← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 174

Sashe 44

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ina ƙara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ƙure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki buƙatar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sauƙi a gareni, amma ni ba hakan nake buƙata ba, haɗin kanki kawai kiyi tunani amma".
Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

"Samha, me ki ke tunani ne?"

Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama zaɓa tukuna"

Samha ta ce "Shikenan" sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

***
Sam ruma ta rasa sukuni, gaba É—aya sallolinta addu'a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo É—ari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa a gidan.
Gashi har wayewar garin yau ba ta samu kuÉ—in ba, wunin ranar bai kulata ba, bai kuma ce ta bashi kuÉ—in ba, sai da dare yayi, ta rasa dalilin da ya sanya yake son hukunta ta da daddare ya hanata bacci.
Tana zaune zuruu ta takure, tana zancen zuci ta ga ƙafafuwan sa, tana ɗaga ido suka yi ido huɗu.
Take ta rikice ya fara "Wallahi yaya ban samo kuÉ—in nan ba, ban san a in da zan samo su ba, kayi mini rai dan Allah".

"Kin san ba ki da inda zaki samo kuÉ—in kika arar mata kuÉ—i, da uban wa zaki biyata da? Wato sata ki ke kenan"

Cikin kururuwa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi ban taɓa ɗaukar kayan wani ba. Wallahi dama niyyata na tara mata, sai na biyata amma wallahi bani da kuɗin da zan biyaka dan Allah kayi haƙuri"

Cikin kaushin murya ya ce "Sai fa kin nemo kuÉ—ina kin biyani, ko a ina ne"

"Wallahi sai dai in kayana za a sayar a biyaka, amma wallahi bani da su"

"Wallahi da kin samo kuɗin nan kin bani, sai na taka kanki, ta tabatta sata ki ke yi, ko a gida ko a waje, amma sai Allah ya ƙwace ki, kin yi sa'a da kin gane shayi ruwa ne, sai na sakaki a mari na kulle, kuma ki cigaba da abin da ki ke yi kar ki fasa, idan ki ka kaini bango sai dai ki ji an ɗaura auranki da malam Ladan, ko na sakaki a mari" jikin Ruma har ɓari yake, saboda wannan taratsin da yake yi mata kamar ta yi fitsari haka take ji. Ba ta samu damar shaƙar isashiyar iska ba, sai da ya bar ɗakin ta dinga ajiyar zuciya.
Mama kuwa sam ba ta tanka musu ba, dan a yanzu kowane hukunci mai sunan Baba zai É—auka a kan ruma, ba zata nema mata sassauci ba, saboda ruma babu alamar shiriya a tare da ita.

Sai da wannan ƙurar ta lafa, sannan ruma ta samu nutsuwa, ta cigaba da harkokinta.

Kamar mai É—aukar karatu, haka ta nutsu a kan waya, tana kallo a Instagram wani abun ta yi dariya wani tayi tsaki.

Kan wani hoto taje, wani kyakkyawan mutum, ya sha kayan graduation, yanayinsa bai yi yanayin fara'a ba, amma ya ɗan geɓare baki yayi murmushi, har za ta yi liking saboda a rayuwarta tana son ta ga mutanen da suka yi nasara, musamman ta kammala karatu.
Kawai sai ta sake wurgawa, ta ga wani hoton nasa a cikin turawa, ta dinga dubawa, sauran hotunan duk a cikin turawa, da kuma aji na karatu, ajin tamkar ofishin wani shugaban ƙasar.
Haushi ne ya kama ruma da tuno yadda ajinsu yake, sheranjiya da aka yi ruwan sama, suka je suka tarar ruwa ya cika ajinsu, murfin kwano ya yaye, sai haÉ—esu suka yi a wani ajin.
Ai babu tunani ta shiga comment section ta ce An ɗibi haramun an je karatu, Allah ya isa kuɗin talakawa, ɓarayin kuɗin mutane, bamu yafe ba muna fama ajinmu ko rufi babu.  daga haka ta ƙara gaba, ta cigaba da kallonta.

Ta gama abin da take, ta ajiye waya ta shiga nata shagali.

Sai da daddare ta dawo, ta sake É—aukar waya, ta ga an yi mata reply a message, ta yi ta murna yau an kulata a Instagram, dan ganin mutanen Instagram É—in take wasu mutane daban.

Sai dai tana dubawa ta ga wani yayi mata replying da 'Ya aka yi ki ka san da kuÉ—in talakawa ya yi karatun'

Cikin zafin rai ta rubuta 'Idan gaskiya ne meyasa ya tafi ƙasar waje karatun, su yi a Nigeria mana" ta rufe datar ta ajiye tana huci, tare da ɗan jin releif a ranta, dan ta daɗe tana son samun damar da zata isarwa irin wannan mutanen abin da yake ranta.
Yanzu take jin kallon waya yayi mata rana, da ta ƙi yin zuciya har ta iya yadda ake amfani da irin wannan abubuwan.

***
Takawa ne riƙe da waya a hannunsa, Jabir sai surutu yake yi masa, amma kasancewar suna da banbancin hali shi da Jabir, ya sanya Jabir bai damu da rashin amsawar Takawa ba, saboda shi mutum ne ba mai yawan magana ba.

Can Adam ya É—ago rai a haÉ—e ya ce "Kai, wai ban hanaka É—ora hotuna na a social media ba?"

Jabir ya yi dariya ya ce "Tuna baya ne, ya sanya na É—ora gashi ka yi kasuwa 'yan mata sai comment suke yi, waÉ—anda kuma suka sanka, suna yabawa tare da jinjina maka"

Adam ya yi guntun tsaki ya ce "Kana da matsala" har ya wuce account É—in Jabir, kawai ya koma ya shiga comment section yana dudduba abin da aka ce.

Sai dai lokaci ɗaya annurin fuskarsa ya ɗauke, har wata zufar ɓacin rai ta fara tsatstsafo masa a goshinsa, duk kusan ko yaushe a cikin damuwa yake, amma ya daɗe bai ci karo da abin da ya daki zuciyarsa kamar wannan ba.
Ya É—aga ido yana kallon Jabir, Jabir ya ce "Ya dai, ya na ga kana kallona?"

Riƙe wayar yayi, ya cigaba da kallon Jabir, Jabir ya miƙe ya duba wayar, ya yi tozali da abin da ya sanya Adam ɓacin rai.
Jikinsa ne yayi sanyi, dan sam bai san an yi wannan comment ɗin ba. Yana ƙoƙarin yin magana takawa ya ce "Kira mini Sidi a waya, ayi mini tracking ɗin account ɗin nan"

(Mun kusa kammala book1 in sha Allah, mai buƙata yana iya yin payment na book 2.
500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank. Sai a turo mini evidence of payment ta 08081012143, zan ɗan bada time kan na cigaba da book2, sai an gama payment, hajiyata idan har kina iya sayen data ki saka a wayar ki, to ki tara kuɗi ki sai book ɗin Ƙanwar maza, you will never regeret tafiyar akwai ƙaruwa a cikinta. Ina alfahari da ku masoya)

Ayshercool
08081012143
                ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

                      P21

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki  glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu  shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
Chapter 44 · 0% Book details