← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 174

Sashe 133

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumaisa ta saba sa ta dawo, mama za ta ce mata, ga ruwan wanka ta wanke wannan gumin da ƙarin ranar, idan an gama abinci ta ci ta yi salla ta tafi islamiyya, amma yau ta dawo ba ruwan wanka, ga mama ba ta kulata ba, haka ta yi abun da zata yi ta tafi islamiyya.

A ƙa'ida, ta kan ci abinci sau huɗu zuwa sama a rana, ba wai abincin take tsayar da hankalinta ta ci ba, zaɓe-zaɓe ne da ita, ga irin cin abincin yara take yi, tana ci tana wasa, ko da ta fara ta ce ta ƙoshi. Kullum ta dawo daga islamiyya sai ta ci abincin yamma, sai dai a yau ɗin ma mama ba ta ajiye mata abincin ba, gashi bata mayar da hankali ta ci na rana sosai ba, bugu da ƙari ta ga mama ta ɗora tuwo a matsayin abincin dare.

Ba ta kula kowa ba, sai kukanta suka jiyo a ɗaki, Usman ya leƙa, ya tarar ta kwaso kayanta, tana ta ninkewa tana zubawa a bagco tana kuka, kamar mai shirin yin yaji.

Cikin mamaki ya ce "Ke! Meye haka?"

"Haɗa kayana nake yi, cikin dare idan kowa yayi bacci in bar gidan nan, tun da dai ba a ƙaunata" maimakon ya ji haushinta, wata uwar dariya ce ma ta kama shi.

"Waye ba ya ƙaunar ta ki?".

"Ba mama ce ba, ta daina kulani, wallahi duk faÉ—an da aka yi da ni nice mai gaskiya, ya za ayi ace in sayo sigari? Kuma dan meyasa wannan shamsiyyar zasu din ga ce mini Æ´ar iska, sai ayi ta yi mini abu ba zan rama ba"

Usman cikin salon tsokana ya ce "Gaskiya babu daÉ—i kam, yanzu to ina zaki tafi?"

"Tun da ba a sona a gidan nan, katsina zan koma wurin Æ´an bindigar, wurin su barde, au ashe an kashe barde to dai daji zan koma na yi bukka na zauna a ciki" ta yi maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.

Usman kamar ya shiÉ—e dan dariya, Aliyu da su Huzaifa kansu dariya suke yi mata.

Aliyu ya ce "Mama ki yi biko, saboda ke za ayi yaji"

Mama ta ce "Idan ta tafi nima na huta, Allah ya raka taki gona, ku ƙara mata kuɗin mota".

Jin furucin mama ya sanya ta sake tunzura tana kuka ta ce "Shikenan, bakomai"

Ta É—auko bagconta tana kuka, Huzaifa ya ce "Allah sarki rumaisa, zamu yi kewarki sai a darul salam" ta sake fashewa da kuka.

Yasir ya ce "Rumaisa a yafi juna, Duk in da ki ka je ki zauna lafiya da mutane, koda yake ai kin ce a bukka zaki zauna ke kaɗai, Allah ya kiyaye hanya ga wannan" ya baya naira ɗari. Ta saka hannu ta karɓa, suka cigaba da tuntsra mata dariya, ita kuma bil haƙƙi da gaske barin gidan za ta yi.

Ta waiwaya tana kallon mama, ta ga mama ko a jikinta, jajjagenta ma take yi, ta nufi hanyar soro.

Abdallah ya ce "Yarinyar nan fa ba hankali ne ya game jikinta ba, bari na bi bayanta.

Ta dafe kayanta ta fita waje, ta tsaya tana tunanin wace hanya za ta bi, kamar sama sai ga mai sunan baba.

Ya kalleta ya ce "Meye haka? Ina zaki? Kukan me ki ke yi?" Ya jejjero mata tambayoyin.

"Tafiya zan yi" ta faÉ—a tana share hawaye.

A kausashe ya ce "Zuwa ina?"

"Mama ba ta so na, kowa ya tsaneni shi ne na ce barin gidan zan yi, an bani kuÉ—in mota ma" tayi maganar tana nuna masa kuÉ—in hannunta.

Takaici ne ya ƙule mai sunan baba, gaba ɗaya rumaisa ba ta da wayo wasu lokutan cikin takaici ya ce "Dalla wuce ko na mareki"
Za ta yi Magana, ya daka mata tsawa zai kai mata duka, ta taka da gudu ta koma cikin gida.

Abdallah da ya biyo bayanta kuwa, dariya kamar zai shiÉ—e.

Mai sunan baba ya biyo bayanta zuwa gidan, su Usman ya saka a gaba ya din ga yi musu masifa, saboda sun bar rumaisa ta fita, ba sa tsoron ta yi wani wurin.

Mama ta ce "Ka daina yi musu faÉ—a, ita ta haÉ—o kayanta ta ce barin gidan za ta yi"

Mai sunan baba ya yi wa rumaisa wani mugun kallo ya ce "Zaki wuce ki ajiye kayan nan, ko sai na zaneki, idan ki ka bar gidan, wurin uban wa zaki je, mara wayo" sumi-sumi ta shiga ta ajiye kayan a falon mama.

Har dare suna yi mata dariyar abun sa ta yi, wanda hakan ya sake tunzarata.

Mama tana kallon rumaisa ta tada kai da kayanta, ta ƙi yin shimfiɗa ta kwanta, kuma ba ta ci Abincin dare ba.

Mama ta girgiza kai ta ce "Ubangiji Allah ya shiryeki, ya rabaki da wannan rashin ji haka rumaisa, idan auren nan alkhairi ne Allah ya tabattar da shi, ya san silar shiriyarki ne".
Ta gyara mata kwanciyar, ta lulluɓeta.

***
Takawa ya ji zafin maganganun Mahmud sosai da sosai, abun yayi masa ciwo, sai dai ya bar abun a ransa, wani irin takaici ya cigaba da ci masa zuciya, a rayuwarsa ya tsani raini da wulaƙanci, amma Mahmud ya ci masa mutunci haka.

Aliyu ne ya faÉ—o masa, dan haka ya kira shi, domin jin idan babu wata matsala.

Aliyu sai da ya É—an ji kunya, ya ce "Tuba nake babban yaya, ni yakamata na kiraka, ya ka je gida?"

Adam ya ce "Lafiya ƙalau, ya mama?"

"Tana lafiya, ta ce za ta yi maka godiya, amma muka tarar ka tafi"

"Ahh haba, ba wannan tsakaninmu, ina fatan babu wata matsala, dan irin yaran nan, ka san suna da nasu yaran, duk da an kama su, kar su cutar da ku, ko kai ko ita da yayi iƙirarin zai kashe".

"Aliyu ya ce babu wani abu, duk muna Lafiya, mutuniyar ce dai ta tatara kayanta wai barin gidan za ta yi, ba a ƙaunarta".

Adam ya ce "What? Ku saka ido a kan ta sosai fa, na fuskanci za ta iya aikata duk abun da ta ce, kar ku je ta yi wani wurin"

Aliyu ya yi murmushi ya ce "Babu in da zata je, mai sunan baba ya tsawatar mata".

Adam ya ce "To Allah ya tsare, ka gaida mutanen gidan"

"Za su ji in sha Allah, a gaishe mana da mai sunan babanmu"

"Zai ji in sha Allah".

Ganin yadda rumaisa ta addabi kanta, ya sanya mama sakkowa daga fushin da take yi da ita, ta yi ta mata nasiha, duk da ta san nasihar tata ba ratsa rumaisa take yi ba, dan za ta iya gama nasihar tana fita tsakar gida, ta É—ora daga in da ta tsaya.
Bayan ta gama yi mata nasihar, ta dubeta ta ce "Ni kuwa rumaisa, ya batun al'ada ne? Tun da ki ka dawo baki yi ba fa, ko kin yi a can hannun Æ´an bindigar?"

Rumaisa ta ce "Wace al'adar?"

"Jinin haila mana"

Rumaisa ta ce "Taɓ, ni fa tun da na yi sau ɗaya, na fitsarin jinin nan, ban kuma yi ba, Allah ya yaye mini, shi ma dan wannan mugun mutumin ya watsa mini ruwan kwata ne na yi" mama ta ɗan yi jimm tana kallonta, dama hakan ta kan faru ga macen da ba ta saba yin al'ada ba, amma ta ƙudirce a ranta za ta kai rumaisa asibiti.

Adam yana office ɗin sa, yana tsaye a jikin window yana kallon titi, hannunsa riƙe da kofin shayi, yana ta tunani daban-daban, ƙarar buɗe ƙofar office ɗin ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya waiwaya.

Jamil ya gani kamar an koro shi, Adam ya ce "Ya dai? Ya na ganka a haka kamar ba lafiya?"

"Adam da gaske aure zaka yi?"

Adam ya ajiye kofin hannunsa ya ce "In ji wa?"

"Mai girma turaki ne ya sanar da ni"

"Ba yana umara ba?"

"Magana mu ka yi da shi ta video call"

Ya juyo ya fuskanci jamil sosai ya ce "Haka ne, Turaki ba zai yi maka ƙarya ba"

"Amma Adam idan ka yi wa Samha haka ka yi mata adalci kuwa? Meyasa zaka auri wata ba samha ba, ko dan ba ƙanwarka ba ce ba ka san zafin so ba?"

Adam ya shafi sumar kansa ya ce "Ba soyayya nake dubawa ba, makomar É—ana nake dubawa, samar masa da jajirtacciyar uwar da za ta kula mini da shi"

"Kana tunanin akwai wanda zai so É—anka, ya nuna masa kulawa sama da ita da suke uba É—aya da Aisha"

"Ba za a rasa ba" ya bashi amsa cikin ko in kula.

Cikin fushi Jamil ya ce "Anya kuwa kana da imani Adam, duk wahala da son da yarinyar nan take yi maka, ba zaka duba ba".

"Jamil, maganar ammi zan ajiye na bi son zuciyata ne?"

"Kana nufin ammi ce ta zaɓi wadda za ka aura?" Abun da Jamil ya faɗa, ya sanya Adam sanin cewa turaki bakomai ya gaya masa ba dan haka ya ce "Ina nufin ammi ma ta yi amanna da Yarinyar"

"Kenan menene makomar Samha?"

Adam ya numfasa ya ce "Da zan iya, da na haɗa su su biyu, sai dai ba zan so gidana ya zama irin gidanmu ba, bana son damuwa, kuma na san dole zan cutar da ɗaya a cikinsu, Samha ƙanwata ce, muna da alaƙa ta jini da ita, zan iya karkata gareta, saboda kusancin alaƙarmu, ita kuma waccan ta yi mini abun da ko duniya zan ba ta ba zan biyata ba, zan iya karkata gareta dan girman halaccin abun da ta yi mini. Sai dai a duk su biyun babu wadda zan gazgata cewar ita zuciya ta ke so, abu ɗaya na sani" ya taka gaban Jamil yayi ƙasa da muryarsa ya ce "Bana son ɗana ya yi rayuwa irin wadda mahaifiyarsa ta yi, so nake ya rayu a matsayin sa na cikakken ɗa a gidan mahaifinsa, ka san abun da nake nufi".

Ayshercool.
08081012143

PAID BOOK NE, ₦500 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143.

Cikin tsananin mamaki, Jamil ya kalli Adam ya ce "Me ka ke nufi?"
Chapter 133 · 0% Book details