Sashe 52
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayshercool
[8/22, 11:41 PM] Maman Aslam: *Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Tamkar wadda aka tsamo da ga kwata haka ruma ta juya ta koma gida tana kuka, mutane a hanya wasu na tambayarta ko lafiya? wasu kuma suna mata dariya, yara sa'aninta kuma suna dariya ta kamo kifi soyayye, saboda yadda ta yi tsumu-tsumu da taɓo.
Takawa kuwa tafiya yayi yana jinjina taurin kai da tsagwaron tsageranci gami da rashin tsoro irin na Rumaisa.
Ya daÉ—e bai ga abin da ya bashi mamaki kamar rumaisa ba, amma babu mamaki kamar yadda ya sanya aka masa bincike an tabattar masa da a cikin maza bakwai ta tashi, har halinta na rashin ji sai da aka gaya masa, tare da makarantar da take zuwa, a nan ya tabattar da muryarta da yake ji tabbas ta ta ce, tun da gidan gonarsu a unguwar su yake. Amma ya aka yi ta san gidansu har ta bishi can.
Ya tsaya da mamakin ne a lokacin da ya tuna ɓarawo da ta laƙanta masa, a take ransa ya ɓaci, ya sake ƙudurar aniyar sai ya ladabtar da ruma ta hanyar da ta dace.
Idan ya tuna sharrin da ta sake liƙa masa, wai ya taɓa mata nono, sai ya rasa me ma zai yi, mamaki ko dariya?.
Mama ce ta kalli ruma ta ce "Meye haka, meya same ki?"
Cikin kuka ruma ta ce "Wani bugagge ne ya wanke ni da ruwan kwata, wallahi ba zan yafe masa Allah ya tattaro masifar duniya da ta gabasa da yamma kudu da arewa....
"Rufe mini baki? Ban hana ki yi wa mutum irin wannan addu'a ba? Wataƙila bai sani ba"
"Mama kalli jikina fa, ya na sane yayi mini, wallahi ba zan yafe ba, kuma in Allah ya yarda sai an sace motar, sai na yi masa tijarar da bai taɓa ganinta ba idan na kuma haɗuwa da shi, kuma sai an sace motar na ga ta tsiya"
"Wane mahaukacin ne yayi miki haka? Makaho ne shi?" Usman ya faɗa yana ƙarewa uniform ɗin ruma kallo, da suka jagalgale da taɓo.
Mama ta ce "A'a, kar ka zigata dan Allah, wuce ki je ji cire kayan, tsautsayi ne, kuma Allah yana tare da masu haƙuri"
Usman cikin takaici ya ce "Haba mama, kalli jikinta fa wallahi wannan da iskanci yayi mata, waye shi a ina yake? Kin gane shi? A nan unguwar yake?" Ya jero mata tambayoyin.
ÆŠan shiru tayi ta tuna furucin takawa, na zai kama yayyenta ya rufe su, ya saka a rushe musu gida. Nan da nan ta ce ni ban san shi ba, zuwa ya yi wucewa, yayi mini haka, to wallahi Allah ya isa na"
Huzaifa ya ce "Ƙaraso na tayaki ki wanke jikinki" ta ƙarasa, Huzaifa ya ɗebo ruwa a rijiya ya hau sheƙawa ruma, sai da ta kusa shiɗewa, mama ta din ga yi masa faɗa, ƙarshe dai ruma ba ta je makarantar ba ranar, ba ta yi jarrabawar ba, wunin ranar kuka ta din ga yi, tare da janyo wa takawa jafa'i iri-iri.
A daren da yakamata washegari su ruma su tafi katsina, ta fara ciwon kai da ciwon ciki, har zuwa wayewar gari, dan haka mama ta ce sai dai a É—aga tafiyar zuwa kwanaki biyu idan ruma ta warke.
Har zuwa azahar ruma tana kwance tana fama da ciwon ciki, Yasir ya ce "Shegen ciye-ciyenki na masifa ne yake janyo miki ciwon ciki, kece ci wannan ci wancan a islamiyya kullum cikin tauna kamar tunkiya" ruma ba ta yasir take ba, ta kanta take yi dan haka bata kula shi ba. Aka kai ruma chemist aka sayo mata magunguna.
Mama aka yi wa waya daga cikin gari, babur ya buge Hauwwaliya ta karye a ƙafa, dan haka babu shiri mama ta shirya cikin tashin hankali ta tafi.
Ruma sai kuka take, ga karayar hauwwaliya, ga zafin ciwo kuma wai mama ba zata tafi ta barta ba. Mama ba ta saurareta ba, ta shirya ta yi ficewarta.
Burgima ta din ga yi a tsakar falon mama tana kuka, kamar wata yarinyar goye, sai gunji take "Wayyo cikina"
"Ke!" Ta ji tsawar mai sunan Baba daga ƙofar ɗakin. Take ta nutsu ta yi shiru.
"Mara hankalin ina ce ke? Dan baki da lafiya sai ki ishi mutane, ba zaki yi addu'a ba?"
Shiru ta yi tana kuka ƙasa-ƙasa dan ita kaɗai ta san abin da take ji.
Aka jima kuma sai amai, ga jikinta ya É—au zafi sosai. In da ta yi aman a nan ta zauna ta kasa tashi. Sai Aliyu ne ya wanke mata baki ya É—agata ya mayar da ita É—aki, ya wanke wurin.
Har bayan azahar mama ba ta dawo ba, ga ruma jiki yaƙi daɗi, Aliyu ya ce zai samo abin hawa ya kaita asibiti. Usman ya ce a fara ba ta abinci ta ci tukuna.
Cikin ruma ya sake ƙullewa, har cikin ƙafafuwan ta, ta tashi da ƙyar, ta tafi toilet yin fitsari.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku dan Allah ku taimake ni " suka jiyo ihun ruma a toilet.
Mai sunan Baba ne ya tafi da gudu ya buɗe banɗakin a razane, dan duba meya sameta, suma sauran suka rufa masa baya, amma suka tsaya a waje saboda ya na bakin ƙofar.
Ruma ce a tsaye, ta gama fitsarin ta miƙe tsaye tana kallon yadda fitsarin na ta ya gauraya da jini, duk da ba wani mai yawa bane ba.
"Meye haka?"
Cikin rawar jiki ta nuna masa ta ce "Mai sunan baba ka ga, fitsarin jini nake, mutuwa zan yi" tayi maganar idonta na cika da hawaye.
"Yaushe ki ka fara irin wannan fitsarin?"
"Yanzu kawai na gani" tayi maganar tana dafa bango, saboda jirin da take ji.
Ya waiwayo ya kalli Yasir ya ce "ÆŠauko mata zanin mama" Yasir shima jiki na rawa ya tafi É—akin mama, dan hankalinsa ya tashi sosai.
Ya sake duban Usman ya ce "ÆŠan É—ora mata ruwa ya yi zafi, ta yi wanka" cikin damuwa Usman ya ce "To meya sameta?"
Ya É—an É—age kafaÉ—a ya ce "May be is her fisrt period"
A razane Aliyu ya ce "What! Rumaisan? How old is she? Yarinya ce fa sosai"
Usman ya ce "Ikon Allah"
Mai sunan Baba ya miƙa mata zani ya ce ta ɗaura ta fito. Ta ɗaura ta fito ya bata kujera ta zauna, Usman ya zuba ruwa ya wanke banɗakin. Ruma kuwa jikinta sai rawa yake yi tana tunanin ƙarshenta ne ya zo.
Usman ne ya fita sayo pad, sai dai babu wanda ya san ya ake amfani da ita.
Gaba É—ayansu suka diririce, musamman ganin yadda ruma ke kuka, Huzaifa kamar ya tayata kukan, ita sam ba ta san menene ya sameta ba, mai sunan Baba ne kawai yake ta wani basarwa.
Aka kai mata ruwa tayi wanka, usman ya tattare kayan da ta cire, ya zuba a bokiti ya zuba musu ruwa.
Gaba É—aya mai sunan Baba ya rasa ta ina ma zai fara, gaba É—aya baya manta lokacin da aka haifi ruma, kamar jiya aka haifeta haka yake gani, wai ita ce yau period ya zo, yarinyar da ko ciwon kanta ba ta sani ba, ban da tarin rashin hankali da rashin kunya ba abin da ta sani, duk wani abu da ya shafi rayuwa ba saninsa ta yi ba.
Sai da yayi browsing, sannan ya ga yadda ake amfani da pad, ya nuna mata, har zuwa yadda ake discarding ɗin ta, ta karɓa ta saka, sannan ta saka kaya.
Ya kalli su Usman ya ce "Su basu wuri, za su yi magana" ba musu duk suka fita.
Ya kalli ruma ya ce "Kalleni nan" ta É—aga kai ta kalleshi.
"Ko akwai wani abu da ya haÉ—aki da wani?"
Ta ce "Eh" gabansa yayi wata irin mummunar faÉ—uwa ya ce "Menene?kuma waye shi?"
"Wani mutumi ne, ruwan kwata ya watsa mini da motarsa jiya da safe".
"Ba wannan nake nufi ba, ko akwai wani wanda yayi miki abin da bai dace ba, ko wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki?"
Tunowa ta yi da takawa, yadda ya cakumota, amma tayaya za ta fara yi wa mai sunan Baba wannan bayanin, ai kan a kai ga takawa, ita zai fara tattakawa, a karon farko da ta yi masa ƙarya ta ce "Babu kowa"
"To idan ma akwai ki ka ƙi faɗa, idan na gano sai na yankaki na zuba a rijiya, kuma wannan yanayi da ki ka shiga, duk wanda ki ka bari ya taɓaki ko yayi miki wasan banza, ciki zaki yi kuma mutuwa zaki yi" gaban ruma ne yayi mummunan faɗuwa, meye makomar taɓata da takawa yayi? Ta yi ciki kenan?.
Haka suka shimfiÉ—a tabarma a tsakar gida, suka kewaye ruma, yau har masu zuwa ball ba wanda ya fita, suna ta jera mata sannu, ban da masu fifita da masu ba ta abinci.
A haka mama ta dawo ta tarar da su, cikin mamaki ta dube su ta ce "Wai har yanzu jikin ne?"
Usman ya ce "Tun da ki ka fita a haka take"
Mama ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, wallahi ina can muna fama, da ƙyar aka samu aka ɗora yarinyar nan, tana jin jiki, sannu 'yar auta" ruma dai ba ta amsawa mama ba, ta sake lafewa a cinyar Aliyu.
Mai sunan Baba kuma yana gefe kamar mai gadi, yana kallonsu.
Mama ta kalli kayan ruma da suke shanye, gidan ko ina tsaf, amma ko girkin dare ba su É—ora ba.
Mama ta ce "Yasir, tashi ka É—ora mana ko taliya ce a ci da daddare" gaba É—aya basu da walwala kamar wadda aka ce musu ruman mutuwa ta yi.
Cikin damuwa mama ta ce "Wai me yake faruwa ne duk na ga kun yi jugum-jugum? Duk dan ba ta da lafiya ne ku ka zo ku ka tare a wuri É—aya haka, ba an sayo mata magunguna ba?"
Duk shiru suka yi, suna sunkuyar da kai aka rasa mai iya yi wa mama bayani.
"Mama fitsarin jini fa nake yi " Ruma ta yi maganar daga kwance.