← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 174

Sashe 168

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Wallahi da gaske nake, ka san yadda ake garkuwa da mutane kuwa, to in gaya maka har sunan wasu na ji, Anty Aisha fa wasu ne suka saka a saceta, saboda papa" kallon ruma yake cikin mamaki. Ta cigaba da cewa "Kuma wai ƴan gari ba su san meyafaru ba, suka ce shi ya kasheta yayi tsafi da ita, na san abubuwa da yawa, na ƙi gaya masa, ya fiye fushi da zafin zuciya, shiyasa maƙiyansa suke nasara a kansa. Ai ni na fi shi wayo fa, in gaya maka ranar da muka tafi katsina a kan bullet da bindigogi na zauna, jakunkunkunan, duk an yi musu lamba, duk na haddace lambobin. Har da wani gari da na je, an ƙona garin, na ga wani tsoho, muka yi hira da shi".

"Amma Meyasa ba zaki gaya masa abubuwa da ki ka sani ba?"

"Sai abu biyu ya faru, ya daina saurin fushi da zuciya, na biyun kuma ba wanda zan gaya wa"

Murmushi yake yana kallon rumaisa, ta fiye surutu, but she's very talented akwai hikima, da kaifin basira a maganganunta.

"Me ki ke yi a nan wurin?" Ta ji muryar takawa a kausashe.

"Daddy na kawo wa Sabir, ya ga takwaransa".

"Uban waye ya ce ki bashi É—a na?"

Ya tunkari Mahmud, zai karɓi Sabir, amma Mahmud ya riƙe Sabir, by force Adam ya hankaɗe shi, ya karɓi ɗan sa, har ya yi gaba ya dawo, ya fizgi hannunta ya nufin sashin Ammi da ita.

Ya balbleta da bala'i "Kin san hatsarin da yake cikin abun da ki ka aikata? Kin san me gayen nan zai iya yi, da ki ka É—auki É—a na ki ka bashi, What if yayi amfani da hakan against me? Wani irin gargadi ne ban yi miki a kan yadda za ki zauna da mutane a gidan nan ba?"

Rintse idonta ta yi, saboda yadda yake ta zazzaga mata masifa.

Ammi ta taso, ganin yadda jikin Adam yake rawa, ta karɓi Sabir, ta ja Adam ta zaunar da shi, ta ce "Wannan haƙilon na meye haka? Ka kwantar da hankalinka ba abun da zai faru".

"Ammi yarinyar nan ba ta jin magana, duk abun da zan gaya mata ba ta ji".

"Ni dai na san ba da kunnen wani nake ji ba, kuma na san abun da na aikata dai-dai ne, ko ba komai na saka uwa ta ga ɗan ta, tun da har ammi ta ji daɗin abun da na yi, ta ga ɗan ta, na ji daɗi, Kuma ni yana yi mini kirki ina ruwana da faɗanku, ni duk wanda yake son sabir ina son sa, na ga kai har cewa ka yi kar a sake bari na shigo gidan nan, shi ya ce a bar ni na shigo, na roƙe shi ya zo ya ga Sabir, ya zo ya ganshi, ya kaini na gaida mamansa, duk da na san ba mamansa ba ce ba".

Adam ya sunkuyar da kai, ya dafe kansa, me zai gaya wa wannan burkitacciyar yarinyar da zai sa ta gane, irin hatsarin da wautar ta ka iya jefasu, da ta wanke ƙafa ta tafi sashin Mummy.

Ammi ta ce "Rumaisa waye ya gaya miki É—a na ne?".

"Da ke yake kama ai, ba ita ba, kuma wannan matar da zata gaya mini magana ya tare mini, to ammi ni sai in shiga faÉ—an da ba ruwana? Kuma É—an uwan baban mutum babansa ne, dan haka shi ma baban Sabir ne".

Ammi ta ce "Gaskiya ne, je ki ki shiryo, ki zo ku tafi, dama neman da muke miki kenan"

Ruma ta wuce ta je ta haÉ—o kan jakarta, da kayanta, ammi ta din ga yi wa Adam faÉ—a tana rarrashinsa, a kan ya bi rumaisa a hankali.

Ganin adam ya tashi zai tafi, ya sanya Ruma cewa Ammi Sabir É—in fa.

"Yayi fushi ne, ki yi haƙuri gobe in Allah ya kaimu, za a kawo shi, ku tafi, ki rabu da shi yau ya ɗau zafi".

"Ammi, meyasa papa da É—an uwansa suke faÉ—a? Ni fa a gidamu ba haka muke yi ba, ya za ayi Æ´an gida É—aya su din ga faÉ—a?".

Ammi ta ce "Kar ki damu, zaki fahimta, bi shi, kar ya sake fushi".

Rumaisa ta bi bayan takawa, suna tafe a hanya, yayi shiru fuskar nan a haÉ—e. Oganniyar ko a jikinta, zura kai ma ta yi taga, tana neman magana.

Tun da suka koma gida, kowa ya kama gabansa, har wayewar gari, ba ta sake sanya takawa a idonta ba.

Ba ta da masaniya ma a kan yana nan ko ba ya nan, dan ko É—akinsa ba ta je ba yau.

Ta gama gyaran saman benen nan, duk da yana bata wahala, saboda girman saman.
Yau har da kunna turaren wuta, tana kallon yadda falon ya yi kyau.

Ƴar siriryar muryar iman ta yi sallama, rumaisa ta ce "Anty iman".

"Ki shirya, takawa ne ya je gida, ya ce Sidi ya zo ya kai ki gida, na ce bari na biku, na gaida mama, na wuce gidan sarki na ɗorayi, na karɓo mata saƙo.

Tsalle rumaisa ta yi, ta na murna ta ce "Jirani, na shirya"

Kamar za ta tashi sama ta shirya, ta fita mota suka tafi.

Da gudu ta shiga gida, ta bankaÉ—a É—akin mama, ta rungumeta.

Mama ta ce "Kai rumaisa, babu ko sallama, wannan ai sai ki karyani"

Kuka rumaisa ta saka tana cewa "Mama ba kya so na, kin ƙi zuwa gidana, kin ce kuma kar kowa ya je".

Aliyu ne ya ga Iman a waje, ya karɓo sabir, ya shigo da shi gidan.

Iman ta ɗauko manyan ledojin da takawa ya yi sayayya, ya ce su tafi da shi, dan da shi yayi niyyar kai rumaisa, ta ɓata masa rai.

Iman suka gaisa da mama, mama ta ce "Iman tun da a kai biki, kin daina zuwar mini, maimakon tun da na baku rumaisa, ni kuma hajiya ta bani ke"

Murmushi Iman ta yi, nan da nan ƴan mazan mama, suka cika ɗakin mama, cike da murnar ganin ƙanwarsu.

Usman ya ce "Ke me yake baki ne ki ka fara ƙiba haka?"

"Me kuwa yake bani, abinci, yaya kun ga makarantar da aka saka ni? Kullum sai na hau lilo, malamanmu, har da turawa".

Aliyu ya ce "Babu a makaranta, idan ki ka faÉ—i daga lilon, ki ka fasa kai ba zaki koma ba".

Mai sunan baba ya yi sallama a falon mama, suka amsa rumaisa ta tashi da gudu ta rungume mai sunan baba.

Ya É—an yi murmushi, ya dafa kafaÉ—arta.

Iman ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau" ya amsa, ya saka hannu ya ɗauki sabir yana ɗaga shi sama.

Iman na son ɗaga kai ta kalli mai sunan baba, amma ta kasa, shi kuma a wayance yake ƙare mata kallo.

Iman ta tashi ta ce "Mama bari na tafi, zan je aiken mama, maman sabir ga kayan abincinsa nan a wannan jakar".

Mama ta ce "Iman ki bari ayi azahar ki ci abinci"

"A'a mama, na ƙoshi ni sai na kai yamma daga yanzu, ban ci abinci ba ma".

Mai sunan baba ya kalli iman ya ce "Nemi wuri ki zauna" tsit kowa ya yi yana kallon mai sunan baba, ai ko motsin kirki ba ta yi ba,ta zauna ta na wuri-wuri da ido.

Ya basar kamar bai yi komai ba, aka cigaba da hira har da shi, haka nan yau yake jin daÉ—in ganin rumaisa a gida.

Sai dai bai ji daÉ—in yadda iman ta takure sosai ba.

Har azahar iman ba ta samu umarnin tafiya da ga mai sunan baba ba, sai da aka gama girki.

Sabir sai rarrafwa yake, kwano-kwano ya ci na wannan ya ci na wancan.
Yadda rumaisa take a cikin yayyenta, ba ƙaramin burge iman yayi ba.

Sai da mai sunan baba ya fita, sannan iman ta samu ta tafi.

Rumaisa da yaya usy ta keɓe, suna magana.

"Yaya yaushe za ka zo, akwai labari fa?"

Usman ya ce "Labarin me?".

"Ni dai kawai ka zo dan girman Allah"

Ya ce "Kar ki damu, zan zo in sha Allah".

Ana idar da sallar magariba, Adam ya zo tafiya da rumaisa, amma ta ce Alla kar ta ba in da za ta" sai da aka kai ruwa rana, sannan ta ɓanɓaru daga gidan nan, suka tafi, sai dai ta sha kuka sosai da sosai, mama ta harhaɗa mata ƴan kayayyakin amfani da za ta tafi da shi.

Sam Adam bai kulata ba, har su ka je gida, dan haryanzu bai huce da abun da ta yi masa ba.

Ya ajiyeta a gida, tana jiran ta ga ya fito daga motar, ta ga ya juya ya tafi da sabir.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bata ba, hakan ya sanya ta shiga ɗakinta, ta yi ta aikin kuka.

Da ya dawo daga mayar da sabir, bai nemi ruma ba, sai da safe, shi ma dan yana tsoron, kar ya kawar da kai a kan ta, ta yi wani rashin jin.

Sai dai ya tarar tana banɗaki, ya ƙarasa gaban gadon, ya kai hannu ya ɗau littafin da yake buɗe, da fensira a kai.

"Duk wanda ya duba littafin nan, ba da izinina ba, Allah ya isa!!!"

Tsaki yayi, ya buÉ—e shafin gaba.

"Zan so ace ni marubuciya ce, da sai kun fi fahimtar abun da zan rubuta, amma gaskiya ba zan iya ba, ban sani ba ko ku gane me nake nufi, idan na zana abu mai muhimmanci da ya sameni a rayuwa, da wanda ya tsaya a zuciyata har in mutu ba zan manta ba, ina fatan ku ji irin abun da na ji, ko za a samu mafita".

Zane ne tiryan-tiryan, zane mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, daga fitarsu daga gida zuwa tasha, tare da taƙaitattaun bayanai, a gefe, na abun da ya faru". Nutsuwa ya nutsu yana bi, sai dai duk da haka ta cire wasu abubuwa masu muhimmanci.

Daga banÉ—akin ta fito, tana kokowa da towel, sai dai ta yi turus da ganinsa, saboda ba ta san ma yana gidan ba.

Kallon-kallo aka shiga yi tsakaninsa da ita, kamar ɓarawo da mai kaya.

"Meye wannan?" Yayi maganar yana nuna mata littafin.
Chapter 168 · 0% Book details