Sashe 93
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAYAN WATA SHIDDA
Ba zatace ga lokacin da ta taba jin dadin rayuwarta irin watanni ukun nan ba, tana gama iddarta ta fara shiga gari yanda take so, satinta daya bayan rabuwarsu da AbdulKadir ta samu ta fita da rana ita da Asma sukaje gidan suka kwashe kayan kitchen dinta, bata samu AbdulKadir a gidan ba, sai Waheedah da sallamar su kawai ta amsa.
Harda kayan abincin da suke kitchen din kaf ta kwashe tana tafiya dasu gida.
Haka tace ma Mama cikin kudin kayan kitchen dinta ne data siyar.
Da su ta siyi atamfofi da leshi, ta rage sauran da a kayan kwalam da maqulashe ta karar dasu.
Kwalliya takeyi ta kece raini, samari ne suke mata layi kala-kala suna mata hadarin kudi, sai yanzun tasan rabuwa da AbdulKadir din alkhairinta ne, sakayau take jinta, a watanta na biyu bayan tagama idda ne ta hadu da Saminu.
Matashin saurayin da bazai shige shekara talatin da biyu ba, daga yanayin shi tasan bai taba aure ba kafin ya tabbatar mata da hakan, da wuri ta sanar dashi cewar ita aurenta biyu, nuna mata yayi duk wannan ba matsala bane ba.
Dogone sosai mai kirar karfi, kusan da kadan zaifi AbdulKadir, sai dai nesa ba kusa ba, ba zaka hada kyawun Saminu da AbdulKadir ba.
Saminu ya tsere mishi tun daga hasken fata da dogon hanci, wayewa kawai AbdulKadir zai nuna mishi.
Da alamu Saminu baiyi karatun boko ba, dan turancin shi irin wanda akan tsinta a hanya ne.
Yace mata dai shi dan kasuwa ne.
Yana siyar da atamfofi da leshi da suke kawowa daga Legas zuwa nan garin Kano.
Rashin wayewar shi bai dami Nuriyya ba, saboda yana sakar mata kudi kamar baisan ciwon su ba, ga siyayya yana mata kaca-kaca.
Mafarkinta ne yake shirin cika, dan a sati Saminu na iya zuwa da mota kala biyu, watan su daya cif da haduwa ta nuna tana so ya fito, yace mata babu wata matsalar komai.
Wannan karin Baba da kanshi ya fadama Wakilan Saminu cewar Nuriyya ta taba aure har sau biyu.
Sukace duk Saminu ya sanar dasu.
Ko sadaki dubu hamsin suka bayar.
Kallo daya zakaiwa Nuriyya kaga tsantsar farin cikin dake fuskarta, ga sabuwar waya kirar infinix dal a kwali Saminu ya kawo mata.
Yar walima tayi a gidansu Asma ta tara kawayenta aka ralle, tunda dubu dari Saminu ya bata dan yin hakan.
Da kan shi yai mata maganar tarewa ta nuna mishi ita bata da wani kayan daki ba kuma tada kudin yi.
Zuwa yayi da mota ya dauke su ita da Asma sukaje wani tsantsareren gida dakuna shidda, da komai da komai a ciki, yace ta duba idan yai mata.
Ranar da suka dawo har Mama sai da ta kula da rawae kafar da Nuriyyar takeyi
"Ki dai bi komai a hankali Nuriyya..."
Cewar Mama, farin cikin da Nuriyya take ciki yasa ta fadin
"In shaa Allah.
Nagode"
Ta wuce daki.
A kwana biyun sosai ta matsama Saminu kan maganar tarewa, yace karta damu zaizo har gida ya dauketa ranar wata alhamis da tayi juyin waina gardamammiya da rayuwarta.
Har gida Saminu ya shiga suka gaisa da su Mama, yayi musu siyayya sosai ta kayan ciye-ciye, ya kuma kara yi musu godiya tukunna ya fita waje yana jiran Nuriyya.
Ta dauki jakarta da mayafinta a kafada Mama ta shigo dakin
"Nuriyya kinga kin samu mijin da alamu suka nuna yana sonki, dan Allah kibi rayuwar nan a hankali, kiyi hakuri da duk yanda zata zo miki..."
Kai Nuriyya take jinjina ma duk wata nasiha da Mama tayi mata badan ta jita ba, dan hankalinta nakan alkawurran da Saminu yayi mata, na cewar hajjin shekarar da ita za'ayi ta.
A satin zasuje suyi hoto, a fara maganar biyan kudi.
Tun a mota take fadin
"Kasan a jirgi kawai nake hango ni"
Dan ta gama fada ma su Asma da duk wasu kawayenta maganar zuwan su Hajji, group dinsu ma yanzun Hajiya Nuri suke kiranta, sunan da yake kara sawa kanta ya kumbura.
Tunda suka hau titin unguwar su take kula da cikin kurna yake nausawa maimakon Rijiyar zaki inda gidan daya kaisu ita da Asma yake.
Ganin suna barin cikin kurna suna nufar dan dinshe, unguwar da tafi tsana duk a cikin karamar hukumar dala yasata fadin
"Naga munayin dan dinshe"
Kai Saminu ya jinjina mata, dan shi din bamai yawan magana bane ta kula
"Zan amshi sakone"
Ya amsa ta a takaice, numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana sake gyara zama cikin motar.
Haka har suka karasa cikin dan dinshe, kusan karshen unguwar dan gidan da yayi parking ne karshe a unguwar sai wani gidan bulo daga gefe, unguwar shiru kamar anyi sata.
Taso ta zauna a cikin motar yace mata ta fito su shiga tare, batason duk wani abu da zai bata mishi rai a daren su na farko yau, shisa ta fito, tadai cika da mamaki ganin ya zaro mukulli a aljihun shi yana bude gidan, bin bayan shi tayi.
Karamin gidane dan karami, da dakuna guda biyu, bandaki sai dan kitchen dako kofa babu, sai karamin risho a ciki da yar tukunya daya tabbatar mata da cewar kitchen ne.
"Gidan fa babu kowa...
Wanne irin sako zaka karba?"
Nuriyya ta fadi tana kallon shi, ko kulata baiyi ba ya tura dakin da yake a share tas, da katifa matsakaiciya an gyarata itama, sai kamshin kafur yake da alamar yanayin damuna yasa aka saka saboda warin raba.
Zuciyarta taji ta kasa natsuwa da ta shiga dakin
"Ni dai ka dauki sakon da zaka dauka mu wuce"
Wani irin kallo Saminu yai mata da yasa hantar cikinta kadawa
"Babu sakon da zan dauka"
Ya karasa maganar yana samun waje gefen katifar ya zauna.
"Ki shigo malama kar sauro ya cika mana daki"
Cike da rashin fahimta Nuriyya take kallon shi
"Ki shigo sai in miki bayani"
Zuwa lokacin kafafuwanta har rawa suke, shiga dakin tayi tana kasa zama, dan zuciyarta dokawa take tayi da wani irin karfi da yake saka jikinta bari
"Wata hudu da suka wuce na shiga unguwarku wajen wani abokina muna zaune majalissa wajen mai rake kika zo kika wuce.
Kina gifta mu naji kin kwantamun har kasan raina, lokacin na furta hakan.
Ban bar majalissar ba saida naji kaf labarinki, aurenki da Anas da kuma mijin kawarki da kika aure.
Cikin kasa da awanni biyu suka fadamun labarin da nasan kinfi karfina, saboda banida kudin da zaki gani ki saurareni"
Saminu ya karasa maganar yana mata wani murmushi da yasa tajin kamar an watsa mata ruwan kankara
"Sunana Saminu da gaske, kuma kamar yanda na fada miki dan asalin kauyen dan busai dake nan jahar Kano.
Abinda baki sani ba shine ni bani da wasu kudi, mahaifinki yasan sana'ata ni direban babban mota ne, kudin duk da nayi miki hidima dasu, kudin da kikai tunanin ina dasu tsintar su nayi.
Sai bayan na tsince sune tunanin inzo miki a matsayin attajirin me kudi yazo mun saboda kin manne mun a zuciya.
Ko kadan bakiyi wahalar siyewa ba saboda abin duniya ne a gabanki, nan dinne gidan dana samu na gina a cikin sana'ar da nake...
Kar kuma kiyi tunanin akwai wani tashin hankali da zakiyi da zaisa in sakeki saboda wallahi nasha banban da duk wasu maza da kika aura a baya, babu kalar tashancin da banci karo dashi ba, banje wajenki ba sai da nayi shirin zama dake a duk yanda kika so mu zauna"
Mayafinta Nuriyya ta sauke daga kafada tana wulwula shi cikin son fifita fuskarta da iska ta daina kai mata, bata taba sanin menene tashin hankali ba sai yau.
Tunda Saminu ya fara magana take jin wasu notika na kwancewa a jikinta, cigaba yai da fadin
"Duk motocin da kikaga ina zuwa wajenki dasu cikin ragowar kudin da suka ragemun nake arowa, gidan dana kaiku na ubangidan wani abokin wasana ne da yake gadi na roke shi alfarma naje daku kika gani, naso inji babu dadi na yaudararki da nayi, sai naga mu dukan mu badan Allah muka gina dangantakar ba, ni dan son mallakarki, ke kuma dan son abinda nake dashi, zaki iya taimaka mun mu gyara zaman mu daga yau mu nemi yafiyar Allah"
Wannan karin dariya Nuriyya tayi da bata da alaka da nishadi, tana son wani yazo ya tasheta daga wannan mugun mafarki, dan a mugun mafarkine kawai zata auri direba, direban ma na babbar mota.
"Da gaske ina kasuwanci, tunda idan nakai timatiri legas ina dauko gawayi in dawo dashi nan in siyar"
Da kuka dariyar ta kwace mata, kafin tasa hannu tana goge hawayen ta ajiye mayafinta a kasa ta kalli Saminu tana fadin
"Wallahi karyar iskanci kakeyi, ni zaka yaudara?
Saminu ni zaka yaudara?
Sakina zakayi yanzun nan dan bazan taba zama da kai ba.
Kaga na maka kalar matar da zata zauna a wannan akurkin kajin?"
Dariya Saminu yayi
"Saki?
Ai wallahi gara ki fara sakawa a zuciyarki mutuwa ce abinda zata gifta ta rabani da aurenki"
Mayafinta Nuriyya ta tsugunna ta dauka tana jin yanda duniyar take jujjuya mata, shirin fita takeyi daga dakin, cikin zafin nama Saminu ya taso yana riko hannunta, juyowa tayi tana daga dayan da niyar sharara mishi marin da zaisa ya saketa a daren nan ta koma inda ta fito ya rike hannun yana hadawa da dayan yai mata rikon da takeji kamar zai karyata tukunna yasa dayan hannun nashi ya sharara mata wani irin mari da yasa ta jin wani gishiri-gishiri a cikin bakinta
"Na gaya miki duk kalar zaman da kike so muyi dake shi zamuyi, idan mutunci kike so zamu lallaba rayuwar mu, idan rashin mutunci kike so zan zauna dake dashi"
Kiciniyar kwacewa take tana auna mishi kalar zagin da in sun kwana a tafa yakanji karuwai nayiwa masu neman su.
Shisa yasha alwashin kudin goron da akewa direbobi nabin mata bazai zamana cikin su ba, koba dan komai ba yana tsoron lahirar shi, duk tangaririya da wahalar rayuwar daya sha da saken daya samu sanadin mutuwar iyaye bai saka shi ya lalace ba.
Iskanci zabine a kowanne yanayi duk da yakan zo da kaddara, amman akwai zabi a cikin al'amuran rayuwa.