← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 174

Sashe 62

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su ruma kuwa yau kwana na huÉ—u kenan suna hannun 'yan bindiga, ba wanka ba wanki, ga azabar yunwa ruma ba ta iya cin abin da ake bata, ruwan nan É—aya idan an basu da shi take sha idan tana jin fitsari ta yi. Duk azabar kashi irin na ruma, ta matse abin ta ba ta yi.
Tun da ruma take ba ta taɓa kawo tsintar kanta a irin wannan halin ba.
Ga duka da wasu lokutan ake yi wa wasu, duk da ita babu wanda ya taɓa dukanta, amma ana dukan wasu ciki har da mata, 'yan bindiga su dake su su taka su da ƙafa.
Wani tarihi ruma ta tuna da aka taɓa basu a islamiyya, a rayuwarta tana son malaman da suke basu tarihi, dan duk abin da take zata nutsu ta saurara.
Akwai ranar da malamin yayi musu tarihin Annabi yunus da kifi ya haÉ—iye shi, ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*
Har ruma ta ce "Kai malam amma kifin da ya haÉ—iye annabi yunus, dai yayi girman duniyar nan?"

Malamin ya yi murmushi ya ce "Meyasa ki ka ce haka? Kin san girman duniya kuwa?"

"To ai malam kifin da inuwa mai kifi yake sayarwa, da wanda ake talla ko É—an tsako ba zasu iya haÉ—iya ba, amma na ji ka ce kifi ya haÉ—iye mutum"

"Kifi ne dai babba ruma, amma ba kamar girman duniya ba, kuma ba a gaya mana girman kifin ba a Alqur'ani, abin da nake son ki riƙe yanzu shi ne, falalar wannan addu'a da annabi yunus Alaihissalam ya karanta, a duk lokacin da kika shiga wani mawuyacin hali, ko ki ka shiga hannun wasu azzalumai to kema ki karanta Addu'ar da Annabi yunus Alaihissalam ya karanta *La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"

"To malam, in Allah ya yarda zan din ga yi, to wace addu'a zan yi idan na yi wa mama laifi kar ta yi mini faÉ—a ko ta saka mai sunan Baba ya sakani kama kunne?" Jik tambayar da ta yi, ya sanya 'yan ajin suka kwashe da dariya.

"A'a ai dole idan ki ka yi laifi ayi miki faɗa ko a hukunta ki, amma a duk lokacin da kike fargabar haɗuwa da wani, mugu ko maƙiyi sai ki karanta *Allahumma inni as'aluka min nuhurihim, wa'auzubika min shuriruhim*"

Ko da ruma ta tuna da wannan tarihin da malaminsu ya yi musu sai ta fara nanata "*La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin*"

Ihun wata mata ne ya sanya ruma waiwayawa taga ko dukan na ta ake, amma taga É—aya daga cikin mutanen yana jan ta tana ihu, tana a taimaka mata. Babu wanda ya tanka mata mutumin yayi cikin dajin da ita.

Ɗaya daga cikin 'yan bindigar ya ce "Ai gara hakan, tun da 'yar matsiyata ce ba za su biyan kuɗin da aka ce su karɓeta ba".

Kusan awa biyu mutumin ya dawo ba tare da ita ba.

Ta ji wasu a kusa da ita suna magana ƙasa-ƙasa "Innalillahi, ita ma sun mata fyaɗe sun kasheta" Ruma ji tayi kamar ta tambayesu meye fyaɗe, tunowa tayi lokacin da take tambayar mama meye fyaɗe su Aliyu suka din ga hantararta.

A take ta fashe da kuka, saboda yadda take kewar gida, duk suka juyo suka kalleta.

"Ke meye haka?"

"Mama" ta faÉ—a cikin kuka.

"Yi mana shiru ko in taka ruwan cikinki"

"Wallahi ba zan yi shiru ba, wayyo Allah mama yaya Aliyu yaya usy dan Allah ku zo ku É—aukeni zan mutu, wayyo Allahna" kuka take sosai kamar wadda wani iftila'in ya afkawa.

Wata mata ce ta din ga rarrashin ruma tana bata haƙuri da ƙyar ta yi shiru, ta cigaba da nanata addu'ar nan.

Mai sunan Baba kuwa yadda yaje ya tarar da gwaggo ne ya sanya jikinsa yin sanyi, ya tarar iya ma tana asibitin ita da mijinta, gwaggo sai kuka take ba ta ko cin abinci, likitoci na ta fama jininta ya sauka abu ya gagara, saboda yadda ta addabi kanta.
Tana ganin mai sunan Baba ta sake rushewa da kuka, "Dan girman Allah ku yi haƙuri, ku yafe mini umaru ban zaci abin zai kasance a haka ba, tsananin ƙaunar da nake yi wa ɗan uwana ce na mayar kanku, ban yi hakan dan baƙanta muku ba, son da nake wa ruma ya sanya na hanata, da na san haka za ta faru da ba zan ce ma azo da ita ba, ku yafe mini dan Allah" gaba ɗaya suka fashe da kuka, har su iya da su Lawisa da aka sace ruma a gabansu.

Ganin yadda dattijuwar ke cikin tashin hankali ita da iyalanta ya sanya ya ji duk jikinsa yayi sanyi, idan ya ce zai É—aga musu hankali bai yi musu adalci ba, tun da suma ba da son ransu hakan ya faru ba.

Ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon gwaggo sannan ya ce "Ki daina kuka, ko dan saboda a samu jininki ya sauka, yanzu ya ake ciki an sanar da jami'an tsaro ne ko kuwa ya ake ciki?"

Dagaci ya ce "Ka san garin namu, jami'an tsaro ba su fiye bamu agaji ba, mu da su mutanen muke yin sulhu, duk abin da muka saka jami'an tsaro wata ɓarnar suke yi mana, amma dai saboda ita rumaisan mun sanar da jami'an tsaro, amma sun ce mu jira abin da 'yan bindigar suka ce sai a sanar musu, muna nan muna jira haryanzu dai ba su yi mana aike ba".

Mai sunan Baba yayi shiru ya ma rasa abin da zai ce, ƙarshe ya yanke shawarar a kai shi wurin 'yan sandan domin ya ji meye abin yi.

Ɗanlami ya ɗauki mai sunan Baba suka tafi, sai dai daga ƙauyen da aka sace su ruma zuwa wurin 'yan sandan uwar tafiya ce mai zaman kanta, da ko menene zai samu 'yan garin ba lallai su samu ɗaukin jami'an tsaro.

Ganin girma da kwarjini da kuma ganin cewa Umar ba É—an garin bame ya sanya DPO garin tsayawa ya saurare shi.

"To ɗan uwa idan zan baka shawara ka koma gida kawai ku yi addu'a, bin bayan mutanen nan aikin sojoji ne bana 'yan sanda ba, mu mun yi iya namu ƙoƙarin, sai dai mun bar sallahun idan sun yi wata magana a sanar mana, haryanzu dai ba su ce komai ba"

Shiru kawai mai sunan Baba yayi, ba zaka ƙara sanin lamarin tsaron ƙasarmu ya taɓarɓare ba sai wani iftila'i ya afka maka.

Ba tare da samo wata mafita ba, mai sunan Baba ya kamo hanyar kano.

Gidansu ruma kuwa tamkar an yi mutuwa, ko magana mai sauti ba sa iya yi, tun da mama ta ɗan samu ƙwarin jikinta ta hau sallaya, canza alwala ce kawai take ɗagata, yunwa kuwa ko jinta ba ta yi.

Ba yadda ba su yi da mama ba a kan ta ci abinci, ta ce su ƙyaleta kawai.

Ko da ta ji sallamar mai sunan Baba, ji ta yi kamar zai ce mata ga ruma nan ya dawo mata da ita, amma ko da ya shiga ɗakinta ta kalleshi ta ganshi shikaɗai, sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta ji zuciyarta ne neman karyewa.

Ya ƙarasa gaban mama ya zauna, su Abdallah duk suka zubo masa ido, amma ya rasa ta ina zai fara yi musu bayani.
Mama ta sake É—aga kai ta kalli ta mai sunan Baba, ya girgiza mata kai ya ce "A dage a cigaba da Addu'a kawai"

Wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mama ta sauke, ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

Huzaifa ya fashe da kuka, Yasir ma ya taya shi.

Cikin dakiya mai sunan Baba ya haɗe rai ya ce "Meye haka kamar wanda ba su je islamiyya ba, ba ku yi imani da ƙaddara bane? Yanzu kuka ne ya kamace ku ko kuma addu'a?" Haka ya din ga yi musu faɗa alhalin shima da zai samu space kukan zai yi. Ya tashi fuuu ya tafi ɗakinsu, yana zuwa ya tarar da Abubakar a zaune yayi shiru ya lula duniyar tunani.

Mai sunan Baba ya zauna a kusa da shi, ya ce "Akhi na dawo?"

Banza yaya Abubakar ya yi masa bai kula shi ba.

"Na san na yi maka laifi, amma yakamata ka yi mini uzuri, ba a hayyacina nake ba, idan ka gama fushin sai mu yi magana" ya yinƙura zai tashi Abubakar ya ce "Yaya ku ka yi da ka je, an samu labarinsu?"

"Babu wani labari mai daÉ—in ji, sai ma kayan takaici, ance mu saurara idan sun kiramu sun ce mana wani abu shikenan sai mu sanar".

"Idan kuma ba su kira ba a haka zata cigaba da zama a hannunsu?"

"I have no idea" mai sunan Baba ya faÉ—a cikin damuwa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Aki meye abin yi?"

"Addu'a" ya bashi amsa a taƙaice.

Dare ya tsala, wasu daga cikin al'umma sun kwanta suna hutawa, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da iyalansu suke kwanan zaune, ciki har da mama da yaranta maza yayyen ruma gaba É—aya mama ta manta da wani abu wai bacci a wannan halin da take ciki, a zaune take tamkar an dasata tun tana iya lazimin da addu'a har ta kasa ta rasa abin da ma zata ja.
Zuciyarta sai zafi take mata, da tunanin a wani hali ruma take ciki.

Wurin baccin ruma ta kalla, da yanzu tana nan mama tana faman gyara mata kwanciya ko tashinta fitsari, da yanzu ta yi ɗai-ɗai sauro na cizonta mama tana mita tana sake gyarata, ko ta ƙaro fanka idan ta fuskanci zafi yayi mata yawa, ko ta kashe fanka ta lulluɓeta idan sanyi yayi yawa.

"Ruma ko a wani hali kike? Ko kina raye? Ko kin ci abinci? Ya in da ki ke kwance? Sanin gaibu sai Allah, ya rabbilarshil azim, dan girmanka Allah ka tsare mini 'ya ta da sauran 'ya'yan musulmi, Allah ka dawo mini da ita cikin aminci" ta ƙarasa addu'ar kuka yana kufce mata, sai a lokacin ta ɗan ji nutsuwa da ta samu hawayen idonta ya zuba.
Chapter 62 · 0% Book details