← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 174

Sashe 137

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ƙosawa Mummy ta ce "Hanzarta, ina jin ki"

"Takawa zai yi aure, sai dai alamu sun nuna kamar Iman zai aura, kuma zancen ya iske Samha ƴar wurin turaki, dan ɗazu ta zo har wurin Iman ɗin ta yi mata kashedi da zafafan kalmomi, dan na laɓe na ji komai"

"What? Aure kuma? A wannan karon kuma ita za a liƙawa, ita ma ya cinyeta, lallai giwa ba ta tsoron Allah, amma na yi mamakin yadda aka yi Samha ta zo ba ta ƙaraso nan ba, kuma ba ta yi mini wannan bayanin ba, ko da yake ni kujera ce, ko dan zama za a neme ni, jeki na gode na ga yadda wannan lamarin zai yiwu"

Baba uwani ta ce "Godiya nake, na barki lafiya".

Mahmud ya so shiga ɗakin Mummy, dan ganin wacece wannan, take zuwa a tsohon daren nan, amma ya fasa, ya lallaɓa ya buɗe ƙofa ya fita harabar gidan ya laɓe.

Can baba uwani ta fito tana dudduƙenta cikin duhuwar fulawoyi, ta nufi sashinsu ammi, tana buɗe ƙofar, fitila ta hasketa, dan haka ya ganeta da kayan jikinta.
Hakan ya fallasa ma wacece ita, domin kuwa baba uwani kayanta ba ɓoyayyu bane ba, duk da tarin alkhairai da suturar da ammi ke bata, amma kullum cikin kaya ɗaya zuwa uku take.
Kan sa ya É—aure da mamakin me take zuwa yi sashinsu, a wannan daren cikin siga ta rashin gaskiya

A hankali ya koma sashinsa, gaba ɗaya baya son wannan halin na Mummy, na bin diddigi da shiga abun da babu ruwanta, ya san ƙarshe ba zai wuce rahoton wani abun ake kawo mata ba. Amma ya sha mamaki, idan har ace hadimar ammi ta kusa da ita, za ta aikata mata haka, to duniya kowa ma ba abun yarda bane ba.

***
Kwanci tashi asarar mai rai, mai girma turaki ya dawo daga aikin umara da ya tafi, duk da an riga an saba zuwa, amma ba a rasa Æ´an sannu da zuwa da su kan zo, domin yi masa barka da dawowa.
Ammi ba ta son takura masa, dan haka ta bashi lokaci, tare da sauraron abun da zai ce mata.

Duk da a nata ɓangaren ta tsananta addu'a a kan lamarin sosai da sosai, tare da fatan tabattuwar alkhairin da yake cikin al'amarin.

Ɓangaren Samha kuwa, da fari a iya tunaninta, za ta iya ji da lamarin, amma abun ya shallake tunaninta, kuma gaba ɗaya hankalinta ya karkata a kan Iman ce ake ƙoƙarin aurawa takawa, dan haka ta fara tunanin yadda za ta yi da ita, a ƙarshe dai ta koma wurin Khalifa, domin samun mafita sannan ta je ta samu Mummy da zancen.

Mummy ta yi dariya ta ce "Yaro man kaza, ai na yi zaton ba zaki gaya mini ba, shi ya sanya na zuba miki ido na ga iya gudun ruwanki, ba shakka giwa wata irin murɗaɗɗiyar mace ce, mara alƙibla, dan haka dole ki zage ki san abun yi"

Cikin damuwa ta ce "To ni yanzu Mummy ya zan yi?"

"Duk abun da ya kama ki yi, ko dai a kan Iman ɗin, ko kuma a kan giwa ko ma adam ɗin. A baya babu abun da ba mu yi ba a kan yarinyar nan, wanda hakan ya sanya duk ta rasa manemanta manyan mutane da suke zuwa wurinta, dan haka yanzu shine giwa ta yanke shawarar ƙarshe na aura mata adam, shawara ta rage gareki, ko dai ki bari ayi auren daga baya ki san abun yi, ko kuma dai ki ɗau wani matakin"

"Taɓ, ai wallahi da na bari ya aureta, gara uban kowa ma ya rasa, ni Mummy a cikin malamanki nake son ki haɗani da wani, a watsa komai ko da kuwa yana nufin in rasa ta rasa kowa ma ya huta ne"

Mummy ta jinjina kai tana murmushi ta ce "To shikenan, zan yi tunani a kai kar ki damu"

"Mummy ba ni da dogon lokacin da zaki yi dogon tunani, dan Allah ki taimaka".

"Na ji zamu yi waya, ko zuwa sunday ne, akwia wani ƙauye da nake zuwa, sai mu tafi tare"

Samha ta ce "To shikenan, na gode sosai Mummy".

Kusan sati guda da dawowar mai girma turaki, giwa har ta fara ƙosawa, tana tunanin ko magana za ta yi masa, babu tsammanni ya kirata a waya ya ce zai zo.
Hakan yayi mata daÉ—i, sai dai ta shiga fargabar da wacce zai zo, da nasara ko kuma babu?"

Kasancewar baba uwani na wurin, ammi ta yi waya da turaki, baba uwani ta saci hanya, ta je ta kira mummy a waya, ta kai mata rahoton cewar turaki zai zo, kuma da alama magana mai muhimmanci zasu tattauna, dan haka Mummy tace lallai ta sanya mata ido, ta naÉ—o mata duk wani rahoto na abun da zai wakana.

Bayan sallar azahar, mai girma turaki ya iso gidan, kai tsaye ya sauka a sashin giwar da.

Hadimai suka shiga hidimar kawo kayan ciye-ciye, sai dai turaki yaƙi magana a kan haƙiƙanin abun da ya kawo shi, a lokacin da hadiman ke kaiwa suna komowa.
Dama tuni ammi ta hana Adam fita, ta ce lallai koma menene ya zauna ayi a gabansa, dan haka shima yana nan.

Ammi ta sallami hadimanta, Sannan ta nutsu ta fuskanci turaki.

Hakan ba ƙaramin ɓatawa baba uwani rai yayi ba, dan babu damar samun rahoton da take son samu.

Ammi ta dubi turaki ta ce "Ranka ya daÉ—e an dawo lafiya ya hanya? Ban samu shigowa ba, saboda ba na son zuwan nawa ya zama takura ko matsi a gareka, shiyasa ban yi maka sannu da dawowa ba"

Turaki ya ce "Kar ko damu, da ke da abun ya shafi zuriyar marigayi, dolenmu ne, kuma babu yadda za ayi ku zama takura a garemu.
Toh! Na zo da saƙonki, a can saudiyya ma na je gidan ɗan uwanki mahadi, mun tattauna da shi sosai, kuma ya bayar da amanna sosai. Sai dai da muka dawo gida da kwanaki uku, mun sami wambai, in da ya nuna rashin amincewarsa da nuna za a sake zubar da darajar masarauta, ta hanyar auro wadda ba jinin sarauta ko tushen arziki ba, sai dai na yi iya yina na nuna masa ƴar gidan daraja ce da kuma gudunmawar da ta bayar.
Har ila yau ya gaya mana zancen da bamu ji daɗinsa ba, ya kawo ƙorafi sosai a kan ka takawa, ciki har da yinƙurin taka ɗan uwanka da mota, wannan lamari bai yi mana daɗi ba, ya ce ya bayar da saƙo ka je, nan ma ka yi burus. Abun bai yi mana daɗi ba, har yayi iƙirarin babu shi babu kai, sai dai mun yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali, in da har mai ɗakinsa ta sanya baki, ta hanyar nuna masa tsaurinsa a gareka yayi yawa, shiyasa ba kwa shiri, amma dai duk da haka yakamata a din ga lura ana kiyaye wasu abubuwan, yanzu idon duniya a kan ka yake".

Ammi ta ce "Wallahi ranka ya daÉ—e, abun da nake yawan gaya masa kenan, amma dai a cigaba da jaddada masa"

Turaki ya ce "Haka ne, akwai buƙatar a din ga kai zuciya nesa, akwai abun da yarinyar nan ta faɗa mini a kan ka, wanda kuma tabbas haka ne ba ta yi ƙarya ba, yana daga dalilan da ya sanya na yi amanna da auren nan sosai, nake yi muku fatan alkhairi".

Ammi ta ce "Allah sarki, Adam kuma ya sunkuyar da kai, yana murza zoben hannunsa.

"To, mun dai yi ƙoƙarin shawo kan wambai da ƙyar, duk da yana nuna ba da yawunsa ba, amma ba wani abun damuwa bane ba zai sakko, illa iyaka kai takawa ka je ka same shi ka bashi haƙuri.
Magana ta gaba kuma, a sanar da iyayen Yarinyar nan, ranar juma'a zamu kai kuÉ—in aure, kuma wata biyu zamu sanya rak, Allah ya tabbatar mana da alkhairi dan ba ma fatan a jinkirta wani abun ya zo ya gilma".

Ammi ta faÉ—aÉ—a murmushin ta tana faÉ—in "Alhamdilillah, Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana da rai da lafiya"

Yayin da adam wata irin mummunar faɗuwar gaba ta same shi, kansa ya sara da ƙarfin gaske, ya ji tamkar ɗakin yana juya masa!

Ayshercool
08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
Chapter 137 · 0% Book details