← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 94

Sashe 44

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba'a san matar soja da rauni ba"
Ya fadi yana mata murmushi, zuciyarshi yake jin tayi wani shiru, hawayenta sun tsaya mishi a makoshi, da gaske Yassar yake, tana son shi, a fuskarta yake karantar hakan, yana mamakin yanda ya dauke shi tsayin lokaci baiga hakan ba.

Har a kasusuwan shi yake jin aurenta ne zabi mafi girma da ya tabayi a rayuwar shi.

"Matar Sadauki"
Tai maganar tana saka idanuwanta cikin nashi.

Kai ya jinjina mata yana maimaita
"Matar Sadauki..."
Sunan na zauna mishi a duka jikin shi, wannan karin ita tai dariya.

Zatai kewar shi tasani, amman ya bata abinda zai riketa harya dawo.

"Allah ya tsare maka hanya ya sauke ka lafiya"
Amsawa yayi da
"Amin..."
Yana dumtsa hannunta dake cikin nashi kafin ya saki, muryarshi can kasan makoshi yace
"Zan kiraki..."
Kai ta daga mishi, tukunna ya juya, agogon shi dake hannunta ta dumtsa tana sauke numfashi mai nauyin gaske, idanuwanta akan shi harya bace ma ganinta...!!!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#BatulMamman*
*#AnaTare*[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Tunda aka fara kamun hankalinta nakan wayarta da Amatullah ta baro mata a gida.

Mutuwa tayi, hakan ya sakata bata dan tasa mata a caji.

Ba tunanin gidan da yake shakare da mutane ko za'a sace mata waya takeyi ba.

Amatullah ta tabbatar mata da ta rufe dakin da mukulli ta kuma taho dashi.

A'a, duk inda karfe bakwai tayi tasan AbdulKadir zai kirata, a watannin shiddan nan da suka wuce mata kamar kiftawar idanuwa, karfe bakwai ya zama lokacin wayarsu.

Duk da tun jiya take baza idanuwa taga ta inda zai bullo, amman shiru, kuma ko da ya kirata jiya saita tsinci kanta da jin nauyin tambayarshi yaushe zaizo din.

Gashi kamun babu maza, matane kawai, batai tunanin zai kaisu har lokacin ba, satin bikin ma jinshi takeyi kamar a mafarki.

Itace za'ai bikinta wai.

Tunda satin bikin ya kama take baza ido taga ta inda Nuriyya zata bullo, amman sai text tayi mata cewar an kwantar da ita asibiti saboda haka ba zata samu damar zuwa ba.

Ta kikkirata yafi a kirga tana mata ya jiki, sosai taso zuwa har asibitin dan ta dubata amman bata samu dama ba.

Ta dauka taji jiki lokacin bikin Nuriyya din, sai yanzun ne tasan yanda ake jin jiki da nata bikin yazo, abinci ma duk yinin ranar bata samu ta saka shi a cikinta ba.

Har wani haske take gani yana gilmawa ta cikin idanuwanta duk idan ta mike saboda yunwar da take ji.

Jiya da sukai waya da AbdulKadir yayi mata fadanshi kaman zai ari baki da tace mishi bataci komai ba, kanta na mata ciwo.

Yanzun ma tana jin alamar ciwon kai na barazar yi mata sallama, cikinta da taji yayi karar yunwa ta dafe tana gyara zamanta kan kujerar da take zaune.

"Ni fa nagaji wallahi, bakiji yunwar da nakeji ba"
Cewar Zahra da take zaune kusa da ita, tayi matuqar kyau cikin alkyabbar da ta dora kan kayan jikinta da iri dayace data Waheedah din
"Nifa duk yau babu abinda yaje cikina banda ruwan shayi da safe"
Juyowa Zahra tayi tana kallon Waheedah da tambayar
"Kina aikin me?"
Langabar dakai tayi, Zahra din naganin tayi mata wani irin kyau da kwalliyar da akai mata marar hayaniya.

Jambakin ya zauna kan labbanta kaman dasu aka halicce shi
"Babu wanda yabani abinci fa...

Anty Hafsah ce ta tambaya ko naci, to tace bari ta kawomun kuma ta shiga wata hidimar inajin ta manta..."
Tabe baki Zahra
"Zubawa nayi na shige daki na zauna naci abuna...ulcer ba zata kamani ranar bikina ba"
Dariya Waheedah tayi sosai tana sa Zahra din yin dariya itama.

Haka sukaci gaba da hira da take tsayawa iya kunnuwansu.

Tsaye yake bakin wajen, jikin shi sanye da shadda ruwan toka mai cizawa sai hula da tayi matukar dacewa da shaddar jikin nashi.

Ya kankance ma Anty Ramatu kanwar Hajja idanuwan shi da suke cike da rikici
"Bansan sau nawa zan gaya maka babu maza ba AbdulKadir, duk da yawancin mutanen da suke wajen yan uwane...me ma kazoyi wajen kamu?"
Ta sake mishi tambayar, dan itama wata makociyarsu da tazo matane zata tafi, ta rakota bakin kofar wajen ta samu AbdulKadir din ya cakumo rigar daya daga cikin masu gadin wajen yana shirin hadashi da bango saboda yace mishi maza basa shiga.

"Me zanyi a wajen kamu.

Waheedah zaki kiramun ko ki matsa in shiga in kirata da kaina"
Kai Anty Ramatu ta girgiza mishi
"Muma yanzun zamu taho...

Addu'a kawai za'ayi...

Ka wuce gida gamu nan"
Kallon da AbdulKadir yake mata ya fara tabbatar mata da cewar babu inda zashi kafin ya bude baki yana tabbatar mata ta hanyar fadin
"Ki kiramun Waheedah..."
Yanajin hakurin shi na gab da karewa, bayason fadin wata magana da zatace ya mata rashin kunya.

Tun karfe wajen biyar ya iso garin Kano, kiran wayarta yayi yajita a kashe.

Duk da yana hanya ma bai hanashi bude WhatsApp dinshi ko zaiga sakonta ba, amman shiru, yinin ranar ko dan text bai samu ba.

Kiris ya kira Yassar ya rokeshi yake ya duba mishi ko tana lafiya, ko ciwon kan ne ya hanata bude wayar.

Da damuwarta ya sauka garin Kano.

Ake fada mishi suna wajen kamu.

Ya jira har lokacin daya saba kiranta dan yana da tabbacin ko da bai kirata ba ita zata kirashi, amman wayarta a kashe.

Bayason ya zauna yana wani tunani, dan ba abokin yinshi bane, shisa yasa daya daga cikin sababbin kayanshi da Yassar ya nuna mishi, yaso su fita amman yaki, baibi takanshi ba suka wuce koma ina ne zasu din, dan shi bai tambaya ba, bayason hayaniyar.

Waheedah yake jin gani yaji dalilin da yasaka rufe waya bayan tasan zai kirata.

Amman Anty Ramatu nason bata mishi rai.

Bada ita yakejin yin fada ba, da Waheedah ne.

Yana kallonta ta jinjina mishi kai
"To kayi hakuri dan Allah ka jira, ayi addu'ar inajin ma an fara saimu fito gabaki daya..."
Ganin har lokacin idanuwan shi na kafe a kanta yasa ta kara fadin
"Kaji...

Yanzun zamu fito"
Kai ya jinjina ma Anty Ramatun a hankali yana juyawa ya koma jikin wata mota ya tsaya saitin kofar wajen.

Dan shi a motar Yassar yazo tunda bashida tashi har lokacin.

Kuma baiyi parking dinta a kurkusa ba, kasancewar akwai motoci da yawa a wajen.

Baifi mintina goma a wajen ba ya fara ganin mutane na firfitowa, hakan yasaka shi raba bayanshi da jikin motar da yake jingine yana tsayawa tare da duba Waheedah da idanuwanshi a cikin taron mutanen.

Anty Ramatu ya hango rike da hannunta, duk da baya ganin fuskarta da take sadde a kasa, ga hular alkyabbar jikinta ta kara boye mishi fuskarta.

Yana ganin yanayin tafiyarta, har suka karaso inda yake din
"Gata nan mintina biyar, kuyi maganar da zakuyi tafiya zamuyi"
Dakuna ma Anty Ramatu fuska yayi
"Zan taho da ita gida.

Nazo da mota"
Kai ta girgiza ma AbdulKadir din, bada ita za'ayi wannan rashin hankalin ba
"Kuyi maganar ku, ko kabari muje gida sai kayi maganar a nutse.

Amman yanda mukazo tare haka zamu koma tare da ita"
Ta karasa maganar tana sauke numfashi.

Cikin bacin rai yake kallon Anty Ramatu
"Meyasa ba zamu tafi gida tare da ita ba?"
Kallon shi take itama
"Haka kawai..."
Kai AbdulKadir ya jinjina, koda zaiji maganar da aka fada mishi yana son ayita da hujjar da zata gamsar dashi, kaf gidansu Yassar ne kawai yakan sakashi yin abu wasu lokuttan batare da ya bashi kwakwaran dalili ba kuma yayi.

Amman ko Abba yana fada mishi dalili, da Anty Ramatu tabashi wani dalili mai karfi zai iya juyawa ya tafi in yaso saisu hadu a gida.

Amman haka kawai ba zata fara gaya mishi abinda zaiyi ba.

Hannun shi ya mika da nufin kamo na Waheedah yajata subar wajen, Anty Ramatu ta tare da fadin
"Ai ba'a daura ba tukunna, Malam AbdulKadir..."
Bude baki yayi zai gaya mata maganar da take yawo cikin kanshi Anty Talatu ta karaso wajen tana riganshi da fadin
"Hajiya Ramatu ke aketa nema.

Ashe kina nan...

AbdulKadir..."
Anty Talatu ta karasa maganar tana maida hankalinta kan AbdulKadir da har lokacin Anty Ramatu yake kallo
"Ai kamun namu babu maza..."
Kallonta Anty Ramatu tayi
"Na fada mishi fa, wai yanzun tare yake so su koma gida da Waheedah....

Nace yaje zamu taho gidan..."
Murmushi Anty Talatu tayi, dan ita tasan halin shi sarai, Anty Ramatun ma da alamu ba sosai suke haduwa da AbdulKadir din ba
"Ki fada mata da Waheedah zan koma gida...

Banaso inyi magana tace na mata rashin kunya"
AbdulKadir ya fadi yana kallon Anty Talatu.

Kai kawai ta jinjina mishi tana fadin
"Allah ya tsare...muma gidan mukayo"
Ta karasa maganar tana janyo hannun Anty Ramatu da take kallon AbdulKadir daya kankance mata idanuwanshi cike da rashin kunya.

"Hannunta fa zai rike Hajiya Talatu.

Kina ganin babu wata matsala su tafi gida su kadai...

Yaron yanzun basuda kunya wallahi"
Wannan karin dariya Anty Talatu tayi
"AbdulKadir ne Hajiya Ramatu...

Babu abinda zai faru...

Idan basu tafi taren bane matsala..."
Kai kawai Anty Ramatu ta jinjina, amman duk da haka bataso tafiyar AbdulKadir da Waheedah din ba, musamman data juya taga ya rike hannun Waheedah din tana bin bayanshi.

Wannan tabe-taben rashin kunyar ko kadan ba sonshi takeyi ba.

Idan yai hakuri gobe dai-dai lokacin ta rigada ta zama mallakin shi duk rikon dazai mata ladan hakan zai samu ba yanzun da babu komai cikin hakan sai tarin zunubi ba.

Bai tsaya da ita ko ina ba sai gaban motar, har lokacin baiga fuskarta ba, kanta a kasa yake, banda dokawa babu abinda zuciyarta take mata.

AbdulKadir ya gama sakata a kunya, batasan ya zata fara hada idanuwa dasu Anty Ramatu ba yanzun, sosai taji dadin zuwan Anty Talatu wajen dan a kasan zuciyarta take jin yanda AbdulKadir yake gab da tsulama Anty Ramatun rashin kunya.

Tana nan tsaye kanta a kasa harya bude mata murfin motar, alkyabbar jikinta ta tattara tukunna ta shiga, zama tayi ta rufe murfin motar tana wasa da yatsun hannunta da ta ajiye kan kafafuwanta.

Bai mata magana ba shima, motar yaja suna kama hanyar gida.
Chapter 44 · 0% Book details