← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 174

Sashe 64

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habiba ce ta faɗo gidan su rumaisa a gigice, ta din ga kallon yayyen rumaisa da mutanen da suke zazzaune, can ta hango mama, ta ƙarasa wurinta da gudu, ta zube a kan gwiwoyinta "Mama, wai da gaske an sace ruma?"

Mama ta ƙura mata ido, amma ta kasa magana.

Maƙwabciyar su ruman ce ta ce "Eh da gaske ne, yanzu ku je ku yi ta yi mata addu'a, Allah ya bayyanata cikin aminci, ya tsareta a duk in da take".

Rushewa da kuka habiba ta yi, tana wata irin sheshsheƙar kuka, gaba ɗaya ta gigice tana wani irin kuka.

A fusace mai sunan Baba ya ce. "Dalla ku fitar mana da mai ihun nan, da wane zamu ji?"

Aliyu yayi saurin cewa "A'a ba haka yakamata ayi ba, akwai shaƙuwa a tsakanin su, bai kamata a hantareta ba"

Aliyu ya fita ya je ya samu Habiba, ta haɗa hawaye da majina tana kuka, ya tuna faɗace-faɗacensu na ƙuruciya tsakaninta da rumaisa, kullum cikin sintirin kan ƙara ake, da yadda yake zaneta ita da yayanta a kan ruma, amma yau ta tayar da hankalinta saboda ɓatan ruma.

Hannunta ya kamo ya ja ta gefe yana rarrashinta, amma babu alamar za ta yi shiru, duk jijiyon kanta sun É—aga idonta yayi jawur saboda kuka.

"Kiyi shiri kar kanki yayi ciwo, sannan addu'a zaki taya mu, Ubangiji Allah ya bayyana mana ita, ki daina kukan, mu je na raka ki gida"

"Allah ya sa kar a kasheta, Allah ya sa ta dawo gobe" ta faÉ—a tana sake fashewa da kuka.

Ƙwalla ce ta cika idon Aliyu, domin kuwa dauriya kawai suke yi, ya wayance ya ce "Amin ya Allah, dan idan kin yi salla ki din ga sakata a addu'a kin ji"
Habiba ta jinjina kai, tana cigaba da share hawaye. ya saka ta a gaba ya rakata gida, amma yanayin tashin hankalin da take ciki, zai tabbatar maka da ta kaɗu sosai da ɓatan ruma.

Hauwwaliya ma da take a zaune tana jinyar karayar da ta yi kafin tafiyar runa, ita ma haka ta burkice, dan da har tana mitar ruma ta tafi ba ta zo ta dubata ba balle su yi sallama, sai labarin an yi garkuwa da rumaisa suka ji.

Hatta malamansu ruma na makarantar islamiyya da take gallaba, gaba É—aya suka shiga damuwa, makarantar kanta kamar ana zaman makoki, saboda babu wanda bai santa ba da halinta. Ita kanta tsohuwar da take sayar da kayan yara a makarantar, da suke yawan faÉ—a da ruma sai da ta yi kuka, dan wataran idan sun yi faÉ—a wata ran suna shiryawa, dan idan ruma ta zo da abinci wataran tare suke ci, duk rashin jin ta akwai shiga rai.

Takawa yana kwance a ƙaton falonsa a kan doguwar kujera, yayi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi, abubuwa da dama sun yi masa yawa, gaba ɗaya ya rasa wace matsalar yakamata ya fara tsayawa ya nemi mafita a kai, duk matsalar da ya tunkara, sai abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa.

Wani irin zazzafan zazzaɓi ne ya kama ruma, saboda wahalar da ta sha, ga azabar cizon sauro da kuma sanyi suka haddass mata zazzaɓin.
Babu wanda yake ta tata, balle ya taimaka mata, tuni wasu aka fara bayar da kuɗin fansarsu, idan sun ga dama su bayar da mutum, idan ba su ga dama ba su karɓi kuɗin sannan su kashe mutum su ja gawar zuwa bayan wani babban dutse da yake nesa kaɗan da in da suke ajiye mutanen su yar gawar ba tare da suturta gawar ba.

Ruma na kwance ta takure tana ta rawar sanyi, ga azabar ciwon jiki, saboda dukan da ta sha, wasu mutane suka zo a kan babur, wanda aka goyo hannunsa ɗauke da ƙatuwar jaka, ta ɗaga ido dan ta ga su waye, wa za ta gani, dattijon bafullacen nan, da ta haɗu da shi har ya rakota gida a garin su Gwaggo.

Kallonsa take, amma ya kawar da kai kamar bai taɓa ganin ruma ba, ya basu jakar, shima suka bashi wata jakar ya hau babur ɗin aka bar wurin da shi. Tunani ta shiga yi a kan abubuwan da ya gaya mata, da kuma tunanin meye alaƙarsa da wannan mutanen? Kenan duk shiri ne?" Idonta ya sauka a kan lambar dake jikin jakar, sak irin lambar jakar da aka nuna mata bullet a ciki lokacin da za su zo katsina!

Guntun tsaki ta ja, a lokacin da ihun wani mutum ya dawo da ita hayyacinta, kan ta gano dalilin da ya sanya mutumin yake ihun, sai ganin abu ta yi a jikinta kamar an watso ruwa, jinin mutumin ya ɓata su an kashe shi.

Gaban ruma ne ya tsananta faÉ—uwa, ta ma rasa wani halin yakamata ta shiga, tashin hankali ko kuma fargaba, ga jikinta babu daÉ—i, ta fara fidda rai da samun mafita.

A hankali ta tashi zaune, ta ƙarasa gaban wanda ya kashe mutumin, ta kalleshi ta ce "Dan Allah nima ka kasheni"

"Saboda me zan kasheki?"

"Na gaji da zaman wurin nan, dan Allah ku kasheni nima" tayi maganar cikin magiya.

Ya kwashe da dariya ya ce "Ai ke zaki yi mana amfani,  ko zamu kasheki sai mun koya miki hankali tukuna, dan ba zaki taɓa barin hannunmu ba, an jaddada mana mu kula da ke, bakinki ba shi da linzami, ko mun karɓi kuɗin fansarki kashe ki zamu yi".

"Idan kuma baku karɓa ba fa?" Ta tambayeshi.

Ya bata amsa da "Nan ma kasheki zamu yi"

"To ku kashe ni, dan ba wanda zai baku kuÉ—in fansata, bamu da kuÉ—i talakawa ne mu"

Dariya yayi, ya cigaba da busa sigari, ya share ruma.

***
"Daddy, ina ganin kamar yadda nace ka bar komai a hannuna, komai ya kankama, kawai mu cigaba da abin da muka saka a gaba"

Senator usman wakili ya girgiza kai ya ce "Ni fa haryanzu a raina ban gama gamsuwa da shirin nan naka ba Khalifa"

Khalifa ya gyara zama ya ce "Please Daddy, ka yarda da ni, ba zan baka kunya ba kamar yadda na yi maka alƙawari zan cika, Ni dai na riga na saka rai, bana son damar ta wuce ni".

"Ni kaina ba zan so damar ta wuce mu ba Khalifa, amma yaron nan yana da taurin kai da nacin tsiya, bana tunanin zai ƙyalemu, ina matuƙar jin tsoron kar ya tona mana asiri"

Khalifa ya É—an girgiza kai ya ce "Amma daddy, sauran members É—in naku ma sun san abin da ake ciki?"

"Sun sani sarai, abin da nake tunani, akwai masu bashi goyon baya da haɗin kai a kan ya kawo ƙarshena, ba wannan ne ya fi ɗaga mini hankali ba, ina tsoron ya bankaɗo mu, dan ko last week na ji yana Abuja ku san kwanansa bakwai a can".

Cikin damuwa da tashin hankali Khalifa ya ce "To yanzu shikenan daddy, babu wani abun yi?"

Usman wakili ya kwashe da dariya ya ce "Abun yi kai, ka zuba ido kawai yaro, babu wani abu da zai iya, muna da wani shiri a ƙasa".

"Allah daddy, shirin menene?"

"Kar ka damu, idan ya tabatta za ka gani, kaima ka je ka cigaba da naka ƙoƙarin zan gani idan zaka iya zama magajina"

Khalifa ya yi murmushi ya ce "To shikenan daddy, ba ka da matsala da ni"

***
Iman ce zaune a falo, an saka mata lalle ja, tana ta kwaɓe fuska za ta yi kuka, wai ita ta gaji ammi sai mita take ta ce "Aikuwa kina tashi sai ranki ya ɓaci, ku kamar ba mata ba mutum yayi ta fama da ku a kan ku dinga ado".

"Ammi fitsari fa nake ji" tayi maganar a shagwaɓe.

"Yi a nan a wanke".
"Mhmm ammi zan yi kuka fa ya matseni".

"Ki bari na zo na sameki a wurin nan kin cire lallen nan, ki ga yadda zan yi da ke".

Jabir ne yayi sallama, Ammi ta amsa ya ƙarasa cikin falon yana kallon iman.

Kan nan nata babu É—an kwali, gashin kanta sai É—aukar ido yake ya sha mai, ta tufke shi. HaÉ—e rai ta yi ta kawar da kai, ya zauna suka gaisa da Ammi, daga nan ya hau zuba kamar an kunna shi, amma hankalinsa ba akan hirar da suke take ba, a kan iman take da ta basar kamar ba ta san da zamansa a wurin ba.
Ganin ba shi da niyyar tashi ne ya sanya Iman tashi, dama a iya hannu aka saka mata lallen, ta wuce É—akinta.

Ko da ta koma É—akin zama tayi tai shiru, tana tunanin irin balahirar da jabir zai jefata a ciki muddin ya ce yana sonta, kuma yadda yake da ammi babu abin da zai hana ammin amsawa, dan kamar É—a shima ta É—auke shi.

Baba uwani ce ta yi wa ammi ƙarya a kan zata je ta dawo, ammi ta bata izinin fita.
Tana fita ba ta tsaya ko ina ba, sai harabar gidan ta tabbatar da babu wanda ya ganta ta yi wuf ta faɗa sashin Mummy, ta ɓarauniyar hanyar da ta saba bi.

A É—aki ta iske Mummy, Mummy ta dubeta cikin mamaki ta ce "Uwani, me ki ka shigo yi nan da yammacin nan sai an ganki".

"Allah ya huci zuciyarki uwar É—akina, Allah ya baki yawan rai, wani labari ne nake tafe da shi, ban sani ba ko zai yi daidai da abin da ki ke son ji ba".

Mummy ta numfasa ta ce "Ina jinki".

"Dama wani al'amari nake ta sanyawa ido, in tabattar da shi, amma ina hasashena yana daf da zama gaske, Jabir naku na gidan Galadima mai ci a yanzu, kamar shi ne yake sinsina iman, akwai alamun yana daf da cewa yana sonta".

Wani uban tsaki Mummy ta ja, "To ni ta ina hakan ya shafeni, ni abin da na saka ki ki yi mini kenan? Ki saka mini ido ki kawo mini labari a kan abin da ya shafi ahalin gidan nan kin kawo mini maganar bare wadda ko gashi ba ta da shi a cikin gidan nan, ni ina ruwana na saka ki aikin samo mini maganin da suke yi wa wancan uban ciwon Adam amfani da shi, amma haryanzu shiru kin tsaya kawo mini shirme"
Chapter 64 · 0% Book details