Sashe 111
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Subhanallah, meye da halin nasa?"
"Ba ki ga yadda ya tsaneni ba? Hmm baki san halinsa ba ne"
Wani ƙarfin hali sai rumaisa, mace da ɗan ta, amma tana faɗin ba ta san halinsa ba ne.
Ammi ta ce "Rumaisa takawa mutumin kirki ne, fiye da yadda ki ke tunani, kawai mutum ne mara son hayaniya da shiga sabgar mutane".
"To ni dai saboda ke zan yi masa addu'a kawai"
"Yauwwa rumaisa, maƙiya sun saka shi a gaba, wai cewa aka yi shi ya kashe aisha ya yi tsafi da gawarta, kuma sabir ba ɗan sa bane ba"
Ruma ta waro ido ta ce "Wai dama da gaske yasir yake, muna tafiya a hanya ya gaya mini, Innalillahi kam bala'i, to shi kuma yayi shiru" ta yi maganar tana ƙare masa kallo.
Sai kuma ta sake cewa "To shine yayi kuka da aka faÉ—i haka? Na ga kamar idonsa yayi ja?".
"A'a ba kuka ya yi ba, addu'a dai zaki din ga yi masa"
Ruma ta ce "Taɓ, ammi kin san wani abu?".
Ammi ta ce "A'a".
"Nifa wallahi dan mutanen duniya sun tsaneni suna yi mini sharri, in dai Allah yana so na shikenan, kin ganni a unguwarmu ce mini ake ƙanwar maza, wai idan na yi tsokana yayyena suna tare mini, eh wataran suna tare mini, idan aka koma gida kuma su hukuntani, har gida aka je aka cewa mama wai bani da tarbiyya, tun da ƴan unguwarmu suka yi mini tambarin rashin ji na daina jin nauyin kowa. Idan na yi musu abun arziki ba a zuwa a gayawa mama ko yayyena, da na yi rashin ji, za su zo su faɗa. Ni kuwa tun da na gane haka na daina saurarawa kowa, idan na yi tsokana ta ko a zaneni, ko.....
Jin zancen nata ba kai ba gindi ya sanya yasir cewa "Bari mu tashi mu tafi".
Ammi ta girgiza masa kai, ta ce "Baka ga hira muke yi ba, ina jinki umman sabir"
Ta sake gyara zama ta ce "Tun da na fuskanci ƴan unguwar nan ba sa yaba mini a kan abun arziki, ya sanya na zauna a kan kalmar rashin ji, idan aka ce na yi abu bana jin shakkar in ce na yi ko kasheni za ayi, idan ban yi ba komai za ayi mini ba zance na yi ba. Allah kaɗai nake tsoro shi ya halicceni kuma jin tsoronsa dole ne. Wallahi ammi a kan gaskiyata sai da a kasheni, kin san bala'in da na gani a hannun 'yan bindiga kuwa? Hmmm ai wallahi idan nice shi, zan kalli duk wanda ya ce na kashe matata na ce na kasheta idan kana da alaƙa da ita ka nemi shaida ka kaini kotu.
Ba dai baba mai farin rawani ne baban Anty Aisha ba, kuma ya ce mini ya san baban sabir ba zai cutar da anty aisha ba, to wallahi sai na kalli uban kowa na ce masa na yi ɗin. Ai su yadda na fuskanci mutane, idan suka yi maka ƙage, ka yi ƙoƙarin kare kanka, to zasu yi ƙoƙarin su ga sun sake binciko wani laifin saboda zasu gane ka tsorata, yaya usy ya ce mini, na koyi rayuwa nikaɗai a lokacin da babu wanda zai taya ni ƙwatar ƴancina, sannan na fuskanci abun da yake bani tsoro, aikuwa na ɗauka, ai tunda na gane ƴan unguwa sun gane lagona su kai ƙarata gida mama tayi mini faɗa na fetsare, ka kai ƙarata gobe na yi maka abun ya fi na jiya, idan ka kawo ƙarata aka tambayeni na yi in ce eh, zaɓi ya rage a kasheni ko a barni da rai.
Wallahi ammi idan ya ce wa masu cewa ya kasheta yayi ɗin, ya gani idan za a cigaba da takura masa, duk wanda ya damu ya kai ƙara, ko kuma tun da ɗan sanda ne ya kamosu ya yanke musu hukunci, su faɗi yadda aka yi suka san kasheta ya yi, ko kuma ya kullesu ba rannan wata haka ta yi ba, wannan kwamishiniyar ba aka ce wani ya ɓata suna ba, aka kai su gidan yari, ko decoration of character ko me ake cewa oho dai".
Duk da damuwar da adam yake ciki, sai da ya tattara hankalinsa yana sauraron rumaisa, duk da ba kallon in da take yake yi ba. Shi wasu lokutan har tsoro take bashi, ta wani fannin maganganunta a kan gaskiya suke, da maganar hankali da shirme haka take kwaɓa kayan ta.
Ammi ta ce "Waii, rumaisa an gaisheki, ban taɓa ganin yarinya irinki ba, ke kuwa ya ƴan bindiga suka iya zama da ke?"
Ruma ta yi murmushi ta ce "Haka suka zauna da ni, amma na ci ubana ba ƙarya ammi. Ni fa tun da ga kano aka ɗaukemu da ƴan bindiga, har kaza suka sai mini da na ce ina jin yunwa, suka nuna mini wata jaka, cike da bullet, har da bindigogi, shugabansu ne fa ya zo in da aka yi garkuwa da mu, ya sakeni ni da sabir, shi wanda ya sai mini kaza, ammi garin da na je, idan ka yi noma ba zaka taɓa ba sai ƴan bindiga sun yi maka izini, ni na je na ɗauki masara aka je aka gayawa mai gari, da nake a gidansa.
Da aka yi garkuwa da ni, baki ji abubuwan da suka faɗa a gabana ba, na ce idan na kuɓuta sai na faɗa suka ce kona faɗa a banza, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, na yi ta karanta musu, ba ƙaƙƙautawa sai Allah ya kawo mini anty aisha, daga baya kuma muka kuɓuta ni da sabir"
Ammi ta yi wata irin ajiyar zuciya ta ce "Amma abun da mamaki, wannan wane gari ne haka?"
Rumaisa ta É—aga kai ta kalli adam, sannan ta ce "Na manta sunan garin"
Adam tambayoyi ne fal a ransa, amma girman kai ya hana ya tambayi rumaisa, gashi ammi ta fara taɓo abubuwa masu muhimmanci, amma rumaisan ta kauce taƙi magana.
Ruma ta yi wa sabir kiss, ta miƙawa ammi shi ta ce "Ammi, bari mu tafi, kar mu yi dare ba mu je gidansu Hauwwaliya ba".
Ammi ta ce "To madalla, Allah ya tsare dan Allah ku gaida mamanku, ku jira bari na baku kuÉ—in mota".
Ruma ta ce "A'a muna da kuÉ—i, na ga kaya na gode sosai da sosai, baba mai farin rawani ma, ya bani kaya har da kayan gara masu daÉ—i da zuma da nono, da kilishi na gode sosai"
Ammi ta takura ruma, ta basu dubu biyar suka tafi.
Bayan tafiyarsu ammi ta kalli takawa ta ce "Adam, dan Allah ne ka fuskanta game da yarinyar nan, ji yadda take magana kamar ana karanta mata?"
"Ni banga komai ba sai shirme da rashin nutsuwa a tare da ita".
Ammi ta ce "No, maganganunta abun dubawa ne, a duk lokacin da duniya ta nemi juya maka baya, ka kama Allah ka nuna musu zaka iya rayuwa kai kaɗai, kar ka yi ƙoƙarin lallai sai an yadda da kai"
Ya numfasa ya ce "Ammi wannan shirmenta ne kawai na ƙuruciya, da rashin sanin ciwon kanta, yaushe ta zo duniyar balle ta san me duniyar ke ciki, tana tunani ne a iya ƴar ƙaramar duniyar ƙwaƙwalwarta, bari na tafi masallaci ".
Ammi ta ce "Shikenan Allah ya taimaka".
Sai dai maganganun rumaisa suka cigaba sa shiga suna fita a cikin kwanyarsa, kamar maganganun ta na bisa turba.
Rumaisa sai da suka je gidansu Hauwwaliya, ƙafar Hauwwaliya ta yi kyau sosai, suka din ga murna da ganin rumaisa, ana yin sallar magariba, Yasir ya tasata a gaba suka tafi gida.
A hanya yasir ya yi ta yi wa rumaisa faÉ—a a kan tsinannen surutunta yayi yawa, ko a jikinta tun da muradinta ya cika.
Bayan sallar magariba, Adam da kansa ya je gidansu Jabir, ya tarar da shi da Jamil suna tare.
Jabir ya ce "Ka gama jan ajin ka neme ni kena?"
"Jan ajin me fa?"
"Ai ka fini sani, ka ce zamu haɗu amma na yi ta kiran wayoyinki ka ƙi ɗagawa"
Adam ya ce "Ba ƙin ɗagawa na yi ba, kaɗaici nake buƙata ne, abubuwa sun sha kaina da yawa".
Jamil ya ce "Ai kai dama yanzu sai ana yi maka uzuri"
"Hmm baku ga abun da yake ta yawo a social media ba, game da mutuwar aisha? Wai yanzu rahoton cikin gidana shine labarin yaɗawa a media dan a ɓata mini suna"
Jamil ya ce "Ni kaina abun ya girgiza ni, na rasa yadda aka yi maganar nan ta fita a haka, tun É—azu ni da Jabir abun da muke tattaunawa kenan, yadda za a shawo kan matsalar nan, amma ya kake gani, me ka shirya gayawa duniya domin wanke kanka?"
"Ba ni da isasshen lokacin da zan ɓata wurin ƙoƙarin wanke kaina a idon duniya, ina da abubuwan yi da yawa a gabana, kuma ba za a kawar da hankalina a kan abubuwan da na sanya a gaba ba, duk wanda yake ganin yana da wani ƙorafi, ko son tuhumata a kan mutuwar matata, idan yana da shaida ya kaini kotu" yayi maganar yana jin kamar za ayi masa kallon wawa abun da ya faɗa.
Jabir ya waro ido ya ce "Yanzu kana nufin haka zaka zuba ido a cigaba da ɓata maka suna?"
"Idan sun gaji zasu daina, idan kuma basu gaji ba zasu cigaba, idan na cigaba da ƙoƙarin wanke kaina, za su cigaba da ƙoƙarin kaini ƙasa, idan na tsaya a kan ƙafata na cigaba da karɓar duk abun da za'a ce kaina, wataran gaskiya zata yi halinta"
Jamil ya ce "Amma kana ganin hakan mafita ce adam? Duk abun da ya shafeka ya shafi masarautar garin nan ne fa kai tsaye"
Adam ya ce "In da nake godewa Allah kenan, atleast masarautar nan wani immunity ne a gareni"
Su da suka san Adam da saka abu a rai, da shiga damuwa sun yi mamakin yadda yau ya nuna halin ko in kula da wannan lamarin.
Jabir ya ce "To, bari mu ga zuwa yaushe wannan mafitar taka za ta kawo sauyi ga lamarin nan, amma a ganina kamar kasada ce hakan, Allah ya yi mana jagora"