Sashe 163
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving É—in su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.
Tashi ya yi ya kunna fitilar ɗakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta ɓata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.
Bai ce mata uffan ba, ya É—auki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.
A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ƴan kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ƙoƙarin tsafta.
Tea yake son haÉ—awa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.
Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka É—auko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".
Ta taka kujera, ta buÉ—e wata drower, ta É—auko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.
Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta ɗauki ƙaramin flask ta juye masa, ta haɗa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".
Kamar soko haka yake kallonta, ta É—auki wani É—an bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.
Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira É—aya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne.
Ta karɓa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ƙyaleta su cigaba da kaiwa.
Ɗakinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banɗaki yana wanka, ta karkaɗe masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi ƙoƙari ai".
Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa.
Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a buɗe yake, gashin ƙirjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe.
"Ya aka yi?".
Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan".
Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke"
"Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?"
Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai".
"Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki".
Ta ji daÉ—i za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba.
Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har ɓarauniyar turare yake ce mata.
Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta ɓalle ta tafi gida.
A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan.
Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab.
Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi.
Rumaisa da sun haɗa ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wulaƙance.
Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi.
Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya daÉ—e".
"Barkanmu dai ƴar albarka, ya gidan ya ƙoƙari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
Adam har leƙa fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka.
Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi.
Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake.
Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan.
Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah".
Gudun kar ta fara sakin layi kamar yadda ta saba, ya sanya adam sakata a gaba suka fita, sai dai a wannan karon sai suka fita ta ƙofar da zasu fita haraba kai tsaye, ba tare da bi ta falon gidan ba, sai dai suna fita suka yi kiciɓis da Samha!
Ayshercool.
08081012143*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please ðŸ™
"Na shiga uku, mama, dan Allah a taimakeni, ƙonewa nake yi fa"
"Ai da ni ki ka yi niyyar ƙonawa, sai dai mu ƙone tare" ya haɗa hannayenta ya riƙe da hannu ɗaya, ya cigaba da zuba mata ruwan har a fuskarta.
Ta dinga mutsu-mutsu ta tashi, amma abu ya gagara, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ta kasa, sai ta hau kuka, tana yi masa magiya, a kan ya ƙyaleta.
"Har da sha mini toothpaste ko, saboda ke ƙazama ce".
"Ni ban sha ba".
"Ai ina jin duk abun da ki ke cewa, idan mu ka gama ƙonewar, sai mu yi jinya tare "
Cikin kuka ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, fata ta zata kwashe, dan Allah ka yi haƙuri".
"Ai baki isa ba, ni zaki ƙona da ruwan zafi ki huta ko?".
"A'a ba haka nake nufi ba, dan Allah ka yi haƙuri ".
"Ni sharifi ne, ba abun da ruwan zai yi mini, ke da ki ka shirya ramin muguntarki, gashi kin faÉ—a".
Ganin ta na kuka wiwi, ya sanya ya cikata, ta tashi da sauri, ta fice daga bath ɗin, jikinta na tsuma ta tafi ɗakinta, ta tuɓe kayan a tsakar ɗakin, ta zura da gudu toilet, ta sakarwa kan ta shower, jikinta yayi ja, ta zauna a toilet ta cigaba da kuka tana faɗin "Wallahi ba zan yafe ba, wuta balbalin bala'i"
Sai da ta daina jin zafi, sannan ta fito ta É—aura towel.
Duba jikinta take yi, tana duba wa ta ga, ko fatarta za ta kwashe, cikin ikon Allah ba abun da ta yi.
"Wato shi ba ma ya jin zafin ruwan, amma ni ya ƙona ni, zai gane ni ya taɓa, sai na rama, har da wani rungumeni saboda tsabar rashin sanin abun da ya dace, Innalillahi Allah ya sa kar a gane idan na fita, ya kuma riƙe mini hannu na kasa guduwa". Ta saka hannu ta toshe bakinta ta ce "Astagfirullah, Allah ka yafe mini".
Sai kuma ta tuna abun da ya yi mata na cewa, ba ta da nono.
Ta kalli jikinta a mudubi, ta ɗan bankaɗa towel ɗin ta kalli ƙirjinta, ta ce "Saboda tsabar saka ido, wai nonona ne bai fi wake ba, mutumin nan ya cuceni, wato kallona ma yake yi haka? To saboda ba ni da su ake cewa ni ba mace ba ce? To na ga ma ba sai mutum ya haihu ba suke da amfani? Amma bakomai, Allah ya sa su fito mini, na huta da gori. Kai Astagfirullah, in rasa mai zan roƙi Allah sai wannan abun, Allah na tuba ka yafe mini. Amma wallahi sai na faɗi abun da mutumin nan yake yi mini, tun wuri ayi mini tsakani da shi, a taka masa burki, kar ya sake rungume ni".
Sai da ta gama surutanta ita da mudubi, sannan ta tashi ta shafa mai ta saka kaya.
Ta daÉ—e a É—akinta, sannan ta fita, ta tarar shi tuni ya fice, ta kwaso kayan gyaran É—akin, ta ce yayi wa kansa dan ba za ta gyara ba.
Ba uwani ce zaune a É—akin su, tana waya, ita da Samha.
"Wai haryanzu babu sani muhimmin bayani a kan in da zamansu ya dosa, ba kya bani wani update".
"Ranki ya daɗe, su suna saman bene, mu muna ƙasa, bana iya sanin me yake faruwa".
"Dole ki din ga bibiya ki sani, bamu saka kin yi faɗi tashi, ta amince ki je gidan ki zauna ba domin ki je ki miƙe ƙafa ba, biyanki zamu din ga yi, dole ki yi mana aiki yadda ya dace, ba kuma iya leƙen asiri ba, ki yi iya ƙoƙarin ki, wurin haɗa husuma a cikin gidan nan, ki nuna mata kin fita daɗewa a duniya, dole ta fito ta bar gidan nan".
"In sha Allah uwa É—akina, za ayi yadda ki ka ce, kar ki damu".
"Ina saurarenki" Samha ta katse wayarta.
Rumaisa kuwa kitchen ɗin ƙasan ta shiga, Aisya da barira suna ta wanke-wanke.
Rumaisa ta ce "Ina kwananku"
Cikin sauri suka risuna suna gaisheta.
Rumaisa ta ce "Dan Allah ku daina gaisheni, wai ba ku ga ni ƙarama ba ce?".
Asiya ta ce "Ranki ya daÉ—e, ai Allah ya riga ya baki girma dole a biki, kuma ke matar basarake ce, dole a girmamaki".
Rumaisa ta yi murmushi ta ce "Kunya ku ke bani ne"