← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 94

Sashe 39

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kije kic
i abinci..."
Dakuna fuska Waheedah tayi
"Mami baki dafa mana komai ba?"
Murmushi kawai Mami tayi, kamar Waheedah zatayi kuka ta baro kitchen din tana zira takalmanta ta fice daga gidan.

Ta manta girkin Mama ne ranar da taci wani abu a makaranta, yunwar da takeji kuma ba zata barta ta tsaya koda indomie ta dafa ba.

Zataje taga ko abinda Mama din ta dafa zai ciyu.

Bangarenta ta wuce tana shiga da sallama, bata samu kowa a dakin ba, dan haka ta wuce kitchen din, kulolin da ake zuba abinci ta bude, tana cin karo da malmalolin tuwon shinkafa da suke kulle a fararen ledoji.

Plate ta dauka, tasaka malmala daya a ciki, lumshe idanuwanta tayi tana addu'a a cikin zuciyarta miyar ta kasance ta taushe ce, ko ya aka watsal-tsala zata iya daurewa taci kodan yunwar da takeji.

Zuciyarta taji tayi wani irin tsalle da yasata bude idanuwanta tana dafa dayan hannunta jikin kantar kitchen din, batasan me tagane nashi ba, takun tafiyar shi, kusan shi, ba zatace ga asalin abinda taji ba, amman ba saita juya ba, tasan shi dinne ya shigo kitchen din, AbdulKadir ne, sosai take jin shi gab da ita, jikinta yai mutuwar da ta kasa juyawa ne kawai, tana kallon shi ya mika hannu ya dauki plate ta saman kanta, ta gefe ya zira hannu yana dauko tuwon guda daya, ya saka a plate din yana karo wani guda dayan.

Tunda la'asar ya dawo gidan, yana daki a kwance ne saboda bayason surutu, bayason magana da kowa.

Ko passing out da akanyi shagali a gida, ayi su calender su menene ya fadama Yassar ya gayama su Hajja bayaso, suyi mishi addu'a kawai, kar wanda ya tara mishi mutane, in sunyi koda yazo zai juya.

Sanin halin shi yasa basuyi komai din ba, duk da haka Hajja tasa ya daukar mata hoton shi guda daya, tayi babban agogo ta kafe a falonta.

Tunda can bayason mutane, saboda suna bashi haushi, yanzun abinne ya karu, ko kadan bayason jin shi cikin mutane.

Yana jiran list din sunaye ya fito zuwa inda za'a kaishi ya hada jakarshi yayi gaba.

Tun da yazo yunwa ke cin shi, bai fadama kowa yana hanya ba, a cikin abokan shi wani zaizo Kaduna ya biyoshi.

Dan haka bai samu kowa a gidan ba, yaran gidan wasu na boko, wasu na islamiyya, Hajja kuma ta fita, har kitchen ya shiga bai samu wani abinda zaici ba, Nazir kadai yagani yace mishi girkin Mama ne, hakan yasa yunwar tashi bacewa na wani lokaci, kafin yanzun ta sake taso mishi tana fito dashi babu shiri.

Hijabin jikinta ya sanar dashi ita dince, bayajin akwai mai saka dogayen hijabai har suna share hanya a gidan nasu banda ita.

Ba zaice ga asalin abinda tai mishi take bashi haushi ba, duk da haushin kowa da komai yake ji.

Amman nata yai yawa, yanajin inda ta fada mishi Nuriyya ta fara kula wasu da yayi wani abu akai kafin lokaci ya kure mishi.

Duk da tun daga ranar da aka daura mata aure, bai sake bari tunaninta ya dame shi ba, ya riga ya faru, babu abinda zai iya akai, amman ya tabashi ta fannin dashi kanshi bai taba tunani ba.

Ganinta yanzun din yana saka wani abu matsewa a kirjin shi.

Wajen tukunya yadan matsa yana budewa, wata irin miyar kuka tai mishi sallama, tunda yake bai taba ganin miyar kuka mai muninta ba, yana ganin ruwan daban, kukar daban, man da yake a sama kamar daga baya akai tunanin zubashi yana gefe shima.

"Mama!"
Ya kira yana saka Waheedah sake lumshe idanuwanta da yanda muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta tana saka tsikar jikinta tashi.

Sai lokacin ta samu karfin juyowa tana sauke idanuwanta akan shi, rigar sojoji ce a jikinshi mai dogon hannu, sai gajeran wando, ya kara mata wani irin girma naban mamaki, sai taganta yar kararrama a gaban shi.

Wani yawu ta hadiye ko zuciyarta zata rage gudun da take a kirjinta
"Mamaa!!"
Ya sake kira a karo na biyu, dai-dai lokacin da Mama ta karaso kitchen din a rikice, dan ko bataji muryarshi ba tasan babu wanda zai mata wannan kiran saishi, bata dai tsammace shi a lokacin bane saboda tasan baya garin
"Wacce irin miya ce wannan?"
Ya bukata yana tsareta da idanuwa, Kallon shi Mama tayi girman shi na bata mamaki, kaf gidan batajin akwai mai tsayin shi.

"AbdulKadir...

Saukar yaushe?"
Ta tambaya maimakon amsar tambayar dayai mata
"Wacce irin miya ce wannan?"
Ya sake maimaitawa yana yin kamar baiji maganar datai mishi ba, hadi da dorawa da
"Ya mutum zai saka wannan miyar a bakin shi?

Meyasa za'ai mana tuwon shinkafa da wannan miyar?

Me yasa kike mana girki kamar Abba baya bada kudin da za'ai mana me dadi?"
Numfashi Waheedah ta sauke ganin yanayin dake fuskar Mama yasata fadin
"Hamma..."
Sai lokacin ya juya yana sauke mata kananun idanuwan shi da suke cike da rikici, kai tadan girgiza mishi alamar yabari, kome yake shirin sake fada karya fada, yai shiru kawai.

Wani irin tsaki yaja yana ajiye plate din ya fice daga kitchen din, itama Waheedah nata plate din ta ajiye tana rufa mishi baya, Mama tabisu da kallo kawai, dan AbdulKadir ya dade da daina bata mamaki.

"Hamma..."
Waheedah ta kira tana mayar da numfashi saboda gudu-gudun da tayi wajen binshi, juyowa yayi gabaki daya yana sata runtsa idanuwanta tukunna ta bude su
"Meye?"
Ya bukata yana tsareta da idanuwan shi da suke birkita mata lissafi, akwai kwarjini na musamman dashi kadaine yake mata
"Me zaka ci?"
Ta bukata, kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana sake juyawa.

Yanajin idanuwanta nabin shi harya sha kwana.

Numfashi ta sauke tana kai hannu a kirjinta inda zuciyarta take doka mata, takai mintina biyu a wajen tukunna ta wuce tana komawa bangarensu, sam ta manta da wata yunwa da takeji, tana shiga ta wuce daki, tana samun Amatullah ta fito daga bandaki da alamar alwalar magriba tayi dan ana gab da kira, hijab ta cire itama tana shiga bandakin ta gabatar da alwala.

Sanda ya dawo daga sallar isha'i ya samu abinci a dakinshi an ajiye.

Tunanin farko da yazo mishi shine Waheedah ce, zama yayi yana daukar plate din ya bude, dankaline da kwai, sai karamin flask din da yasan shayine a ciki, budewa yayi yana zubawa, kamshin shayin yasa shi sanin ba Waheedah bace ba, Hajja ce, ita kadai take saka Na'a'na'a a shayinta.

Haka kawai a kasan zuciyarshi sai yaji yaso ace ya fito daga hannun Waheedah ne, daya girgiza mata kai bayana nufin bazaici komai bane ba, yana nufin baisan me zaici ba, amman bata kawo mishi komai ba.

A cup ya zuba shayin ya soma hadawa da soyayyen dankalin da kwai yana ci, lokacin yaji an turo dakin da sallamar da kafin ya amsa Yassar ya dora da
"Ba zaka iya cemun zaka zo ba?"
Kafadu yadan daga ma Yassar din bayan ya amsa sallamar da yayi, gefen shi Yassar ya zauna yana daukar cokalin dake cikin plate din ya cako dankalin yasa a bakin shi yana soma taunawa tukunna ya ajiye cokalin
"Kafadu zaka dagamun?"
A kasalance AbdulKadir yace
"Me kake so inyi to?

Na riga nazo, komawa zanyi in kiraka ince maka zan taho?"
Kai Yassar ya jinjina, sosai rashin kunyar AbdulKadir ta karu tun shekarar data wuce, wani abu ya same shi da baisan menene ba, bakomai yake fada mishi ba, amman baya rufe shi har haka, ko kiranshi yayi a waya da cewar zaije Kaduna ya dubashi sai yace mishi babu lokacin da zai ganshi, tun yana zuciya yaqi zuwa harya kula AbdulKadir din na boye mishi ne, saiya dinga share shi baya kiranshi saiya shiga Kaduna tukunna.

To har yanzun kuma boye mishi yake, wannan ba kanin shi bane ba.

Wayarshi da take a hannun shi Yassar ya danna dan yaga ko karfe nawa, hakan yasa AbdulKadir cewa
"Nasan yarinyar nan..."
Yana dakuna fuska, danna wayar Yassar yayi haskenta ya dauke, da sauri AbdulKadir din yakai hannu yana fisge wayar Yassar din ya sake dannawa
"Kaban wayata AbdulKadir..."
Sosai yake kallon hoton fuskar wayar Yassar din
"Hawwa ce ko?"
Ya tambaya yana mika ma Yassar din wayar daya karba yana fadin
"Ban sani ba"
Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye plate din dankalin ya dauki kofin shayin shi daya rike da hannuwa biyu yana kurba
"Tun yaushe?"
Shiru Yassar yayi ya kyaleshi
"Hamma magana fa nake maka...

Tun yaushe?

Zaka fara dating baka fadamun ba ashe?"
Kallon shi Yassar din yayi
"Kamar yanda wani abu ya sameka baka fadamun ba kake nufi?"
Numfashi AbdulKadir ya sauke dan bashi da abinda zai fada, wani abu ya same shi da gaske, amman kuma ya riga ya wuce, fadar bashida amfani tunda ba wani abune zai canza ba idan yayi hakan.

"Me yasa ba za'a hada dana su Hamma Yazid ba?"
AbdulKadir ya bukata yana son sake akalar zancen.

Yassar yagane hakan, bazai takura shi sai yasan meya same shi ba
"Bamu dade ba, ba mufi wata biyu ba, kar wani abu ya canza a gaba..."
Kallon shi AbdulKadir yayi
"In har kasata a fuskar wayarka kana jinta a ranka Hamma, bana tunanin akwai abinda zai canza..."
Murmushi Yassar yayi, wata biyu da fadama Hawwa yana sonta, amman ya dan jima yana yin haka daga nesa-nesa daman, duk sanda zasu zo gidan, kuma suna dan chatting kadan a WhatsApp.

Bayaso abinda ya faru da Yazid akan Waheedah ya faru dashi, shisa bai kwauron baki ba, kuma da dukkan alamu itama ta jima tana jinshi din, duk da haka bayason yin gaggawa, duk da zaifi so suyi shagalin bikin nasu tare da Yasir, amman sam Yasir yace mishi shi bai shirya yin aure dan lokacin ba, da alama zai rigashi.

"Kayi magana kawai ayi bikin nan duk mu huta"
AbdulKadir ya fadi cikin sigar tsokana.
Chapter 39 · 0% Book details