← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 174

Sashe 36

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ÆŠan shiru Fauziyya ta yi, ta fara zancen zuci 'wannan ai wata damar ce ga Mummy, tabbas Khalifa wakili zai yi wa mummy amfani' da hanzari Fauziyya ta tashi ta fice daga É—akin.

***
Yau wunin ranar ruma ba a hayyacinta take ba, duk ta rasa abin da yake yi mata daÉ—i. Allah ya taimaketa mai sunan Baba bai dawo ba sai dare, tun da ya dawo ta rasa sauran nutsuwarta, tana jiran mai zai ce mata.
Sai da ya gama abin da yake, har ta kwanta ta fara bacci, ta ji ana dukan gefen katifarta.
Gabanta ne ya faÉ—i da ta yi tozali da shi, ta tashi zaune tana rarraba ido.
Da hannu yayi mata nuni da ta fito ta biyo shi.
Haka ta fito ya na gaba tana baya, zuwa tsakar gida.
Ya ja kujera ya zauna, ita kuma ta zauna a ƙasa tana sunkuyar da kai.

"Ɗago ki kalleni" ya faɗa a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

"Aure ki ke so ko?" Nan ma ba magana sai girgiza kai.

"Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura É—in, ranar juma'a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta"

Da sauri ta É—ago ta kalleshi, "Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba"

"Ƙarya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so"

"Wallahi a'a, ban san batsa nake tambaya ba"

"Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma'a za a É—aura miki aure"

"Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba"

"A ina saurayin naki yake?"

"A cikin tv nake ganinsa, É—an wrestling ne, amma ban san a ina yake ba"

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce "To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to saƙonki ya isa za ayi abin da ki ke so"

"Wallahi yaya ba haka nake nufi ba"

"To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu'a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ban sani ba"

Ya sake tsuke fuska ya ce "Ƙarya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan"

"Wallahi ban sani ba, 'yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa"

"Wace irin soyayya?"

"Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daÉ—i, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba".

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma'a É—aurin aure"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah ka yi haƙuri, manya ake yiwa aure ban da yara"

Cikin zafin rai ya ce "Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri" jiki na rawa ta tafi É—aki, tare da fashewa da kuka.
Gaban mama ta je tana kuka ta ce "Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini"

"To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaɓa miki shikenan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi"

Mama ta ce "Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya"

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ƙarshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
Da safe kuwa wasan ɓuya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, taƙi yadda su haɗu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba É—aya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta ɓuya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
Mama ta shiga banɗaki ta lallaɓa ta ɗau wayarta, ta kira Abubakar.
Yana É—agawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faÉ—i "Ruma, menene? Meyafaru?"

"Yaya, mai sunan baba ne"

"Me ya same shi, me ya yi miki?"

"Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama taƙi hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so"

Cikin rashin fahimta ya ce "Wani irin aure kuma?"

"Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi"

"Kwantar da hankalin ki 'yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa"

"A'a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai"

"To an gama, kiyi haƙuri babu mai yi miki wani aure yanzu".

Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta É—an nutsu.

***
Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuɗiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaɗa ƙafa yake a hankali.

Ta yi murmushi ta ce "Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera"

Bai kalleta ba ya ce "wace irin kujera ce gingimemiyar?"

"Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba É—aya"

Mahmud ya ce "Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi"

Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce "Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba É—aya a ka É—auka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk 'ya'yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma É—an galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta".

Mahmud ya É—an yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

"Mahmud, kar ka watsa mini ƙasa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?"

Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce "Mummy, zan je salla daga nan zan ɗan shiga gari, sai na dawo" yana gama maganar ya miƙe a hankali ya bar falon.

Fauziyya da ke laɓe take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce "Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud ƙawazucin kujerar nan, yaron nan akwai baƙin taurin kai, ɗan uwan ɗayan ne a taurin kai, tun da ƙuruciya nake kwaɗaita masa daɗin mulki, amma yaƙi ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa'idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar ƙiyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaɗayi take na ta ɗan ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu"
Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daÉ—i"

"Wani labarin kenan?"

"Khalifa Usman wakili, kin san case É—in su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu"

Mummy ta jinjina mata kai.

"To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haɗa kai, su kawo ƙarshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi"

"Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta ƙarƙashin ƙasa, amma labarin nan yayi mini daɗi sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni"

"In sha Allah Mummy, Allah ya ida nufi"

Suka yi murmushi gaba É—aya.

Takawa ne zaune a wani ƙaton falo, mai ɗauke da kayan ado na gidan sarauta, gefe gud kuma tarin litattafai ne a jere a cikin wata drower.
Ya sanya system a gaba, yana dannawa yana É—an juyi a jan kujerar da yake kai.
Jabir na zaune a kan kujera yana facing É—in sa. Jabir ya tattara nutsuwartsa a kan Adam ya ce "Takawa, kana bibiyar shafukan sada zumunta kuwa?"

"Meyafaru?"

"To ai gani na yi ka yi burus, kamar baka bibiyar meke faruwa"

"Shi ya sanya na tamabayeka, meyafaru?"

"Tone-tonen da ka ke ƙoƙarin yiwa Senator usman wakili, akwai ƙura fa sosai da sosai"

Ya ɗan ɗago ya kalli Jabir ya ce "Ai ni ƙurar nake son ta tashi, ta hana kowa nutsuwa, saboda haka nake wannan aikin"

"Duk da haka, ko dan tsaron kannka da lafiyarka, yakamata ka san yadda zaka din ga gudanar da ayyukan ka, taɓa manyan nan ba abu bane ba sauƙi ba fa"

Adam ya yi murmushi ya ce "Na fahimce ka mutumina, kar ka wani damu, ka tayani da addu'a kawai, amma dole mu yi wa ƙasarmu hidima"

Jabir ya jinjina kai ya ce "Haka ne".

***
Chapter 36 · 0% Book details