Sashe 157
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin É—aukar ta.
Haka ma ƴan mazan nan, Aliyu cewa yake "Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ƙarama wallahi".
Usman ya ce "To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?"
"A'a addu'a kawai nake yi"
Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faɗa da ya haɗa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faɗa ba, haka suka kai har wurin ƙarfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure.
Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam.
Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matuƙar tafasa da wani irin masifaffen kishi.
Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba.
Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banÉ—aki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a É—aki.
Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faÉ—i, dan ya É—auka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich É—in É—akin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke wai a nan ki ka kwana?" Yayi maganar yana taɓa ta.
Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi.
"Tashi, ki je ki yi salla" nan ma bata tashi ba.
Toilet ya shiga ya É—ebo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska.
A rikice ta tashi tana faÉ—in "Huzaifa meye haka wai?".
"Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini É—aki ki tafi ga naki can ba"
Maimakon ta yi magana, sai ta haÉ—e rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba.
Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya riƙe hannunta ya yi waje da ita, ɗaya bedroom ɗin ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta.
Kallon É—akin ta yi, wasu furnitures É—in ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai.
Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma É—akin da aka fara kai ta, wato É—akin da Adam ya ce nasa ne, ta buÉ—e drower ya É—au hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguÉ—a baki take ita kaÉ—ai tana harare-harare.
Ta koma ɗakinta, ta yi salla, ta idar ko addu'a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli ɗakin sai ƙamshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba.
"Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su ɗauki ɗakin ƙasa, ko shi baban sabir ya koma ƙasa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu" ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta.
Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet É—in.
Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi.
Shiru ta É—an yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce "In sha Allah sai na fita na koma gida".
"Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan, baƙi sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ƙasa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba".
Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce "To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba".
Mamaki ne ya kama shi, baƙar magana rumaisa ta gaya masa.
Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce "Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je"
"To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?"
"Wuce mu je na ce" ya faÉ—a a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa É—akinsa.
Ya nuna mata banɗaki ya ce "Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ƙasa suna jiranki".
Sai da ta gama kalle-kallenta a banɗaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a jiƙe, alamar yayi amfani da shi.
"Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba"
Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito.
Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buÉ—e wardrobe ya É—auko, kaya ya tsaya ta gama shafa man.
Ya kalleta ya ce "Ga kaya nan ki canza".
Ta karɓa ta ce "To a gabanka zan canza kayan?".
"Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?"
Zare masa ido ta yi, ya ce "Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani"
Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta.
Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito.
Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta.
Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace É—in yayi mata kyau sosai. Ba wani iya É—auri ta yi ba, dan haka kawai ta É—ora É—ankwalin a kanta.
Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi.
Iman ta ce "Amaryar takawa, ina kwana"
Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta.
Ya kalli iman ya ce "Ta yi a haka?"
"Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a É—an yi kwalliya sama-sama".
Rumaisa ta ce "Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a É—aÉ—É—aure kamar ba ta wa ba".
Iman ta ce "Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya".
Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu.
Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daÉ—i, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta É—aura mata É—ankwali.
Adam ya ce "Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi" Iman ta jinjina kai ta fita.
Ya kalli rumaisa ya ce "Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba".
"Kidnapping É—ina zaka yi kenan?" Ta yi maganar tana kallon sa.
"Eh" ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun da aka faÉ—a tana da amsar bayarwa..
Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta.
Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen.
Iman ta shigo ta ce "Yaya ku fito".
Ya ce "To, muna zuwa"
Ya sake kallon rumaisa ya ce "Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself"
Ta yi ƙuri da ido tana kallonsa. "Am talking to you" yayi maganar a ɗan kausashe.
"To" ta amsa a hankali.
Miƙa hannu yayi zai riƙo nata, ta janye a ɗan razane.
Ta girgiza kai ta ce "Ka daina taɓani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka riƙe mini hannu".
Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ikon Allah, to mu je" da ƙyar ta yadda suka jera, suka fita.
Suna fita aka din ga rafsa guÉ—a, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura.
Suka ƙarasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu'a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ƙuri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar.
Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta miƙawa adam hannu ta ce "Ban ga ka fito da ƙyalle ba, dan mu tabattar da me ka aura".
Ya ce "Haba jakadiya, wannan al'adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?" Yayi maganar yana kallon rumaisa.
Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?.
"To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka buƙaci gani, kar mu je saura aka kawo mana".
Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi.
Sai da ƙirjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce "Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan"
Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga ɗakin, na kwana a ƙasa, meye wani abun alfahari.