← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 174

Sashe 113

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka adam ya tashi ya tafi, yana ta tunani kala-kala a ran sa. Idan har turaki zai fito duniya ya kareshi, zai iya fuskantar duniya ya ce duk mai cigaba da zarginsa idan yana da hujja. Kansa na kashe aisha ya je ya nema mata hakkinta a kotu.
'kar dai shawarar wannan yarinyar mara kan gado zaka É—auka, ta kai ka ta baro' wata zuciyar ta gargaÉ—e shi, tsaki ya ja ya kawar da wannan tunanin a ransa.

Maganar da turaki ya fito ya yi, ta ƙara yamutsa hazo, kowa da abun da yake faɗa, yayin da hakan ya ƙara tunzura wambai, turaki ya ƙara zubar musu da mutunci ta hanyar kare adam.

Yau kwanaki kusan bakwai rabon rumasa da jaririnta, dan haka ta shiga damuwa ba kaɗan ba, tana ta tunani daban-daban a zuciyarta. Wata irin ƙishirwar son ganin yaron ke damunta.
Ta gama shirinta tsaf za ta tafi makaranta, ta fito daga gida har ta nufi hanyar makaranta, ta kalli kuÉ—in makarantarta a hannunta, kawai ta canza hanya, ta nufi titi.

Ta san kuɗin hannunta ba zai kai ta gidansu takawa ba, dan haka ta saɓi hanya da ƙafafuwanta ta dinga tafiya kamar mara hankali.
Tun da sanyin safiya, har rana ta É—aga ta fara jin zafinta sosai a jikinta. Idan ta gaji ta zauna ta huta, idan ta huta ta tashi ta cigaba. Sai da ta ci fiye da rabin tafiyar sannan ta samu napep ta yi masa magiya ya É—auke ta, shi ma in da ya ajiyeta da sauran tafiya, ta sauka ta cigaba.

Sai dai da ta ƙarasa, tana zuwa ƙofar gidan, security suka tare ta.

Ta kalli wanda ya sha gabanta ta ce "Wucewa zan yi"

"Ki je ina?" Ya tambayeta.

"Ciki mana wurin É—ana, ko ba ka gane ni ba ne?".

Ya ce "Na gane ki, sai dai an ce kar mu sake barinki ki shiga idan ki ka zo?"

Cikin mamaki ta kalli securityn ta ce "Waye ya ce kar a sake barina na shiga?"

"Takawa, shi ya ce kar ki sake shiga idan kin zo in ba shi ya ce ba"

"Kam bala'i, wai wannan wane irin mutum ne, shi wane irin azzalumi ne, idan har ba zan din ga shiga ba, ya bani É—ana mana, ai dai ya san ba maula ce take kawo ni ba ko?"

"Ke da shi ne wannan, matsa daga nan"

Wata irin zuciya ta turnuƙo rumaisa ta ce "Wallahi ba in da zani sai an bani ɗa na, wallahi yau sai na shiga gidan nan, wane irin mugun mutum ne shi, ba shi da imani ba shi da tausayi, wallahi sai na shiga sai dai ku kasheni" ta yi maganar tana tunkarar gate ɗin.

Tare gate É—in É—aya yayi, cikin tsawa wani ya ce mata "Ki ka motsa daga nan sai na harbeki"

"To ka harbenin mana, sai me? Allah sai na shiga"

Gaba É—aya ta rasa abun da za ta yi, ta fashe da kuka, saboda uwar wahalar da ta shawo, kan ta samu ta zo, amma ta tarar wai an hanata shiga.

Ta fi mintuna talatin a tsaye a rana tana kuka, É—aya daga cikin masu gadin ya ce "Wannan wace irin jarababbiyar yarinya ce haka?"

"Kai ne baka santa ba, kwanakin baya ta taɓa zuwa gidan nan, zata aikata fiye da abun da ta yi yanzu"

Kamar daga sama, ta hango shi yana tunkaro ƙofar gidan, sanye da ƙanan kaya, kunnensa ɗaya da Bluetooth, fuskar nan tasa fayau ya yi ƙiba abunsa, kan ya ƙarasa gate ɗin rumaisa ta tashi da gudu, ta je ta riƙe rigarsa tana kuka.

Sororo yayi yana kallonta, "Shi ne kace idan na zo kar a sake barina na shiga, ka san da haka ka karɓe mini yarona? To ka shiga ka ɗauko mini sabir ba zan sake zuwar muku gida ba"

ÆŠaya daga cikin security zai yi magana, ya É—aga masa hannu ya dakatar da shi, ya kalli rumaisa ya ce "Wane jaririn ki ke magana a kai?"

Waro ido rumaisa ta yi ta ce "Ni zaka rainawa hankali ka mayar mahaukaciya, wato ma baka san wane jaririn nake magana a kai ba, wallahi sai na ɗebo maka ƴan sanda, ko kuma tun da kai ma ɗan sanda ne, na san haɗa baki zaku yi, alƙali zam je na gaya wa, kuma ka bani ɗana ba zan sake zuwar muku gida ba"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, mu shiga ki ga É—an na ki, sakar mini rigata".

"Wallahi ba zan cika ka ba, ka gudu su hanani shiga" ta ƙara riƙe masa riga, suka nufi gate ɗin.

"Ranka ya daɗe, Yallaɓai ya ce kar a sake bari ta shiga".

"Ni kuma na ce sai ta shiga, ko nima an hana ni shiga ne?"

Ya girgiza kai, suka buɗe gate ɗin, suka shiga, sai da suka zo ƙofar shiga sashen ammi, sannan ta saki rigarsa ta shiga ciki da sauri.

Sai dai tana shiga babban falon ammi, abun da ta gani ya razanata.

Turus! Ta yi ta tsaya, Adam ta gani a zaune sanye cikin suit farare, da shi da ammi a falon, sabir a kan kujera yana barci.

Ta waiwaya ta kalli hanyar da ta shigo, sannan ta kalli in da Adam yake.

Ammi ta ce "Rumaisa daga ina haka?"

Ta ƙarasa ta zauna, safarta tayi futu-futu saboda tafiyar ƙafa, ta zauna ta ce "Tun safe nake tahowa, da ƙyar na zo gidan nan, dan na ga sabir, amma da na zo aka hanani shigowa, wai ya ce idan na zo kar a sake barina na shigo, sai kuma na ganshi ya zo wucewa zai shigo gidan nan, tare muka shigo na bar shi a waje, amma kuma da na shigo na ganshi a nan a zaune, a waje da ƙanan kaya na ganshi, amma kuma a nan na ganshi da wasu kayan". Tayi maganar tana kallonsa.

Adam bin rumaisa ya yi da kallo, yana mamakin anya kanta ɗaya, jin ta ce da ƙafa ta taho, kuma yanayinta ya tabattar da hakan.

Ammi ta ce "Ohh Mahmud ya shigo gari kenan?"

"Waye Mahmoud? Ba shi na gani a waje ba kenan?".

"Ba shi ki ka gani ba" Ammi ta bata amsa.

Rumaisa ta gyara zamantaz tana shafan kan Sabir, sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah ya sa idan na fita na ganshi na bashi haƙuri ban san ba shi bane ba, na yi ta masa masifa*.

"Amma rumaisa ba makaranta zaki je ba na ganki da uniform?".

"Makaranta zani, amma na kasa jurewa, ba bu abun da nake so sai in ga sabir, amma na zo wai an hanani shigowa, ban da dalilin sabir ma ni mai zai kawoni gidan nan, ina ga ma alhakin yaran mutane da nake cin zali ne ya kamani, Allah ya jarrabeni da son yaron da ake wulaƙanta ni a kansa, bakomai wataran sai labari"

Maimakonsa ammi ta ji maganganun rumaisa sun yi tsauri, sai ma wani irin tausayinta da ya kamata, lallai rumaisa tana cikin jarrabawa ta gaske saboda sabir.

Ammi ta riƙe hannunta ta ce "Rumaisa, babu mai wulaƙantaki a kan sabir, sabir ɗanki ne, ki yi haƙuri zan ɗau hukuncin da ya dace a kan Adam, amma daga yanzu duk lokacin da ki ke son ganinsa, akwai lambata a wayar mamanki, ki kirani ni kuma zan saka a kawo miki shi, ko na kawo miki shi da kaina, kin ga yanzu kin yi missing school, bari ya mayar da ke gida, tun da dama wurin aiki zai koma"

Rumaisa ta girgiza kai ta share hawaye ta ce "A'a, zan koma gida da kaina, kuma ba zan sake zuwa gidan ba, balle masu gadi su ci mutuncina a waje kamar yadda aka yi mini yau kamar Æ´ar maula" tayi maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka.

"Kiyi haƙuri, in sha Allah hakan ba zata sake kasancewa ba, babu mai sake wulaƙanki a kan sabir, ko shigowa gidan nan, tun da gidanku ne, bari a kawo miki ruwa ki sha, ki ci abinci sai ya mayar da ke gida".

Ta girgiza kai ta ce "A'a na gode, dama sabir kawai nake son na gani, ban ci wani abun ba balle yayi tunanin ina fakewa da son ganin sabir ina zuwa kwaÉ—ayi".
Kalaman rumaisa ya tabattarwa da ammi rumaisa ba wauta da ƙuruciya kawai ta iya ba, ta san mutuncin kanta, kuma tana girmama kanta.

Ta ce "Ai na baki haƙuri, kuma na gaya miki zan ɗau mataki a kansa, kuma ko me zai ce ki rabu da shi, abun da ki ka yi masa a rayuwa bai isa ya biyaki ba, ladanki yana wurin Allah, tashi mu je ki sha ruwa ki sake karyawa, wannan tafiyar da ki ka yi na san kin gaji sosai" da ƙyar rumaisa ta amince ta tashi ta bi ammi, dan tana ganin mutuncinta da darajarta, amma ba dan haka ba, sai ta ce ko iskar gidan ba zata shaƙa ba balle ruwa, saboda cin mutuncin da aka yi mata.

Ammi ta kai rumaisa falonta, ta saka a ka kai mata abinci, ta fita ta bata wuri dan ta ci, ta dawo ta tarar da Adam a falo.

Rai a ɓace Ammi ta ce "Ban ji daɗin abun da ka yi ba ƙwarai da gaske, muzanta yarinyar nan da aka yi a waje, a kan me zaka ce kar a sake barinta ta shigo?"

Cikin ladabi Adam ya ce "Tuba nake, ba na yi haka ne domin ɓata miki rai ba, amma yawan zuwanta gidan nan akwai matsala, bana son ta shiga cikin wani hatsari saboda ni ko ayi amfani da ita wurin cutar da waninmu"

Ammi ta ɗan yi shiru ta ce "Ban ƙi ta taka ba, amma a ƙuruciya irin ta ta, da irin ƙaunar da take nunawa gudan jininka bai kamata a ɗauki wannan matakin kai tsaye a kanta ba, ba tare da bin wasu hanyoyi da ba zata ga an wulaƙantata ko cutar da ita ba. Tana da matuƙar wayo da kaifin basira, dan haka abun da ka yi mata dole ta kirashi da wulaƙanci da tozarci, kar ka sake yanke makamancin wannan hukuncin ba tare da izinina ba".

Ya risuna ya ce "In sha Allah"
Chapter 113 · 0% Book details