Sashe 17
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Addu'ar Allah ya tsare da ta neman saukin zafin rai yake nemawa Abdulkadir din, da damuwar yanda kanin nashi zai rayuwa shi kadai a wani gari batare da kulawar wani nashi a kusa ba...!!!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#FWA*
*#AnaTare*[
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Zaune take gaban mudubi badan zatai kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta sakama jikinta riga da wando na Pakistan, ta dauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna batare da tasan asalin abinda take tunani ba.
A hankali ta dauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken kara fitowa.
A hankali cikin sanyin yanayinta tayi baya da kujerar da take sama tana mikewa tsaye.
Madai-daicin tsayin da take dashi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta.
Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riqe da hijab
"Ke ba dake za'aje kun shin ba?"
Mami ta bukata, tana kallon Waheedah data girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yanda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah din tace a aji shidda sakandire, Waheedar tace take shirin zana jarabawar gama aji shidda, ko Amatullah ta gitta sai taita kallon su, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take ma fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zaiji abinda ake ji.
"Jikina yamun nauyi Mami, suje abinsu, nace Amatu zata sakamun jan lalle idan zamu kwanta..."
Waheedah tai maganar tana katse wa Mami tunanin da take.
"Allah ya kaimu...
Zamu fita kasuwa da Haj.
Halima"
Kai Waheedah ta jinjina tana fadin
"Saikun dawo..."
Tsaye tayi har saida taga Mami ta fita daga dakin tukunna, daga nan cikin dakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da zasu sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta baya mata ciwo, dan bawai tana son hayaniya bane, amman biki yara uku ita kanta tasan saidai suyi hakuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za'a daga, dan ginin shi ko rabi baikai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai daki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi.
Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulkadir ne manne da zuciyarta, zata iya cewa tun tafiyar shi da rana daya bai taba barin tunaninta ba.
Lokutta da dama tana tashi daga bacci takanji kirjinta yai mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara daya akace zaiyi yazo gida, amman yanzun shekaru biyu kenan.
Watannin baya kasa hakuri tayi, batasan lokacin da tambayar ko yana lafiya ta subuce mata a gaban Abba ba, shine ma yace mata yaje ya duba shi sau daya.
Yana lafiya, tukunna taji tadan samu nutsuwa ta wasu fannonin.
Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma'a.
Ta rigada ta saba data idar da sallar asuba take karantawa, yau din bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, dan duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja.
Tunanin taje ta dauko Qur'an din takeyi, Aminu ya shigo da sallamar data amsa mishi cikin sanyin murya
"Commander an diro..."
Ya fadi yana dariya, hadi da wucewa kitchen, muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma'anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta taji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, dan yanda ta fara doka mata, in bata miqe ba, tanajin tsaf zata fito daga kirjinta tayi kafafuwan kanta ta fice daga dakin dan neman duk inda Aminu yace Abdulkadir din yake.
Mikewa Waheedah tayi tana saka hannu ta dafe kirjinta, inda take jin zuciyarta na kara gudu da duk daqiqa.
A bakin kofa ta zira takalman bandaki da batasan ya akai suka zo wajen ba.
Manya-manya ne, karamar kafarta na yawo a ciki, amman bata ma kula ba.
Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, kafafuwanta take takawa tana nufar bangarensu, badan sun taba doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amman tanajin wata irin sanayya da tai mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in akazo maganar sanin halayen shi.
Abdulkadir din data sani bazai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa bangarensu zai wuce yaga mahaifiyar shi, banda Abdulkadir, zai iya jira, daya shiga hayaniyar da take bangaren Hajja gara ya jira.
Tana da tabbacin yana bangaren su.
Nan kuwa kafafuwanta suke daukarta, bayan shi ta fara hangowa, zata rantse da Allah ba girma kawai ya kara ba, harda tsayi, jakace rataye kan kafadar shi, rigar jikinshi ta kamashi kamar zata bude, damtsen hannun shi tabi da kallo daya kusa yar siririyar cinyarta.
Sosai take takawa, bugun zuciyarta na karuwa, wani irin dumi taje ji jikinta ya dauka kamar zazzabi na shirin kamata.
Tsaye tayi a bayan shi tana kasa motsa labbanta, hannunta daya na kan kirjinta kamar maison kare zuciyarta da take tunanin zata iya fitowa kowanne lokaci.
Hannun shi Abdulkadir yakai yana sake kwankwasa kofar, yana jiyo kidan da suka kunna har nan inda yake tsaye.
Tsaki yaja yana addu'ar wanda zaizo ya bude kofar ya kasance kasa yake dashi, yanda zai zabga mishi marin tsayuwar da yasha a bakin kofa, in ba wulakanci ba, ya zasu kunna kida su kuma kulle kofa daga ciki.
Yana shigowa gidan ya fara dana sanin zuwa.
Baisan meye a maganganun Yassar da sukanyi tasiri akan shi haka ba, amman saiya sauke mishi sakashi zuwan da yayi.
Bayason hayaniya irin haka, saboda yasan dole sai wani ya bata mishi rai, ga hannun shi yana saurin tashi, yanzun abin harya fi nada.
Yana sane yaqi zuwa hutun sallar da sukan zo na kwana biyu ko uku in yayi tsayi.
Bawai dan baiyi kewar gida ba, sosai yake jin kewarsu, musamman Hajja da Zahra, babu wanda yagani tunda ya tafi daga Abba da sai Yassar.
Dan shi kusan duk wata biyu sai yaje ya duba shi, kafin ya tafi kuma duk zuwan da zaiyi sau sunyi fada.
Saida yaja dogon tsaki tukunna ya kara kwankwasa kofar da karfi wannan karin.
Alama yaji ta cewar akwai mutum a bayan shi, kafin ya tsayar da hankalin shi waje daya, yanajin shiga da fitar numfashin Waheedah da takeyin shi a tsorace.
Juyawa yayi gabaki daya, yana tsorata Waheedah da take tsaye, ta kuwa yi baya gabaki daya, cikin zafin nama ya riqo hannunta, saida yaga ta tsaya da kafafuwanta tana ware mishi idanuwanta da suke cike da tsoro tukunna ya saki hannunta, yana mamakin yarinyar daya bari ce a gaban shi, komai ya canza tattare da ita banda farinta, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su akanta, tayi wani irin girma naban mamaki, farin da rashin kibar yana nan, sai dai za'a iya kiranta da budurwa, duk da a idanuwan shi tana nan a yar yarinyarta.
Waheedah kuwa dayan hannunta ta saka tana kama wanda Abdulkadir ya saki, zuciyarta naci gaba da lugude a cikin kirjinta, numfashinta ma kokawa take dashi cikin yanayin da kusanci dashi haka kadai yake bayyanawa, sosai ya canza mata, kuma ba askin kanshi kadai bane yasa fuskar shi canza mata, dan ya aske shi qasa sosai, Abdulkadir da yake tara suma, fuskar shi tai mata fayau da askin da akan kira buzz a turance.
Ga tabbai qananu a fuskar da batasan yanda akai yaji su ba.
Tabon da yake gefen goshin shine kawai tsohon abu a fuskar shi, dan tasan dashi tun kafin ya tashi.
Idanuwanta ta sauke zuwa wuyan shi, inda yake da wani dogon tabo daga gefen mummuqen shi zuwa wuyan, yana bace ma ganinta daga inda rigarshi ta lullube, wani abu na matsewa a zuciyarta, hannunta takejin yana mata kaikayi haka kawai, so take ta kaishi kan tabon da alamu suka nuna sabone sosai, ta kuma kirga duka qananun da take gani kan fuskarshi, yanda inya sake dawowa zata ga ko yaji wani sabon ciwon ko baiji ba.
Kofar da Abdulkadir yaji an bude yasa shi dan juyawa, kafin ya sake juyowa yana mayar da hankalin shi kan Waheedah.
Yana mamakin yanda ta tsaya tana kallon shi, kamar tana son bude har tsokar jikin shi taga ko yana boye wani abu cikin kasusuwan shi, yana kuma mamakin tsoron da yake cikin idanuwanta bai hanata kare mishi kallo haka kamar ta aike shi ba, batun yanzun yake kula da ita ba.
Ko abu su Zahra suke son tambayar shi ita din suke sakawa, haka zata kalle shi cike da tsoron shi da baya hanata yi mishi tambayar, karfin halinta bazai gaji da bashi mamaki ba.
Baisan dariya mai sauti ta kubce mishi ba, saida yaga yanda ta hadiye wani abu da yafi karfin yawu
"Hamma..."
Ta furta, muryarta can kasan makoshi, idanuwa Abdulkadir ya kafeta dasu, yana sata sake hadiye wani abu da take ji tokare da makoshin ta.
Zata rantse tanajin zuciyarta ta yunkuro mata da tambayar da ta jima tana ma iska a dakin su, tunda shidin da take son tambaya baya nan.
"Shekara daya akace Hamma....
Shekara daya akace zakayi kazo...
Me yasa ka dade?"
Wata gajerar dariyar Abdulkadir ya tsinci kanshi da sakeyi
"Shine gaisuwar?"
Ya bukata, muryar shi na nutsar da gudun zuciyarta.
Ta dauka girman shi zaisa muryar shi ta canza ko ta kara budewa, tana nan yanda tasanta, shidinne kawai ya canza a bayyane.
Dan murmushi taji ya kwace mata
"Ina wuni..."
Kai Abdulkadir ya girgiza kawai
"Ki kawomun abinci"
Ya fadi maimakon amsa gaisuwarta, ya juya yana sa hannu ya tura kofar, akan ce idan ka girma, rana da abubuwa nasa haskenka yadan dishe.
Bayajin ko wahala zatasa Waheedah dishewa, da tunanin farinta da yakeji cikin idanuwan shi har lokacin ya shiga dakin yana fadin
"Uban waye ya kunna kida ya kuma kulle kofa daga ciki?"
Ya karasa maganar yana kare musu kallo, dakin kusan cike yake da mutane, bakin fuskar da bazai wuce dukan su ahalin Bugaje bane ba, dan ga kamannin nan yana gani, wasu kuma ya gane su.