabi ta saka, kasancewar daga ita sai towel.

Baba uwani ta ce "Haba ranki ya daÉ—e, ai na haifeki, meye na damuwa kuma, gyara miki É—akin zan yi".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ki bar shi kawai zan gyara da kaina, kaya zan saka".

"Ki saka kayanki kawai, aikina zan yi".

A É—an hasale rumaisa ta ce "Ki bar shi kaya zan saka".

Ta kalli rumaisa, ba wata uwa a jikin nata sai tsirfa. Ta juya sumi-sumi ta bar É—akin.

Guntun tsaki rumaisa ta ja ta ce "Wannan mata meye damuwarta ne? Bana son shishshigi", rumaisa ta saba yawonta a gidansu, babu suturar kirki ba ta damu ba, amma ba ta yadda wani na waje ya ganta ba. A gaggauce ta saka kayan, tana son ta yi magana da adam Kafin ya fita.

A falo ta tarar da adam yana danna system, babu alamar zai fita yau.

"Ina kwana" ta faÉ—a ba dan ta na tsammanin ya amsa ba, aikuwa bai amsa É—in ba.

Ta É—ora da cewar "Dama, tambayarka zan yi, yau tun da juma'a zaka É—auko mini Sabir É—in, ammi ta ce za a din ga kawo shi, juma'a zuwa ranar lahadi, sannan dan Allah ka kira mini yaya Aliyu a waya, dan Allah su zo".

Ya kalleta ya ce "Da ni ki ke ko da system É—i na, ko akwai wani bayan ni a nan?" kallonsa ta yi da mamakin rainin hankalin da ya yi mata ta ce "Da kai nake mana".

"Bani da suna ne ko yaya?"

Rumaisa ta ce "Ka na da shi".

"Ok, ya sunana?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

Har ta buÉ—e baki za ta ce Adam, sai ta ji sunan yayi mata nauyi a bakinta, gashi ya tsareta da ido, yayi mata kwarjini sosai.

"Papa" ta faÉ—a a hankali.

Adam ya ce "Waye hakan?"

"Saboda Sabir, na ji ya fara koyar faÉ—an sunanka"

ÆŠan rausayar da kai ya yi, a ransa ya ce "Ashe kina da hankali wasu lokutan '.

A zahiri kuma ya ce "Me ki ka yi wa baba uwani, na ga ta fito daga ɗakinki, kamar ranta a ɓace?".

Ta É—an tura baki ta ce "Ba abun da na yi mata"

"Bana son ƙarya"
Chapter 155 · 0% Book details