← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 174

Sashe 123

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasir ya ce "Ba ke ki ke son mai kuÉ—i mai kyau ba, gashi ya zo ki ce ba kya so, ke kin san menene son ma?"

Ta yi farat ta ce "Na sani mana, yanzu ba na ji ina son ku ba, ina son zama a gidan nan ba, ai shine son"

Huzaifa ya ce "Ji shashasha mara kan gado"

Abubakar ya ce "Ƙanwata, zo nan ki ji wata magana"

Rumaisa ta koma wurin yaya Abubakar ta zauna. Ya dubeta ya ce "Dan rumana ki girma mana, ki daina biyewa su Yasir, shi lamarin rayuwa Addu'a ake yi, Allah ya zaɓa mafi alkhairi"

Mai sunan baba ya fito ya ce "Ke tashi ki bar nan wurin, ta ce ba ta so, dole sai ka tursasata ta amsa ne?"

Abu ya nemi ya zama faÉ—a, sai da mama ta shiga tsakani.

Kasa jurewa Ammi ta yi, ta kira mama a waya take tambayarta yaya.

Mama ta ce "To, ni dan ta ni babu matsala, tun da kullum Addu'a da fatan alkhairi ka ke yi wa yaro, sai dai yayyenta wasu sun ƙi yadda, ita kanta ƴar ta ki ta ce ba ta so, mai sunan baba kuma ya goya mata baya".

Mama ta ce "Subhanallah, lamari bai yi daÉ—i ba, to shikenan ba damuwa"
Ammi har ta kashe wayar ta ji ta kasa jurewa.

Ta cewa Iman "Idan an idar da sallar magariba, ki shirya zaki rakani unguwa"

Iman ta amsa da to, ammi ta kira takawa a waya, ta ce masa idan an idar da sallar magariba ya zo zai kaita unguwa, ya amsa mata da to.

Mamaki ne ya kama takawa, da Ammi ta sanar masa da cewa gidansu rumaisa zasu je, ya fara tunanin mai zai saka ta ce su je gidan ba tsammani haka?
Ya din ga addu'a Allah ya sa ammi ba yarfa shi za ta yi ba saboda yarinyar nan.

Rumaisa kuwa ta fita sayen maganin sauro, daga zuwa soro ta É—au keken Huzaifa ta tafi da shi sayen maganin sauron, shagon da za ta sayo É—in a farkon layinsu yake, amma saboda tsabar neman magana ta É—au keke.

Ta shiga gida ba ko sallama ta fara da "Waye ya ajiye mini mota a wurin da zan yi parking É—in kekena, saboda an rainani".

Huzaifa ya ce "Uban wa ya saka ki É—aukar mini keke, ban hanaki É—aukar mini keken nan ba?"

"Huzaifa kana da damuwa, wannan kwaraɓaɓɓen keken kamar wani mota, ka kwantar da hankalinka, zan saya maka mota wataran".

Dalla wuce ki bani wuri, daga tsakar gida ta zauna ta ce "Mama ga maganin sauronki, canjin kuma na sayo coc zan sha, idan yaya usy ya dawo sai ya baki"

Ta ji shiru mama ba ta amsa mata ba, ta ware murya ta sake cewa "Mama ga aiken, canjin na sai coc".

"Ni zan biyoki tsakar gidan na karɓi aiken kenan?"

"A'a, zan ajiye miki a kan window, idan kin huce zan shigo É—akin, na san sai kin yi mini faÉ—a na kashe miki canji, kuma ba laifina bane raina ne ya biya ta É—au sanyi"

Mama ta ce "Zan kama ki ne"

Rumaisa ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Mama da wasa nake miki, kwata na faɗa da keken, bari na ɗauraye ƙafata na shigo".

Sai kuma ta É—aga hanci sama ta ce "Hmmm warin turaren baban sabir nake ji".

Huzaifa ya ce "Malama ki nutsu, wane irin turarene mai wari kuma?"

"Kai yasin turarensa ba daÉ—i, tayar mini da zuciya yake"

Daga ɗaki mama ta ce "Idan kin gama tsokanar tawa ki zo kin yi baƙi".

"Baƙi da daddaren nan kuma wurina suka zo? Anya wannan baƙin alkhairi ne da daddare? Ai sai ace bani da gaskiya" ta je ƙofar ɗakin mama tana leƙewa, ta ga Adam da ammi sai iman.

"Kaii ammi ke ce da daddare, Innalillahi amma baku ji me nake cewa ba ko?"

Ammi ta ce "Bamu ji komai ba, ance ba a sonmu ban ga ta zama ba, na ce bari na zo ƙafa da ƙafa".

Rumaisa ta shigo ta zauna daga wajen bakin ƙofa ta ce "Ammi ina wuni?"

"Lafiya ƙalau maman sabir, kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau ammi, iman ya kike ina sabir?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Yana gida, yana gaisheki".

Ammi ta ce "Rumaisa, yau gani ga ki ga baban sabir, ki gaya mini meyasa ba kya son sa? Gaya mini abun da ya yi miki?"

Ruma ta kalleshi ta ce "hmm mama ki rabu da shi kawai, ni dai kawai bana son sa"

"Ai ba a ƙiyayya babu dalili rumaisa, gaya mini meya haɗaku?"

Rumaisa ta ce "Ammi kina ganin hantarata yake yi, yayi ta hararata"

Adam kuwa takaici ne ya ishe shi, kamar shi, wai ake lallaɓa wannan ƙwailar yarinya wai ta aure shi, wanda da shi mai kule-kulen ƴan mata ne, da bai san iya adadin ƴan matansa ba.

Ammi ta ce "Rumaisa, bani da nufin cutar da ke, har ga Allah ina matuƙar ƙaunarki, ba zan so abun da zai cutar da ke ba. Daga yanzu zuwa kowane lokaci magabata zasu fara yi wa adam maganar aure, bana son a bashi matar da zata wahalar da sabir kamar yadda mahaifiyar sa ta fuskanta.
Kin ga aisha ina da alaƙa da ita, itakaɗai mahaifiyarta ta haifa ta rasu, ta sha wahala sosai a wurin matar uba, mahaifinta yana basarake amma ta kwana ba ta ci abinci ba. A kulle ƙofa ta wuni a haraba, banda duka da cin mutumci, ta sha wahala a rayuwa sosai da sosai, zaki so sabir ya fuskanci irin haka?"

"To Ammi ba sai ki riƙe shi ba"

"Rumaisa dole wataran zan bar duniya, ko bana so dole sabir ya koma hannun mahaifinsa, ba ni zaki duba ba, ba baban sabir ba É—an ki. Zaki samu cikakkiyar damar kula da shi sosai ya zama naki"

Wayar iman ta fara ringing, dan haka ta tashi ta fita waje amsawa.

Rumaisa ta yi shiru tana tunani, ammi ta ce "Ba zan takura miki ba rumaisa, ba zan so ayi miki auren dole ba, idan baki amince ba shikenan, ba zan takura miki ba, na so dai ki zama É—aya daga cikin iyalaina ne, ba takuraki zan yi ba rumaisa".

Shiru ruma ta yi, ba ta ce komai ba.

Har ammi ta fidda ran rumaisa za ta yi magana, dan takawa ya fara ƙulewa.

Mama ta ce "Rumaisa ke fa ake jira ki yi magana".

"Mama tsoro nake ji, Æ´an ajinmu sun ce maza mugwaye ne, wai ba Æ´an goyo bane, tsoro nake ji ni yarinya ce".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Ya danganta, kuma ba haka abun yake ba, ke kin yadda ba ƴan goyon bane? Ke yanzu ba ƙanwar maza ba ce, kalli yadda suke kula da ke fa, komai yi miki suke, da kin motsa damuwarsu a kanki take, da ba ƴan goyo bane, ai ba za su yi miki haka ba, ki yanke hukunci da abun da yake ranki, ba surutun mutane ba".

"Ammi na amince!"

Ayshercool.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
Chapter 123 · 0% Book details