← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 94

Sashe 55

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batasan me AbdulKadir yagani a jikin Waheedah ba, akan ce kana kiba inka haihu, amman tana nan yanda take, kamar sillen kara, in zasu jera ita da Waheedah, babu abinda Waheedah take dashi da za nuna mata.

Tana da kyau tasani, daga na fuska harna jiki, batasan abinda Waheedah din take dashi har haka ba.

Ko me tayiwa AbdulKadir din harya aureta.

"Yanzun haka mayyar ita tace tana son shi"
Ta fadi a fili, zuciyarta kuma na saka mata, indai wannan hanyar Waheedah tabi, to itama gata akai, amman babu alamar nasara.

Saqe-saqe take a zuciyarta.

Kafin taji wayarta da ta saka a silent tana zuuuu alamar kira ya shigo.

Karamin tsaki taja, dan batasan kowanne maye bane cikin dare, tana dubawa jikinta taji har kyarma yake, ga zuciyarta na wani irin dokawa, ganin sunan AbdulKadir din da tayi editing zuwa
'Masoyi
Na fitowa kiri-kiri, tunda tace tana son shi ta sake sunan, haka kuma takan kira shi dashi a duk sakonninta, bai taba kiranta ba, ita dinma inta kira shi ba dagawa yake ba.

Jikinta rawa yake sosai lokacin da ta kara wayar a kunnenta
"Masoyi..."
Ta tsinci kanta da fadi, muryarta a karye, tanajin shige da ficen numfashin shi ta cikin wayar, yafi mintina biyu baice komai ba, badan numfashin shi da takeji da shuu kamar alamun yana cikin mota ba, zata iya rantsewa ya kashe wayar.

Kafin yace
"Sai da safe..."
Yana kashewa din batare da ta samu damar amsa shi ba, murmushi tayi tana sauke wayar ta rungume a kirjinta, wani irin nishadi takeji yana ratsata ta ko ina.

Ko ba komai yau ya kirata da kanshi, hakan kawai nasara ne.

Da tunanin shi fal ranta bacci ya kwasheta.

Bata gane cikin Fajr kamar sadakar shi aka bata ba sai yanzun da take dauke da cikinta na biyu, da tun a satika kadan da shigarshi ya soma wasan kura da rayuwarta.

Daga zazzabi zuwa amai tun kafin asubahi.

Duk wani labari da taji masu ciki na bayarwa lokacin da take da cikin Fajr ne ya hadu waje daya yake wujijjigata.

Bata son jin kamshin duk wani abinci mai miya.

Nabila ta kira ta kwashe mata duk wani kayan miya da yake cikin gidan ta tafi dashi.

Abinci sai dai ta saka mai da yaji, man ma na ja, idan tasha bakin ruwa sai tayi kamar zata amayar da kayan cikinta.

Citta ta gyara ta dandaqa da kanumfari ta saka a fridge, duk in zata sha ruwa sai ta dan tsiyaya a ciki dan ya canza launi.

Bata taba ganin tashin hankalin irin na watanni ukun nan ba, ga cikin harya fito mata, kamar mai yan biyu.

Hankalin AbdulKadir yaki kwanciya, duk yanda take tabbatar mishi da lafiyarta kalau, laulayine kawai, kuma ance zai mata sauqi in cikin yadan kara girma.

Amman duk wani dan lokaci da zai samu cikin kiranta yake.

Har dariya takan mishi idan yana mata wasu tambayoyin
"Kanki na ciwo?

Kina jin zazzabi, bani lamba daga 1 zuwa 10 ya kikeji?"
Wani lokacin har da fushin shi inta ce mishi ita lafiyar ta kalau, ya sha kiran Hajja inyaji muryarta can kasa yasa tazo, kunya yakan bata kamar ta nutse a kasa.

Akwai randa suna cikin waya amai ya taso mata, ta ajiye wayar, ashe yanata magana, sai da tagama aman ta dawo hayyacinta ta kira shi.

"Wahee ban samu Hajja ba, na kira Abba amman, yace za'a turo wani"
Babu kalar salatin da batayi ba, balbaleta da fadan shi yayi, me yasa bazai kira Abba ba, ai ba abin kunya bane ba, su da zasuje da baby gidan harma su bashi.

Meye dan yasan babyn na hanya.

Shiru tayi harya gama ya kashe kiran, tayi murmushi kawai.

Rigimar shi babu kalar da bata sani ba, akwai kalar da ta kasa sabawa da itane har yanzun kawai.

Nabila tazo tayi mata su shara da mopping, anan ta kwana, da safe ma sai da ta soya mata dankali da kwai tasa a kula, ta dafa ruwan zafi, har taliyar Hausa da Waheedah din tace tana so a bayar ai mata saida Nabila ta dafa mata, tukunna ta wuce gida.

Da Fajr ta wuce, itama ta samu sauki.

Tana da tabbacin dai AbdulKadir zaije ya dauko shi inya iso.

Ta ga ma har goma da rabi, wayar shi take kira taji yana ina, in yabi motar dare da sassafe yake isowa.

Taji sallamar shi, sanyi takeji saboda zazzabin da take ta fama dashi tunda dare, da ruwa mai zafi tayi wanka, amman duk da haka sanyi takeji.

Wando ne a jikinta dogo, baqi, ta saka tshirt, ta dauki rigar sanyin AbdulKadir din ruwan toka mai hade da hula ta saka.

Kalba ce manya a kanta da Nabila ta taimaka tayi mata, ko dankwali bata saka ba, hular rigar sanyi taja ta saka a kanta.

Kafin ya bude kofar ta sakko daga kan gadon, a tsakiyar dakin suka hadu tana rungume shi, ya zagaya hannuwan shi a bayanta ya lumshe idanuwan shi, kamshin turarukanta sun canza mishi
"Sannu da zuwa..."
Ta fadi tana sake makalewa a jikin shi, wata irin kewar shi take ji tana danneta duk da yana tsaye a gabanta, tana jin dumin shi a jikinta
"Turarenki ya canza mun"
AbdulKadir yace maimakon ya amsa mata sannun da tayi mishi.

Murmushi tayi, batasan kalar sabon da yayi da komai nata ba, da kuma kalar kula da yakeyi, ko a whatsapp suke chatting in yaga tana amsa shi kayi dai-dai sai ya fara tambaya me yai mata bata mishi hira.

Bayaso yaga canji a tare da ita kowanne iri ne.

Murmushi tayi
"Akwai kamshin da bana so a wancen, shisa..."
Dagota yayi daga jikin shi yana saka dayan hannun shi ya taba kuncinta dashi zuwa wuyanta.

"Zazzabi kike ko?

Ina hijab dinki muje asibiti"
Kai take girgiza mishi tun kafin ya karasa maganar
"Nasha paracetamol ai, zai tafi, yana mun haka wani lokacin"
Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi
"Waheedah..."
Ya kira cike da alamar tambaya da rashin yarda da ita, yana kara taba jikinta, dariya tayi tana kama hannun shi ta sauke daga wuyanta
"Da gaske"
Numfashi yaja yana fitarwa
"Nikam cikin Fajr ba haka yayi bafa, baki sha wahala da yawa ba..."
Sanin halin shi yasa ta canza maganar da fadin
"Abinci ko zaka fara watsa ruwa?"
Dan jim yayi, dan yanajin yunwa sosai.

Amman yafi so yaci a nutse, jakar daya dawo da itama a falo kan kujera ya ajiye.

Tare suka shiga bandakin, ya korota karta taba ruwa tunda yaganta da rigar sanyi, ta mishi wani irin fayau, kamar cikin yasa ta kara haske sosai.

Wanka yayi ya fito, kaya ma shiya dauko da kan shi, dan tana gefen gado ta zauna.

Tare suka fita zuwa kitchen din, ya dauko mata kula da plate.

Shayin shiya hada a kitchen ya fito dashi, ita ta zuba taliyarta da manja, tunda babu abinda ta iya sakama cikinta.

Zama sukayi, AbdulKadir ya dan fara shan shayin da yake tunanin kamar ya mishi yawa ma, gashi sukarin baiji ba, Waheedah ita data zuba inya sha sai yaji yayi dai-dai.

"Shayin salaf..."
Ya fadi yana kara kurba
"Baka zuba sukari ba?"
Kankance mata idanuwa yayi
"Na zuba"
Taliyarta take cakudawa
"Kaje ka kara..."
Kafada ya makale mata, dan a gajiye yakejin shi, kuma zaman ya mishi dadi.

Tashi tayi yaba binta da ido, ta dauko kwalin sikarin ta ajiye a gaban shi, kallonta ya sakeyi
"Guda nawa zan saka"
Dayan hannunta da babu manja ta saka ta dibi guda uku ta jefa mishi a kofin ta cakuda, dan gara mata Fajr da tabarar AbdulKadir lokutta da dama, sai da ya dauka ya kurba, tace mishi
"Yayi?"
Kai ya jinjina mata yana soma cin dankalin
"Ni baki bani taliyar ba Waheedah..."
Ta bakinta ta hadiye tukunna ta amsa shi
"Sadauki taliyar hausa ce...

Kwanaki dana dafa cakayi mun wacce irin taliya ce wannan?"
Shayin shi ya sake kurba
"Amman bance banaci ba ai, kuma wannan ba irin waccen bace, da manja fa, inata kallon ki tun dazun, baki bani ba.

Kuma raina ya biya..."
Murmushi tayi, ta tsame hannunta daga taliyar tana mika mishi kwanon, ita kenan Nabila ta dafa mata, dan bata dauka zaici ba, mikewa tayi ta wanko hannunta a kitchen ta dawo.

Ta same shi ya cinye taliyar yana fadin
"Ki kara dafa mana anjima....

Irin wannan"
Kai ta jinjina mishi kawai, shiya kwashe kwanonin ya dawo.

"Bacci nake ji"
Ya karasa maganar yana mika mata hannun shi, ta kama tana mikewa.

Ta riga tasan ko batajin bacci saita kwanta, rigimar AbdulKadir bata karewa, ko da Fajr na jariri haka ta dinga fama dasu biyun.

Sai dai ta saka Fajr daga gefenta, AbdulKadir na bayanta.

Dakinta suka wuce, duk da yana da nashi bangaren da bata ga amfanin shi ba, sai ta kwana hudu ma bata taka sashin ba, takan shiga ta share inyai kura, haka ya siyi gidan bangare biyu, dayan bangaren bai kai nan inda take girma ba, amman da falo da bedroom da bandaki, harda kitchen.

Nata kuma bedroom biyune, kitchen harda store, kuma akwai bandakin baki daban ta cikin falon nata.

Har kujeru da komai AbdulKadir ya zuba a dayan bangaren, kitchen dinne kawai babu komai, wasu lokuttan in yana nan, takan ja shi su shiga, su zauna, kafin aljanu su samu wajen labewa.

Ko minti sha biyar ba suyi da kwanciya ba, bacci ya dauke shi, itama gyara kwanciyar ta tayi tana rufe nata idanuwan tana jiran bacci yai gaba da ita.

Bacci suka wuni yi, da sukai azahar ma komawa sukai har la'asar, garama AbdulKadir ace ramuwar bacci yake.

Ita kam cikinne yake sakata wani irin bacci kamar kaza.

Taliyar ta dafa musu suka ci.

Suka zauna suna kallon wani indiyan film, gabaki daya AbdulKadir ya langabe mata, duk da zazzabin da take ji ya sauka, jikinta babu karfin kirki.

Amman ya tattara kafafuwan shi ya dora kan kujerar dan ya kwanta a jikinta.

"Ka karyani Sadauki...

Sai ka huta kaga"
Waheedah ta fadi jin yanda ya sake naniqe mata.

Sake gyarawa yayi bai kulata ba, tunanin da bashi da daliline bayason yi.

Nuriyya kuma ta addabi rayuwar shi, tunda ya shigo gidan ya kashe wayarshi ya ajiye.

Yasan yana kunnawa zaici karo da sakkoninta.
Chapter 55 · 0% Book details