Sashe 35
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanda take karantarshi har mamaki yake bashi, tashi yayi ya dauko wallet dinshi ya ajiyeta gefen kanshi yana gyara kwanciyarshi.
Hotonta yai amfani dashi ya danne na Nuriyya da zai sakashi tunanin abubuwan da zasu addabeshi.
Baccin ya fara jin yana fisgarshi
'Hamma kayi addu'a'
Yaji muryar Waheedah na fadi cikin kanshi, batare daya bude idanuwanshi ba yayi addu'a, ko tofawa baiyi ba, bacci ya dauke shi.
Washegari da yake ya fada asabar, Ahmad ya dame shi, suka shiga kasuwar wayoyi ya gyara screen din wayarshi tukunna suka dawo.
Suna dawowa charge ya saka wayar dan yaga yayi kasa sosai.
Yai sallar azahar yazo ya zauna ya fara cin abinci, wayar ya ciro daga chargy ya bude data dinshi yana ci gaba dacin abincin, text dinshi ya shiga ganin wajen sakonnin ashirin, ya kuma san Waheedah ce.
Dubawa yayi duka na jin ko yana lafiyane.
Zuciyar shi na daukar wani irin dumi da sakonninta ne kadai kan haifar.
Tana bashi kulawar da yake so, kulawar da babu wanda yake bashi ita sai Hajja, itama bakowanne lokaci ba.
Whatsapp din ya shiga, sakkoninta ne da yawa, zaice ita kadai take turo mishi sakkoni haka, su Nawaf gaisuwace, sai kuma zagi idan ya karanta bai amsa ba.
Yassar ma hakan ne, yafi jin dadin nata fiye da nakowa, ita kadaice bata taba magana akan halayyarshi ba, asalima tana saka shi jin babu wani abu marar kyau a abinda yakeyi din.
Bata damu dako ya amsata ko bai amsata ba, idan tazo takan sake mishi magana ta kuma bashi labari, Waheedah daban take da kowa na rayuwar shi.
Daga farko ya fara karanta sakon, da gaisuwa ce, hirar makaranta.
Sai kuma ta fara bashi labarin suna hidimar biki.
Karanta sakkonin yake yana cin abinci, kafin yaji shinkafar ta bimishi ta hanyar da bai kamata ba, tari ya kuwa sarqe shi, ruwa ya dauka babu shiri yana kwankwada, amman tarin bai daina ba, ga kirjinshi da yakeji kamar an fara hada wuta a ciki, idanuwan shi harsun kawo ruwan wahalar shaqewar da yayi, hakan yasa shi kankance su yana sake duba sakon Waheedah
'Nikam nagaji sosai Hamma, daman haka hidimar bikin kawa yake?
Allah nafi Nuriyya gajiya'
Kasa yayi babu shiri yana isa sakonta na karshe
'Hamma har an daura auren Nuriyya fa'
Karanta sakon yake yana son fahimtar asalin ma'anar shi, kafin yaji numfashin shi na barazanar daukewa.
Kanshi yake girgizawa yana sake danna wayar ko zaiga wani sabon sakon Waheedah din da zai karyata na karshe.
"No...
No...
Wasa ne wannan"
Ya furta yana jin zuciyarshi kamar tana rabewa biyu, kullum Waheedah na mishi hira, me yasa bata taba ce mishi Nuriyya zatayi aure ba, sai yanzun ne zata fada mishi an daura mata aure.
"Haka nace ki jirani, in nutsuwa waje daya Nuriyya.
Nace ki jirani"
Yake fadi kamar wanda ya samu tabin kwakwalwa, ji yake gabaki daya duniyar ta hade mishi waje daya.
Wayar ya cilla kan gado yana ture abincin, mikewa yayi ya fice daga dakin kwanan nasu.
Wajen motsa jiki ya nufa, yana addu'ar kar wani ya tare mishi hanya, dan ko gani bayayi sosai, wani abu yake son duka, idan ba punching bag ba, to fuskar duk wanda tsautsayi ta gifto dashi.
Allah ya taimake shi harya karasa wajen motsa jikin baici karo da kowa ba, bai kuma kula ko ana kaucewa bane idan an hangoshi
"A.
Bugaje..."
Ahmad dake wajen ya kira ganin yanayin Abdulkadir din
"Ka matsamun Ahmad..."
Abdulkadir ya fadi yana karasawa ya dauki abin nade hannu ya fara nannadawa a hannun shi.
Ahmad na karasawa wajen shi
"Me ya faru?
Lafiya?
Kaimun magana dan Allah..."
Dayan hannun Abdulkadir yake nadewa
'Hamma har an daura auren Nuriyya fa'
Shine maganar dake mishi yawo a ko ina na jikin shi tana kara saka kirjinshi wani irin radadi, yasan bacin rai, yasan fushi, yasan abubuwa da dama.
Amman yanayin da yakeji yanzun daban ne a rayuwarshi, yanayine da baya fatan ya sake jin shi har abada, dan haka bazai bari ya dame shi ba, zai daki wani abu har saiya daina jin kirjinshi na mishi kamar zai bude.
"A.
Bugaje..."
Ahmad ya kira cike da damuwa a muryarshi, Allah ne shaida yana jin Abdulkadir din kamar dan uwanshi.
Bai kuma taba ganin yanayin da yake gani a fuskarshi ba, bai kula shi ba, punching bag din ya soma duka kamar zai jijjigota, da dukkan karfin shi yake dukanta, amman ji yake kamar yanayin da yakeji na karuwa da duk dukan, kamar da tunanin Nuriyya a matsayin matar wani zuciyarshi na kara budewa.
Saida yaji numfashin shi na barazanar daukewa tukunna ya daina dukan yana dora hannuwan shi gwiwoyin shi hadi da wani irin sauke numfashi, tukunna ya dago ya hada wata irin zufa.
Kankance idanuwan shi yayi yana kallon Ahmad, muryarshi can kasan makoshi yace
"Tayi aure.
Ahmad tayi aure..."
Kai Ahmad ya jinjina mishi yana fahimtar dalilin da yasa Abdulkadir din shiga yanayi, bai magana na ba, dan yaune karo na farko da Abdulkadir din yake fada mishi wani abu mai girma haka
"Ta jirani fa in nutsu ne...
Shine tayi aure.
Ni nace banyi tunanin aurenta bane?
Me yasa zatayi aure?"
Ya karasa yana sauke numfashi, hannu Ahmad yakai ya taba kafadar shi cikin son nuna mishi yana tare dashi, ya fahimta.
Abdulkadir din ya kauce yana fadin
"Don't...
Kabarni"
Ya juya yana ficewa daga wajen motsa jikin, dan iskar da take wajen ta mishi kadan, kanshi kamar zai bude saboda bacin ran da yakeji a cike dashi.
Har wani ja-ja yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi.
Tayi aure bata jira shi ba, shine tunanin da yake cike dashi, yana jin wani yanayi na maye gurbin koma meye yake ji akan Nuriyya...!
#TeamAbdulKadir
#TeamYassarDinAntyFati
#TeamWaheedah
#FWA
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
adauki dan Allah...
Ka saukake mun auren nan"
Muryar Waheedah ta daki kunnuwan shi tana dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake budesu akanta.
Dubawa yake ko zaiga alamar wasa a tata fuskar, ko zaiga hijabin da ta saka tsakanin su ta yaye.
Kan hannun kujerar dake kusa dashi ya zauna yana maida numfashi, sosai ya girgiza, bazai tuna ranar karshe da wani abu ya girgiza shi haka ba.
Kallon Waheedah ya sake yi da yaji kamar kafafuwan shi na rawa saboda tashin hankali.
Hannu yaga tasa tana share kwallar da ta tsiyayo kan kuncinta.
Kirjin shi yaji yana zafi, gani yake yau din gabaki daya duk wani abu da tasan bayaso takeyi, kamar kuma tana yi dinne dan ta bata mishi rai.
"Wahee..."
Ya kira muryarshi can kasan makoshi, bata dago ba, taji shi, ta saurara ne ko tsikar jikinta zata tashi kamar ko da yaushe, tsayin shekaru baisa ta daina jin yanayin soyayyar shi ta daban da take taso mata duk idan ya kira sunanta.
Wannan karin babu abinda taji banda gajiya da komai, duniyar take ji ta hade da ita a waje daya, kamar tana cikin dakin da babu ko da window ballantana kofa, ji take fitarta daga dakin zata zo da saukake mata auren shi da zaiyi.
"Wahee magana nake miki"
Abdulkadir ya fadi, yana kokarin danne bacin ran da yake ciki, yanayin da yazo mishi a wahalce, saboda Waheedah ce, bai taba boye wani yanayi nashi ba a tare dashi.
Bai taba tsoron bude mata komai nashi ba, tare da ita bai taba jin akwai wannan bukatar ba, idan ranshi a bace yake yana nuna mata saboda tasan yanda zatayi dashi, idan farin ciki yake takan gani.
A gabanta yake dariya sosai dan yasan bazata taba raina shi ba, a yar karamar duniyar shi daga ita sai Yassar yake tsokana sosai.
Ita fiye da kowa, ko Yassar kanyi shakkar mishi wani wasan, amman cikin ido Waheedah kan kalle shi ta tsokane shi.
Ganin tayi shiru har lokacin yasa shi saukowa daga kan kujerar yana tsugunnawa kusa da ita.
Hannuwanta ya kamo duka yana rikewa cikin nashi.
Kusancin shi bai taba kinyin tasiri akanta ba, yasani, lokutta da dama ko damun shi tayi da surutunta, matsawa zai ya rike hannunta bakinta zai shiru.
Idan wani abu yai mata daya riketa a jikin shi yaji ta zagaya hannuwanta a bayanshi yasan ta karbi hakurin shi batare daya furta ba.
Yanzun ma hakan yake so yayi amfani dashi kafin komai ya karasa kubce mishi.
Ita kanta Waheedah mamaki takeyi, dan tasan abinda yake kokarin yi din, lokuttan duk da yayi tasani, amman hakan bai taba hanashi tasiri akanta ba, wannan karin zuciyarta ta gama bushewa.
Hawayen da ke shirin zubo mata taji sun tsaye cik, kamar tabatan da yayi ya kara busar mata da zuciya.
Hannuwanta ta zame daga cikin nashi, tana yawata idanuwanta akan fuskar Abdulkadir din
"Ka kwashi yaranka, ka bani takardata..."
Tai maganar muryarta na mata baqunta cikin kunnuwanta, balle Abdulkadir da yake kallonta idanuwanshi na kankancewa da bacin rai.
Kallon shi take, yanayin da take gani a fuskarshi a da zai tsoratata, sosai zuciyarta zata fara rawa da abinda zai faru, amman yau ko a jikinta take ji.
Itama ranta a bacen yake, karo na farko da takejin son dora bukatarta sama da tashi.
Wani murmushi yayi mai sauti yana mikewa, bin shi da kallo Waheedah tayi ganin ya soma tafiya, amman ba kofa ya nufa ba, hanyar da zata kaishi dakin Anty.
Wani sabon zazzabi take ji yana lullubeta, da gaske Abdulkadir yakeyi yaranta zai dauka.
Hawayen da suka bushe mata take jin sun fara farfadowa.
Tana kallon shi harya bace mata, dakin Anty ya nufa kanshi tsaye.
Ko kwankwasawa baiyi ba ya tura kofar yana samunta a tsaye.
"Ikram zaki bani"
Kallon shi Anty takeyi, tasan taurin kanshi tun yarinta, amman nayau da take gani daban ne, musamman Waheedah, bata taba ganin ran yarinyar a bace irin nayau ba, ko menene Abdulkadir din yai mata mai girma ne.
Amman hakan baya nufin tana son ganin mutuwar auren nasu, kodan yara dake tsakani
"Abdulkadir karkayi haka, karka yanke hukunci cikin fushi dan Allah.
Ka duba yarinyar nan duka watanta nawa a duniyar?
Idan zaka tafin ne ma, ka dauki Fajr shi.