Sashe 129
Kanwar Maza 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin kai ƙarata, mama ta ce sai na zo na baki haƙuri, na cire takardar da na saka miki, na cire takarda, idan ki ka kuma kai ƙarata zan yi miki abun da baki zata ba, kuma wallahi ban yafe miki ba sharrin da ki ka yi mini, wuta balbalin bala'i, idan baki nemi yafiyata ba, sai kin ga abun da Allah zai yi miki, kayan da ki ke sayarwa ma sai an daina siya" tana gama maganar ta juya ta tafi.
Da sauri ta biyo bayan rumaisa, sai dai tana zuwa ta tarar da sabuwar ta'asar da rumaisa ta ƙyanƙyasa mata a ƙofar gida, ta kankare tsakiyar ƙofar da ƙusa, duk fentin ya fita ga sauran takardar ba ta gama fita ba, gaba ɗaya ta sauya fasalin ƙofar.
"Na shiga uku ni Jamila, wace irin masifa ce wannan, fentin ƙofar da bai fi sati da yi ba ki ka dirje?".
Rumaisa ta waiwayo ta kalleta ta ce "Idan baki gaji ba, yanzu ma ki je ki kai ƙarata, zaki sha mamakin abun da zan yi miki next"
Ta shige gida tana sunkuyar da kai, mama ta kalleta a fusace ta ce "Kin bata haƙurin ko kuwa?"
"Na bata" ta amsa tana sunkuyar da kai.
Aliyu ya kalli rumaisa ya ce "Allah ya shiryeki ruma, ke ko gajiya da É—aukar magana ba kya yi, kullum ayi ta yi miki faÉ—a, daÉ—i yake yi miki ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Zo ki karɓi kuɗin nan ki sayo mini milo a kantin malam lawan, zan sha shayi bana son cin abinci" kallon yaya Aliyu ta yi, kamar tana hararsa ya ce "Ni ki ke yi wa wannan kallon, ko ba zaki ba?" Ta durƙusa ta ɗauki kuɗin, ya ce "Ki taho da manja kwalba ɗaya, na ga wanda muke da shi ya kusa ƙarewa".
Ita dai ba ta amsa masa ba, ta fice ko da ta fita a ƙofar gida ta hangi shamsiyya da mijinta, suna duba ƙofarsu da ta dirje, ba ta kula su ba ta tafi shagon.
Malam lawan mai kanti, yana ta yi mata wasa yana tsokanarta, amma ta share shi, ya auna mata manjanta, ta fito. Sai dai tana fitowa ta yi karo da wani tantirin É—an daba da ya addabi unguwarsu, wanda har kisan kai yayi, amma aka sake shi.
Ya kalli rumaisa ya ce "Ke, karɓo mini sigari a cikin shagon nan"
Tsaki ta yi, zata wuce, ya sake daka mata tsawa ya ce "Ke, na ce ki karɓo mini sigari a cikin shagon nan"
"Na yi maka kama da ƴar iska, ni ce ma zan taɓa sigari saboda wulaƙanci, to ba zan karɓo ba" ware jajayen idanunsa ya yi a kan rumaisa, a hargitse malam lawan ya ce "Yi haƙuri bari na miƙo maka".
Cikin muryar mashaya, É—an daban da ake cewa É—an kada ya ce "Ni ki ke gayawa haka?".
Fitowa ta yi zata wuce shi, ta tafi, amma ya sanya ƙafarsa ya kwashe na rumaisa, a take kuwa ta faɗi ƙasa, manjan hannunta ya fashe, ta datse goshi.
Idan da abun da rumaisa ta tsana, bai wuce ganin jini a jikinta ba, jiki na rawa ta tashi ta kalleshi, ya kalleta ya ce "Sai na tsarge hanjinki da wuƙa, na kashe banza ni zaki nemi ki zaga wata jagwal da ke"
Cikin hanzari malam lawan da sauran mutane suka fara lallaɓa ɗan kada suna bashi haƙuri, rumaisa ta shiga cikin shagon, ta dumbuzo ƙwan da ke kan teburi, ta fito ta shiga jifan ɗan kada da shi.
Rikicewa malam lawan yayi, dan yanzu aka sauke ƙwan ko lissafawa ba ayi ba, ji ta yi zuciyarta na tafasa, ta juya da gudu ta tafi gida.
Aliyu na ganinta ya ƙare mata kallo ya ce "Meye haka?" Cikin kuka ta kwashe komai ta gaya masa, nan da nan ransa ya ɓaci ya ce "Mu je" mama na banɗaki tana gyaran murya, amma Aliyu ya ja rumaisa suka yi waje.
A ƙofar shagon suka tarar da ɗan kada, har ya karɓi sigarinsa ya fara sha, malam lawan kuma yana ta masifa, yana sai ya je gidansu rumaisa an biya shi, shi kansa ɗan kada yayi alwashin sai ya kashe rumaisa, saboda wulaƙancin da ta yi masa,ta din ga jifansa da ƙwai.
Idan da abun da samarin gidan maman suka tsana, bai wuce taɓa Wannan tilon yarinyar ba, dan haka a zafafe Aliyu ya ƙarasa, yana zuwa ba tambayar ba'asi ya ci kwalar ɗan kada, ya shiga kifa masa mari.
Kokawa ta kacame, ga É—an kada a buge, dan haka ya kasa wani abun arziki, Aliyu ya din ga haÉ—a masa naushi.
Da ƙyar mutane suka shiga tsakani, ana rirriƙe ɗan kada yana rantsuwa sai ya kashe Aliyu.
Mama kuwa a gigice ta fito daga banÉ—aki, jin wanda rumaisa ta tsokano, dan babu wanda bai san yadda ya addabi unguwarsu ba.
Mama ta kira mai sunan baba a waya, ta ce masa duk abun da yake ya bari ya tafi shagon malam lawan, Aliyu ya fita ba ta san mai zai aikata ba.
Aliyu kuwa ya kalli ɗan kada ya ce "Jinina da na zuriyar gidanmu ya fi ƙarfin mutum irinka, duk wani hauka da iskanci da kake ji da shi a unguwar nan ƙyaleka aka yi, ƙanwata ta fi ƙarfin wawan mutum irinka su cutar da ita"
Malam lawan ya ce "Wai Meye haka ne Aliyu, ina nan aka sace ƙanwar ta ku me ku ka yi, sai yanzu zaku haddasa mana masifa a cikin unguwa"
"Wallahi malam lawan, duk shekarun da muka yi tare a unguwar nan, idan ka taɓa rumaisa sai na tuɓe na yi maka bugun sakwara, saceta kuma da aka yi wannan ƙaddararta ce, ba yadda muka iya"
Rumaisa ta riƙe hannun Aliyu ta ce "Yaya mu tafi gida"
Da ƙyar rumaisa ta riƙe hannunsa, suka juya suka fara tafiya, sai dai ana sakin mai kada, ya zare wuƙa ya nufi Aliyu da ita gadan-gadan yana ihu.
Ihu rumaisa ta saka ganin wuƙa tsirarata, wuƙa ba ta wasa ba an nufo yaya Aliyunta da ita, wanda ba da tabbacin ita aka nufo ko shi. Aliyu ya hankaɗeta, ya kuma riƙe mai kada suka hau kokawa ga wuƙa tsirarta.
Aliyu ya danne mai kada a ƙasa, ya ɗau wuƙar ya ce sai ya yankashi da ita a wurin.
Nan aka din ga kokowa da Aliyu, aka kasa ƙwace wuƙa.
Rumaisa ta ce "Yaya Aliyu kar ka yi kisan kai, amma dai ka yi masa dukan tsiya".
Cikin takunsa na isa da taƙama, ya din ga ture dandazon mutane, ya ƙarasa in da Aliyu yake kan mai kada ana fama da shi, ya riƙe hannun Aliyu mai wuƙar ya murɗa, ya jefar da wuƙar, sannan ya ɗago shi daga kan mai kada ya tsayar da shi a kan ƙafafuwan sa ya Kalleshi ya ce "Meya haka? Shaye-shayen kai ma ka fara ne?" Ya kalli rumaisa ya ce "Duk saboda ke ko? Sai ku wuce mu tafi ai".
Daga kwance mai kada ya ce "Na rantse da girman Allah, idan har ina yawo kana yawo a unguwar nan, sai na kasheka na kashe matsiyaciyar yarinyar nan, na ga uban waye gatanku"
Aliyu ya sake tunzura, jijiyoyin kansa suka kumbura, mai sunan baba ya kalli mai kada ya ce "Idan kana zubar da jini a unguwar nan kai da yaranka, ana tsoronku, kar ka ratso ta gidanmu, wallahi duk wanda ka zubarwa da jini in dai É—an gidanmu ne, kaima sai na zubar da naka, ka kiyaye"
Ya riƙe rigar Aliyu, hannu ɗaya ya tankaɗa ƙeyar rumaisa zuwa gida.
Mutane wasu har da shewa, abun ya burgesu, kaf unguwar nan babu gidan da suke da haÉ—in kai da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa.
A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ƙasa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba.
"Mai sunan baba, maiyafaru?"
"Kar ki damu, ba abun da ya faru"
Mama ta riƙe Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faɗa da gagararren ɗan daba saboda ɗorawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ƙyaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi haƙuri"
Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu É—inki, suka dawo gida.
Mama ta kai ƙarshen ƙulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ƴan mazan faɗa a kan biye mata wurin tare mata faɗa.
Kasancewar maƙwabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ƴan kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ƴan ƙato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wulaƙancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ƴan sanda abun da ya faru.
Mama har ta bar sallahun a rufe gida, Æ´an sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.
Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha ɗayan dare, ƴan sanda suka ƙi bayar da Aliyu, ƙarshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi iƙrarin kisan kai.
Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da É—ora zargin komai a kan rumaisa.
Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya É—an tsaya yana kallon ammi.
"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka saƙo ka kai wa rumaisa"
Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ssƙon?"
"Ban isa ba kenan?"