← Book details Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 174

Sashe 40

Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ke namiji ce, da zaki zauna a haka nan gaba da kanki zaki zo kina nema daga baya, ke da a da ki ka ce zaki sayo na sayarwa ki saka"

"To ai yanzu na fasa, gara kar ya fito, idan ya fito fa ba zan din ga yawo ba riga ba"

Mama ta ƙarewa ruma kallo, alamomin girma duk sun fara bayyana a jikinta, mama ta numfasa ta ce "Yanzun ma ai na hanaki yawo babu riga"

Ruma ta É—au vest É—in ta ta saka, ta ce "Mama kalli fa, kalli yadda vest É—in fa tayi mini, to wai tsayi zai cigaba da yi? Ko kuwa?"

"Nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito, sai ki ga yadda za su yi, ki dai kula da kanki, ban da wasan banza da maza ko mace, duk wanda yayi miki wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki, idan kin zo ki gaya mini, wannan wurin ba wurin wasa bane, gaba É—aya jikinki ma al'aura ne abin alkintawa ne".

"Ni mutum ya taɓani ma, ba sai na sumar da shi ba"

"Ni dai bana son rashin hankali, ki kula da kanki, zuwa gaba in ga mai yakamata ayi, idan rigar mama yakamata a saya, sai a sayo ki farawa sakawa".

Ruma ta ce "Taɓ, haka kurum a din ga yi mini kallon 'yar iska"

Mama zata yi magana, usman  yayi sallama ya shigo, ba ta amsa sallamar ba ta ce "Yaya usy, kalleni me ka gani?"

Ya ce "A ina?"

"Au dan ubanki gaya masa zaki kin fara nono, ni yau na ga ta kaina, Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Jin abin da mama ta ce ya sanya Usman ja da baya ya bar É—akin.

(Masu nema daga farko, ku din ga dubawa watpad ko arewabooks)

Ayshercool
08081012143
[01/08, 5:33 pm] JAKADIYAR AREWA:                 ƘANWAR MAZA
                

*Na Aisha Adam (Ayshercool)*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

P19

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki  glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu  shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.

P 19

"Wai ke duk yadda mutum ya so ya kwaɓeki ya nuna miki rayuwa ruma ba kya ganewa, sai ka ce rainon daji, yanzu usman ɗin zaki gayawa kin fara ƙirgar dangi, abin da ake ɓoyewa a tattala?, kai wannan yarinya kune yaran ƙarshen zamani"

"To mama ai gani na yi yayana ne, kuma bana ɓoye musu komai"

"Eh ba kya ɓoye musu komai, kuma aka ce miki ciki har da tsairaicin ki ko? Ɗauki kaya ki saka ni ki fice ki bani wuri, kan na taso kanki."

Ruma ta durƙusa ta ɗau kayanta ta saka, dama mama ce za ta aiketa.

Mama ta kalleta ta ce "Ruma wai ke komai naki butsu-butsu babu kintsi, haka ake ɗaura zanin ma, dama a dama ake ɗaura zani, kalli ƙwaurinki duk a waje kamar zaki tsallaka wuta"

Kamar ruma za ta yi kuka ta ce "Mama ni ya zan yi, ni wallahi bana son zanin nan, idan ina tafiya a hanya ji nake yi, kamar na kwance shi na riƙe a hannu, harɗe mini ƙafa yake, ni nafi son wando ko doguwar riga"

"Aikuwa kin daina saka su, dole ki koyi É—aurin zani ki na 'ya mace, matsonan na É—aura miki"

Ruma ta ƙarasa fuskar ta a haɗe, dan har ga Allah ba ta ƙaunar zani sam.

Mama ta É—aura mata sannan ta kalleta ta ce "Ga farar hoda can a kan mudubi, ki É—an shafa sannan ki saka kwalli"

"Mama farar hoda kuma kamar wata 'yar tashe, ni ki bar mini fuskata a haka kawai, bana son shafa mata komai, kwallin nan ma idan na saka zazzagowa yake fuskata ta koma kamar ta boka"

Mama ta miƙe ta danƙi hannun ruma, ta ja ta zuwa gaban mudubi ta ce "Wallahi sai kin saka kwalli, ba zaki fita da ido kamar jan nama ba" ruma har da kuka mama ta gwale idonta ta saka mata kwalli, ita ruma a rayuwarta duk wani abu ma shafe-shafen kwalliya na mata, bai dameta ba ba tayi, dan basa burgeta. Ta sha zagi wurin mama kan ta tafi aiken nan.

***
Takawa kuwa lokacin da ya shiga É—aki, kan sa ciwo yake yi masa sosai, dan bacci ma yake ji a lokacin.
Kwanciyarsa babu daÉ—ewa bacci mai nauyi ya fara É—aukarsa, sai dai baccin bai je ko ina ba ya fara jin wannan muryar a kunnensa tamkar ana yi masa raÉ—a "Sarki mai koriyar alkyabba" a hankali ya buÉ—e idonsa, ya hau dube-dube a É—akin, amma babu kowa.
Kawai sai ya ji ba ya son kwanciyar, dan haka ya tashi da sauri ya fito daga É—akin.

Iman kuwa sai da ta tsaya ta share hawayenta, sannan ta shiga sashen Ammi.

Ammi tana nan a in da suka bar ta a falo ba ta tashi ba, Iman ta ƙaraso cikin yaƙe ta ce "Ammi, kin ga Mummy ce ta kirani ta bani"

Cikin mamaki Ammi ta ce "Ke da ki ka fita kaiwa Jabir lemo, me kuma ya kai ki sashin su? Kin san bana son zuwanki in da suke"

Iman cikin dakiya da ƙoƙarin danne hawayenta ta ce "Yaya Mahmud ne ya kirani, ya ce Mummy na nemana shi ne ta bani, bari na je na gwada" ta na gama maganar ta yi gaba, dan kar Ammi ta fahimci wani abu.

Takawa na tsaye a falon, har Iman ta yi gaba, ta ji ya janyota ya dawo da ita, ya ɗan ƙura mata ido.

"Me suka yi miki?"

"Wai ni? Babu komai fa, kaya kawai ta bani"

"Me suka yi miki?" Ya kuma maimaitawa.

Tunanin ƙaryar da zata yi masa ta hau yi, amma kan ta kai ga furta komai ya daka mata tsawa, hakan ya sanya jikinta fara rawa. Cikin razani ta gaya masa abin da ya faru.

"Wuce ki tafi" ya faɗa yana nufar ƙofar fita daga falon.

Ammi ce ta tare shi ta ce "Ban lamunta ba, kar ka kuskura ka je in da suke, da gayya suka yi, ka ƙyale su kawai"

"Ammi, ba saboda Iman kawai nake wannan abun ba, na san a duk lokacin da aka taɓata, kai tsaye ka aka yiwa, Ammi ko tausayin yarinyar nan ba sa ji?"

Ita kanta Nusaiba da ke zaune tana cin abinci, al'amuran gidan sun fara isarta, tana tausayin Iman sosai da sosai.

Ammi ta ce "Na fahimce ka takawa, amma tun da ka ga ina kawar da kai, to kai ma ka dinga haɗawa da haƙuri, ka koyi kawaici ba a komai zaka yi magana ba, kar ka kula su".

Baba Uwani da ke 'yan kaye-kaye a falon ta ce "Ayi haƙuri uban gidana, ban san ka da yawan hasala ba, Allah ya huci zuciyar magajin Galadima, ayi haƙuri"

Da ƙyar Adam ya haƙura, ya nemi wuri ya zauna, ya na jin yadda zuciyarsa ke tafasa,  shi dama ba ta Mummy yake ba, Mahmud kawai yake son ya yiwa kashedi a kan rayuwarsu.

Nusaiba tsam ta miƙe, ta nufi ɗakin Iman, ta tarar da Iman ɗin zaune ta zuba uban tagumi, tana kallon kayan da aka yi amfani da damar bata, aka ci zarafinta, kayan da basu wuce ta yi kyauta da ninkin su ba.

Nusaiba ta dafata ta ce "Masoyiya"

Iman ta kalli Nusaiba ta ce "Na'am Anty Nusyna"

Kallon idon Iman Nusaiba ta yi, idonta ya nuna ta yi kuka sosai.

"Be brave iman, kiyi haƙuri, ban san yadda zan fasalta miki abin da nake ji ba, idan aka cutar da ke ba, muna sonki sosai Iman, kin san yanayin halin da ki ke ciki, dan Allah ki daina damuwa ko ɓata ranki"

Iman ta yi murmushi ta ce "Kar ki wani damu, yayata ai na ma riga na saba"
Chapter 40 · 0% Book details