← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 94

Sashe 82

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin abinda zasuyi suhoor dashi takeyi da yanda zata kaya musu washegari, ranta duk baya mata dadi, amman yanzun tasan indai girki ne ta kare, fadansu da ta hango ita da AbdulKadir kan hakan ya wuce.

Sosai hankalinta ya kwanta
"Waheedah...

Ashe kin dawo"
Ta fadi tana saka Waheedah din da AbdulKadir juyawa a tare, Waheedah najin wani abu ya taso mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta yana dawowa kirjinta ya tokare, AbdulKadir kuwa wani irin tsoro da baiyi tsammani ba yaji ya lullube shi, kar Nuriyya din tayi kokarin rike shi a gaban Waheedah, da sauri yazo ya rabata ya fice daga kitchen din yana wucewa bedroom din Waheedah ya turo kofar, jikin shi yakeji har bari yake mai, dan baisan ya zaiyi ba, a karo na farko a rayuwar shi da komai ya kwance mishi.

Waheedah kuwa wani kallo tayi ma Nuriyya din da yasa taji gwiwoyinta sunyi sanyi.

Ba zatace tun zuwanta gidan suna hira da Waheedah din ba, ko kuma sunci gaba da zama kawaye, amman suna gaisawa kullum, kuma tana shigowa bangaren Waheedah din ta zauna a falo, har remote take dauka tayi kallo, musamman in tajiyo kamshin girki, data kula ko batazo ba tana bata abinci saita rage zuwa sai AbdulKadir na nan.

Amman Waheedah daman ta daina fara'a a gabanta, sai dai bata mata irin wannan kallon, bata mata kowanne kallo ma.

"Sannun ki"
Waheedah ta fadi tana juyawa taci gaba da abinda takeyi, watakila ko dan batajin dadine, Nuriyyar tayi tunani, hakan yasa ta wuce ta koma bangarenta dan bata kula da sanda AbdulKadir ya fice ba.

Tsaf Waheedah ta karasa gyara kitchen din tana share shi, fridge dinta ta bude taga an dibar mata robobin kayan miya, ta kuma san Nuriyya ce, daga yau kuma ta kare, can gidan kasa ta tsugunna, tana janyo kwami ta ciro roba fara mai murfi, dakyar ma ta fito da ita dan tayi kankara.

Farfesun kayan cikine a ciki, tukunya ta dauko ta saka robar a sink tana sakar mata ruwa dan yadan saki.

Doya ta yanka da zata isheta iya cikinta, ta fere tana zuba dan mai a abin suya, ta soyata fararta, tana kwashewa a plate.

Lokacin farfesun ya saki, iya wanda zai isheta ta diba ta zuba a tukunya tana mayar da sauran a fridge.

Ta dora, da yake yasha kayan kamshi, kafin kace wani abu gidan ya budade da kamshin daya fito da AbdulKadir yazo kitchen din yana fadin
"Me kike dafa mana?"
Juyowa tayi tana kallon shi
"Daga dawowata zan karbi girki?

Banda lafiya ko ka manta, sai jibi nikam"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta
"A'a ba abin tashin hankali bane ba, sai in koma gida, jibin in dawo"
Kai ya girgiza mata da sauri, shi bashida karfin fada koyin gaddama da ita.

Duk da yaso jinta a jikin shi daren yau, kwana biyu bazai canza wani abu ba, sanin tana cikin gidan ya ishe shi, ran shi ya biya da abincin sosai, wata yunwa da baisan yanajin taba ta taso mishi.

Dan waje ta samu ta juye farfesun a ciki, AbdulKadir din yakai hannu zai dauki guda daya ta doke hannun shi
"Ni ban dafa da kai ba Wallahi"
Tana janye kwanon ta ajiye gefe, kallonta yake, yayi mata laifi yasani, ya bata hakuri kuma
"Ba kyau horon yunwa"
Ya fadi can kasan makoshi, Waheedah nayin kamar bataji shi ba, duk abin ya mishi wani iri sosai dan bai saba ba, sau nawa take hakura da abu tabar mishi, amman yau itace take cewa tayi girki banda shi, zuciyar shi batai mishi dadi ba sam, tukunyar data bata take wankewa.

Sai ga Nuriyya ta shigo kitchen din tana ta washe baki, dan tana sallar isha'i take jiyo kamshin, yawunta sai tsinkewa yake, kwana biyu bataci abu mai galmi-galmi ba.

"Kamshi duk ya cika gidan, me ake dafa mana ne"
Ta fadi kamar yanda ta saba, AbdulKadir na kallonta a karo na farko yaga kwadayi a fuskarta, baisan ko dan shima an hanashi bane yasa shi jin haushin kwadayin nata.

Ga mamakinta ko inda take Waheedah bata kalla ba, asalima plate din doyar ta dauka da kwanon farfesun tana zuwa ta gabansu,
"Kudan fita zan rufe kitchen din"
Ta fadi tana ganin suka fita bakin kitchen din suna ta kallonta, sai da ta janyo kitchen din tasa mukulli ta rufe tukunna ta wuce da fadin
"Sai da safen ku"
Su biyun suna binta da kallo cike da mamaki
"Ina namu?"
Nuriyya ta fadi bayan Waheedah ta shige lungun da zai kaita dakin baccin ta, dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Nima bata bani ba"
Ya amsa ranshi a jagule yana wucewa bangaren Nuriyya din, da duk da mamakin da take bai hanata jijjiga kitchen din ba taji da gaske a kulle yake, dan Waheedah bata taba rufe kitchen dinta ba.

Tsaye tayi a wajen ta kasa yarda da abinda ya faru...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Da wani irin sanyin gwiwa ta karasa bangaren ta, watakila har yanzun Waheedah batajin dadi, in baka da lafiya daman komai fita ranka yake shisa.

Ko kuma taji haushine dan batai mata ya jiki ba, ita kuma sai lokacin tunanin yazo mata.

A haka ta karasa bangarenta, ta samu AbdulKadir kan doguwar kujera a zaune.

Karasawa tayi ta zauna a gefen shi, yanajin shigowarta, ran shi a bace yake, ga yunwa da yakeji kuma.

Baisan me yasa sai yanzun yake jin haushin ta ba, dana kudin shi da ta kashe, da kuma na yau da ko kadan bata neme shi ba ballantana tasan bashida lafiya harya yini a asibiti.

Har yanzun yaga alama batasan waye shi ba, ko dan rashin Waheedah a kusa dashine yasa yake ganin komai ma bashida muhimmanci, yanzun da yasan ba zata barshi ba, ya samu natsuwar da zai fuskanci sauran matsalolin shi.

Bayason kashe kudin da bashida dalili, komai nashi a kan tsari yake, sosai yakan yi tunanin abinda takeyi da kudi, kuma ba a dan zaman sun nan ya kula da idan ya ajiye kudi a wallet tana kwashewa ba, ko yazo yin kwana biyu, indai zai mata nata kwana dayan saita dibar mishi kudi.

Idanuwa ya dauka ya saka mata yaga gudun ruwanta, yanzun ne ta gama kawo mishi wuya.

"Mu me zamu ci?"
Nuriyya ta bukata muryarta a sanyaye, dan sosai ta saka ranta a abinda Waheedah din ta girka.

Sai takejin da wahala ta iya cin taliyar da ta dafa
"Ke ba mace bace?

Baki dafa naki bane?"
AbdulKadir din ya bukata yana tsareta da idanuwa, duk da maganganun shi sun mata zafi, murmushi ta danyi
"Na dafa mana taliya"
Baice mata komai ba, ganin hakan yasata mikewa ta samu plate ta zubo musu taliyar, har miyar ta hade.

Tare sukaci, AbdulKadir na rasa ranshi da yake a bace ne, ko taliya ce da bai cika so ba, ko kuma girkin ne bashida gabas, dan ko gishiri-gishiri na miyar ma baiji ba, sai wani daci-daci.

Turawa kawai yayi, ita kanta Nuriyya da tana da wani zabi sam ba zata ci taliyar nan ba, sa ma ranta cin girkin Waheedah da tayi yasa taliyar kara fitar mata daga rai.

Tana kai kwanon kitchen dakin baccinta ta wuce, ta dauki wayar ta.

Tallar littafin Hauwa A Usman Jiddarh tagani na Saki Reshe, tana tunanin sarkakkiyar da take ciki na yanda za'ayi jarumin ya kasance gagarumin dan fashi.

Ba'a kai da fara shi ba, hakan yasata jan dan karamin tsaki, daman jiya littafin Fadime na Bingel ta maimaita dan sosai takejin dadin littafin, soyayyar da aka shimfida ciki na tuna mata dalilin da yasa ta auri AbdulKadir tun da farko, amman yanzun ta fara gajiya dan taci karo da abinda bashi take tsammani ba.

Ganin babu abinda zata karanta yasa ta dauko system din ta, daman tana lallaba fina-finan da take dasune, tana budewa sai ga AbdulKadir ya shigo dakin, karasawa yayi kan gadon yahau yana saka hannu yaja system din
"Masoyi..."
Ta fadi tana kallon shi, bai mata magana ba yasa hannu yana kashe system din dauketa daga kan gadon gabaki daya ya dora kan drawer din da take gefen shi ya juyo yana tsura mata kananun idanuwan shi da suka sata yin shiru
"Ki kashe mana wuta"
Ya fadi, dan makunnin ba'ayi shi a kusa da gado ba, mikewa Nuriyya tayi tana zuwa ta kashe wutar ta dawo ta kwanta itama, sai dai ga mamakinta, juya mata baya AbdulKadir yayi da alamun bacci zaiyi.

Wani abu taji yai mata tsaye a makoshi, batason ya sauke mata fadan shi, shisa ta hakura bata dauki system din ba, wayarta taci gaba da dannawa, tana ganin yanda status din kowa ya gauraye da maganar ganin wata
"Anga wata"
Ta fadi, AbdulKadir ya jita, surutunne ba zaiyi da ita ba yau, asalima niyyar azumi ya daura a zuciyar shi, sake gyara kwanciya yayi yana fuskarta, wayar da take hannunta ya fisge yana sakata a key ya ajiye a tsakiyarsu tare da fadin
"Ki kwanta Nuriyya"
Muryarta can kasan makoshi tace
"Banajin bacci wallahi, bakasan baccin da na sha ba yau daka fita"
Shisa bata neme shi ba, baccin ta yafi jin inda yake muhimmanci.

AbdulKadir ya fadi a ran shi, zuciyar shi na kara jagulewa
"Bazan sake magana ba..."
Cewar AbdulKadir din cikin iko da gadarar shi da take bata mata rai.

Gyara kwanciya tayi, ranta in yayi dubu a bace yake, batasan iya lokacin data dauka a haka ba har bacci ya dauketa itama.

Su dukkan su baccin suke, shi AbdulKadir baccin daya kwana biyu baiyi bane ba, ita kuma Nuriyya baccin da batayi da wuri bane, ko ma da wurin ta kwanta shi yake tashinta sallar asuba, inba haka ba sai dai ta makara, dan in baya gari makara takeyi.

Hakan yasa ko kiran sallar farko basuji ba, sunata bacci har karfe shidda saura.

Haske AbdulKadir yagani cikin idanuwan shi, kasancewar window din dakin baccin Nuriyya din daga waje yake, duk da wanda yake waje ba zai iya hango su ba, su da suke ciki zasu iya hango shi, haka gilashin window din yake.

Amman bai hana hasken da yake nuna alamar gari ya waye shigowa ba.
Chapter 82 · 0% Book details