← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 174

Sashe 167

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai meyasa Æ´an dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da É—ankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba".

Mahmud ya yi dariya ya ce "Wow, i like your confidence "

"Wai kai ya sunaka ne?".

"Mahmud" ya bata amsa, É—an turus ta yi tana kallon sa, "Dan Allah da gaske?"

Ya ce "Eh"

Ta ce "Innalillahi, sunan babana, sunan É—a na"

ya ce "Shikenan na yi Æ´a, na zama daddynki"

Ta yi dariya ta ce "yauwwa to ka taɓa zuwa ka ga ɗa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi".

"Zan je wataran".

Rumaisa ta ce "A'a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taɓa gani ba, kai ma sai mu je ka ga ɗa na, mai sunan ka".

Mahmud ya ce "mijinki ya huta kallon Tv, ke kaÉ—ai kin isa ba shi dariya".

Ta ce "Taɓ, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita" ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy.

Ya ce "Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata"

Gaba É—aya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo.

Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ruƙayya, sai dai suna haɗa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faɗuwa.

Mummy ta ce "Wace wannan?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya".

Mahmud ya kalli Samha ya ce "Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba" ya kalli rumaisa ya ce "Daughter, ga mamana nan"

"To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?" Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa.

Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce "Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?"

Mahmoud ya ce "A'a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata".

Fauziyya ta ce "Tirƙashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma"

Samha cikin ƙuluwa ta ce "Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye alaƙarta da ke, tun da ba ɗanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?"

A fusace rumaisa ta ce "Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba".

Mahmud ya ce "Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana".

Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce "Barka da wannan lokaci "

Mummy ta ce "Barkanmu dai, kuna lafiya?".

"Lafiya ƙalau"

"Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini É—an naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?".

Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

Mummy ta ce "Ruƙayya, ki saka a kawo mata abinci".

"A'a na ƙoshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi".

Cikin ƙarfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ƙirjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta.

"Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk Æ´aÆ´anmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruÉ—ani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun 'yan bindiga, abun bai yi mana daÉ—i ba".

Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud "Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka alƙawarin" kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taɓin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban.

Yayi murmushi ya ce "To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta".

Rumaisa ta ce "Eh, Mummy sai anjima "
"To amarya, sai mun zo gidan naki kuma"

Allah ya kawo ku.

Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ruƙayya ya ce "Wannan ƙannena, ga Fauziyya ga ruƙaiyya"

Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce "Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini Æ´ar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaÉ—ai ya yi mini mutunci a gidansu".

Yayi murmushi ya ce "To shikenan mu je" suka fita.
Samha ta tashi zaune ta ce "Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa".

"Jikina ya na bani akwai wani abu ɓoyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su"

Fauziyya ta ce "Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye"

Mummy ta ce "Na gani" nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa.

Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya É—an fara É—agawa.

Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sauƙin kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce "To shikenan, ki gaishe mini da takwarana". Ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa"

Ya É—an yi jimm yana kallon rumaisa, "Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir".

"Ki shiga ki É—auko shi, ki kawo shi na ganshi".

Ta noƙe kafaɗa, kawai ya tsinci kansa da bin rumaisa.

Ba Ammi ba, har iman sai da ta razana, ganin Mahmud a filin falonta, shi kansa tsayawa ya yi yana bin su da kallo, rabonsa da falon nan, kusan shekara da wani abu, da Ammi ta neme shi, ta nemi alfarmasa kai tsaye ya ce ba zai yi ba.

Ammi ta ƙure shi da ido, kamar yau ta fara ganinsa.

Kallo ɗaya ya yi wa ammin, ya sunkuyar da kansa, ƙasan zuciyarsa yana tuna abun da ya yi mata na ƙarshe da ya kasa mantawa.

"Ashe ka dawo, ya makarantar?"

Ba tare da ya É—ago kai ba ya ce "Lafiya lau"

Ruma ta ce "Ka zauna mana" ta nufi in da Sabir yake wasa da kayan wasansa, yana ta rarrafe yana ɓarna, ta ɗaukko shi ta kawo masa shi.

Ya karɓi sabir, ya zauna da shi a jikinsa, ta kalli sabir ta ce "Waye wannan?"

Sabir ya ƙura masa ido, Mahmud wani murmushi ya saki, ya shafa kan Sabir, wata irin ƙaunar yaron ta shiga ransa, da yake jin tamkar daga jikinsa ya fito. Har aka yi dambarwar nan aka gama, bai taɓa ganin Sabir ba.

Cikin murmushi ya ce "Na yi kama da babanka ko, nima babanka ne"

Su Nusaiba kamar tv, haka suke kallon Mahmud da rumaisa.

Ruma ta ce "Ba papa ba ne, uncle ne wannan"

Mahmud ya ce "A'a Daddy dai" ya miƙe da Sabir a hannunsa ya nufi hanyar waje yana faɗin "Allah ya bani  ɗa ba mata"

Ruma ta bi bayansa tana cewa "Ai wallahi gara in bar maka takawa da in bar maka Sabir"

Ammi ta ce "Kun ga ikon Allah, me rumaisa ta gaya wa yaron nan ya yarda ya zo in da nake?"

Nusaiba ta ce "Wallahi ammi ni ma mamaki abun ya bani, wancan karon fa, kalli yadda aka kai ruwa rana, kan ya zo kiran da ki ka yi masa, bai kuma zuwa ba, kin ga ikon Allah yau shi ne har cikin falonki, kai lamarin baiwar Allah nan yana É—aure mini kai"

Kasa jurewa Ammi ta yi, ta fashe da kuka, nan da idonta ya yi ja.

Iman ta ce "Ammi dan Allah ki yi haƙuri, ki cigaba da jurewa, jikina ya na bani komai ya kusa zuwa ƙarshe"

"Allah ya sa, ina fatan hakan".

Yauwwa share hawayen, iman ta yi maganar tana gogewa Ammi hawayen fuskarta.

Mahmud kuwa ba abun da yake sai dariyar shirmen rumaisa.

"Ka ga daga nan, ba zan É—ara ko ina ba, sai ka bani É—a na, daga gani sai ka ce zaka tafi da shi, to in gaya maka yau gidanmu zamu tafi da shi, sai ranar Litinin za a dawo da shi".

"Ta yaya zaki kula da shi? Kema baki wuce a kula da ke ba ai"

"Zan iya, wanka ne dai, sai in saka ko baba uwani, ko su barira su yi masa wanka".

Ya ce "Baba uwani kuma?"
Ta taɓe baki ta ce "Na fasa ba ta, ni matar nan ba ta yi mini ba, dan dai kawai ammi ta ce ta zo ta zauna da ni ne, ta yi saka ido, kamar mara gaskiya".

"Daughter, ki kula sosai da lamarin gidan nan kin ji ko? Sannan kar ki yadda wani ya din ga sanin abun da yake faruwa a gidanki, mussaman baba uwanin".

"Kai ma ka lura ta na da saka ido ko?"

Mahmud ya ce "Eh to kusan haka, sannan ki kula da takwarana sosai, da sosai"

"Taɓ, ka manta ni na kula da shi ranar da aka haife shi ranar majaifiyarsa ta bar duniya, kwananmu uku muna bulayi a daji, bamu samu hanya ba, na zaci ma mutuwa zai yi " ya ɗan ware ido ya ce "Haba dai"
Chapter 167 · 0% Book details