← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 174

Sashe 87

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya girgiza kai tare da goge hawaye ya ce "A duniya bani da makusancin da ya fiki, daga ni har aisha, kin san komai Ammi, kamar yadda muke ta neman magani tsawon shekaru huɗu, aka dace cikin jikinta ya zauna, bayan ɓari da take ta yi babu ƙaƙƙautawa a dalilina, cikin nan  babu wanda ya san da shi, bayan ke sai mu, wanda hakan shawarar ki ce, har zuwa lokacin da kika bayar da shawarar ta je Saudiyya wurin ɗan uwanki kawu mahadi, ta zauna ta raini cikin a can, idan ya isa haihuwa ta dawo Nigeria, duk dan kaucewa hatsarin da ka iya faruwa da cikin, muka yi nesa da juna ni da ita.
Bayan na kai ta ta yi watanni huɗu, na sake komawa Saudiyya umara, na dubata, na dawo babu daɗewa ta ce mini ita ta gaji da zaman Saudiyya so take ta dawo gida. Ta ce mini wannan kakar ta ta, mariƙiyar mamanta babu lafiya, dan haka ita so take ta dawo ta je ta ganta, kar ta rasu basu gana ba. Gudun ɓacin ranki, ya sanya ta dawo babu wanda ya sani, sai dai a lokacin cikin yayi girma sosai ta sanya rigima a kan lallai sai ta je duba matar, an ce ba ta gane kowa, wankin ƙoda ake yi mata ma. Duk sauƙin kan Aisha, haka ta kafe a kan lallai sai ta je katsina duba matar, a daidai lokacin kuma ni tafiya Abuja ta kamani, bayan tafiyata ta sanya ɗaya daga yarana, masu tsaron lafiyarta ya kai ta katsina. Ta turo mini saƙo a waya tana bani haƙuri a kan ita fa ta tafi, ba zata iya jira na dawo ba, a tsorace take kar kakarta ta mutu. Bayan dawowata daga Abuja, sai samun saƙo na yi, an tsinci gawar yarona da motar, ita kuma ba a san in da take ba, tun da ga wannan lokacin nake ƙoƙarin gano in da take, har zuwa wannan lokaci, daga ni sai Bashir muke ta ƙoƙari, dan ko su Jabir basu sani ba, na san na yi laifi ammi amma ba da gayya na yi ba.

"Adam nika ɗai zan fuskanci wannan bayanin naka, duk mutane sun san da cewa tana Saudiyya, babu wanda ya san ta zo Nigeria haka zalika babu wanda ya san tana da cikin ma, kawai sai mu ce ga ɗa to ita tana ina, na gaya maka bana samunta a waya, amma ka yi ta yi mini ƙarairayi, dama akwai abun da zaka iya ɓoye mini Adam? Me zaka cewa Turaki?".

A raunane Adam ya ce "Ko babu wata cikakkiyar shaida,ni na san da cewa É—ana ne, babu yadda za ayi yarinyar nan ta san wasu abubuwan idan ba gaya mata tayi ba, amma ammi ni yanzu ba abun da mutane zasu ce ne ya dameni ba, samo aisha ne ya dameni, babu wata hujja da nake jira yaron nan nawa ne, ko a fuskarsa kamanni na ne, sannan da kaina zan gayawa turaki komai, duk hukuncin da zai yi mini zan É—auka".

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zan cigaba da yi maka Addu'a, Allah ya kawo mana mafita, amma yarinyar nan ka bita a hankali dan Allah, in sha Allah yadda jaririn ya kuɓuta, ita ma zata kuɓuta".

Adam ya jinjina kai kawai, ya tashi ya fita daga É—akin, su Nusaiba suna falo a tsaye cirko-cirko, adam ya zo ya fice.
Cikin rige-rige suka tafi É—akin Ammi, amma suka tarar ta shiga toilet, ko da ta fito umarni ta basu, na su je su kwanta sai da safe, dan kar su bi diddigin abun da ya faru, sai dai a tsorace take da abun da ka iya faruwa idan zancen nan ya fasu.

A asibiti kuwa, Aliyu ne ya dubi rumaisa ya ce "Ke dai a rayuwarki ba a taɓa rasaki da matsala, an samo uban yaro kin ce ba shi ne ubansa ba, sai ki nuna mana waye ubansa?"

Usman ya ce "Ai ko da uban me ki ke yawo, sai an mayar musu da É—an su"

Mama ta ce "Yanzu dai a bar wannan maganar, Allah ya dawo mana da ita, daga dawowarta sai a bari ta sarara kan a hau yi mata faÉ—a, Ali ku je gida haka, kwa sanar da mutane an ganta"

Mai sunan Baba ya ce "Eh amma kar su sanar da Asibitin da take, kar azo a takura mata, ko ayi ta surutu saboda jaririn nan, a bari komai ya daidaita"

Mama ta ce "To hakan ma babu laifi, kar ku gayawa Abubakar a daren nan tun da ba a samu wayarsa ba, ku bari sai da safe kar ya ce zai bsro dutse yanzu"

Usman ya ce "In sha Allah"

Mai sunan Baba ya saka hannu, ya karɓi jaririn da ga hannun rumaisa, sai bin sa take da ido, kar ya fita ya bawa Adam yaron, ya ƙarewa yaron kallo ya ce "Bari na bawa nurses ɗin nan, su mayar da shi ɗakin da ake kulawa da sh, mama gobe in Allah ya kaimu zan zo mu koma ki ga likitan ki"

Mama ta ce "Ga mara lafiya ni ina zani? Dama rashin lafiya tawa saboda ita ne"

Ya ce "Duk da hakan, yakamata ke sai da safe, ki nutsu ban da gardama da taurin kai ki yi addu'a ki kwanta ki huta"

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce "Dan Allah mai sunan Baba kar ka bawa kowa shi, wallahi zan iya rasuwa idan aka rabani da shi" bai ko waiwayo ba ya fice daga É—akin.

Mama ce ga rungumota tana rarrashinta ta ce 'Ba wani zai bawa ba kin ji, ki yi haƙuri ɗakin da ake kula d shi zai kai shi" rumaisa ta yi lamo a jikin mama, can ta ce 'Mama"

Mama ta amsa mata da na'am.

"Ba mafarki nake ba ko, ba zan kuma farkawa na ganni a dajin ba, na ga kun daÉ—e a wannan mafarkin nawa".

Mama ta shafa bayanta ta ce "Ba mafarki bane ba, duk muna tare da ke".

"Mama kin ga yadda ki ka rungumenin nan? Haka maman yaron nan take rungumeni tana rarrashina idan na tunaki ina kuka, sarƙarta da zobuna ne a cikin ɗankwalin nan, ɗan kunnen da ki ka cire a kunnena shi ma nata ne, mama ba zan manta da ita ba" rumaisa ta yi maganar cikin kuka.

"To ya isa, ita ma in sha Allah zata kuɓuta cikin amincin Allah" rumaisa ta cigaba da kuka, dan ba wanda ta gayawa aisha ta rasu.

Aliyu suna zuwa unguwarsu, ya wuce gidan su Habiba, lokacin kusan ƙarfe goma na dare, ya aika yaro ya ce yana sallama da Habiba.
Maimakon Habiba sai babarta ta fito tana masifa, wani watsatstsen ne ya zo neman habiba a wannan daren, yar habiban guda nawa take?

Tana ganin Aliyu ta yi sak, ta ce "Ya aka yi ne, ko laifin ta kuma yi maka, ko ƙanwar ta ka ta kuma duka ka zo rama mata, duk da ance an yi garkuwa da ita"

Ya ce "Ba É—aya, wani abu zan gaya mata".

"Wani abu ne kenan?"

Aliyu ya ce "Shikenan tun da na ga hankalinki bai kwanta ba"

Sai kuma ta ce "A'a, bari na taso ta" ta koma cikin gida, mintuna uku sai ga habiba ta fito tana mutsutsuka ido.

"Habiba" ya kira sunanta, ta kalleshi ta ce "Yaya Aliyu ina wuni"

"Albishirnki" yayi maganar cikin murmushi.

Ta É—an yi saroro ta ce "Goro".

"To zaki bani goron nan, Alhamdilillah addu'a ta karɓu, rumaisa ta kuɓuta yau, tana asibiti ma"

Gigicewa ta yi ta ce "Innalillahi, dan Allah da gaske, dan Allah kar ka ce da wasa kake yi, dan Allah mu je in ganta".

"No, ba a zuwa wurinta yanzu, ba ta da lafiya, amma zan zo da kaina na kaiki ki ganta"

Hawaye ta fara matsewa tana "Allah sarki ƙawata, Alhamdilillah, Allah na gode maka"

Ya ce "Maza ki je ki cigaba da baccinki, Sai da safe"

"Dan Allah yaushe zaka zo ka kaini na ganta, gobe?"

"A'a zan zo dai, ki je ki cigaba da baccinki" yayi maganar yana É—aga mata hannu ya tafi.

Ta shiga gida da gudu tana murna.

Adam kuwa yana zuwa É—aki ya zauna ya fashe da kuka kamar yaron goye. Wai matarsa ce ta haihu a daji a hannun 'yan bindiga, ko a yaya ta haihu oho, ko a wani hali take sanin gaibu sai Allah.

"Why aisha, meyasa ki kasa jira na dawo ki ka tafi? Duk yadda muka tssra rayuwa bayan kin haihu, ƙarshe a tsinto mini ɗana babu ke, haba aisha kin ga sakamakon rashin jin magana ko, matar da ki ke so ki je ki duba ita bata mutu ba, amma ke kin shiga wahala. Amma bakomai, Allah ya sa kina cikin ƙoshin lafiya, zan fito da ke ko da zan rasa rayuwata ne!

ƘANWAR ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

Ayshercool
08081012143.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
Chapter 87 · 0% Book details