← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 94

Sashe 30

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana jin Abdulkadir din ya wuce, danko dagowa baiyi ba, ya saka daya daga cikin nashi kayan, idan zasuyi mishi kenan, dan yaga ya kara budewa...!
*#TeamAbdulkadir*
*#TeamYazid*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Da kayan shi rungume a kirji ya shiga dakin hadi dayin sallama, bai samu kowa a falon ba sai Yassar daya amsa mishi sallamar yana kuma binshi da kallo yana fadin
"Meye a jikin kayan daka rungumosu kamar sabon jariri?"
Murmushin shi Yazid ya kara fadadawa, Waheedah ta goge mishi kayan, akwai kalar kamshin da ya kula tana yi duk idan ta gifta shi a cikin gida, idan zata fitane kawai bayajin yana kamshin, sosai kuma yake jinjina ma kokarinta na wajen ganin ta gujema abubuwan da addini ya haramta mata da mata kan dauka kananun zunubi a zamanin da ake ciki.

Haka kawai yau da ita ya tashi manne a ranshi fiye da kowanne lokaci, shisa yakai mata kayan yace ta danne mishi ta kuma shafa mishi turare.

Tunda ya amso yake jin kayan har kasan zuciyar shi.

"Hamma..."
Yassar ya fadi ganin yanda murmushin Yazid din yake kara fadada da duk dakika.

"Karka dameni Yassar"
Yar dariya Yassar yayi, harda shi cikin yan gidan wajen yima Yazid surutun kin nemo matar aure, amman yanayin da yake nunawa yanzun kamar na sabon kamu a soyayya
"Anya Hamma?

Baka kamu ba kuwa?"
Dakuwa Yazid din yai mishi, yana tsintar kanshi da jin wata irin kunyar kanin nashi da ta bashi mamaki.

Sosai Yassar yake dariya yanzun kam
"Yaa Rabb...

Hamma da gaske soyayya kake?

Wace mai sa"ar ce?"
Ya karasa tambayar da farin ciki nannade a muryarshi, a kasan ranshi harya fara addu'a da fatan ta gari ce, akance ba'a shaidar mutum, amman zai tashi tsaye yai shaidar dan uwan shi, duk a cikin gidan Yazid ne kawai zai bada shaida akan shi batare da wani shakku ba, ya yarda da nagartar shi dari bisa dari.

Yana da tabbacin matar da duk zata kasance karkashin kulawar shi ba zata taba samun dalilin yin koke ba.

Yazid mutum ne mai hakuri da kauda kai akan al'amuran duniya.

"Wacece Hamma?

Kaji?

Dan Allah wacece?"
Yassar ya sake jero mishi tambayoyin yana saka shi sauke numfashi mai nauyi.

Bai taba fadama kowa sirrin da yake zuciyarshi ba, har ita Waheedah din da sirrin ya shafa, amman yau yana jin ya fada ma wani, yana kuma jin son raba sirrin da wani, watakila ya samu karfin gwiwar fadama Waheedah din itama.

Ya kuma san Yassar na da sirri ba kadan ba, idan bashi yace ya fadama wasu ba, maganar ba zata taba wuce tsakaninsu ba.

Cikin sanyin murya Yazid yace
"Bata sani ba har yanzun ai"
Dan ware idanuwa Yassar yayi
"Jiran me kake to?

Meyasa baka fada mata ba?"
Kafadun shi duka biyun Yazid yadan daga cikin yanayin dake fassara shima baisan dalili ba
"Ina ganin kamar tayi yarinta ne, hakan nake fadama kaina saboda banason tabbatar da na rasa karfin gwiwa ne"
Fuskar Yassar dauke da murmushin fahimta yace
"Ba'a yarinta da sanin 'So' Hamma, saboda abune mai wahalar sha'ani..."
Kai Yazid ya iya jinjina ma Yassar din, yanajin jikin shi yayi wani irin sanyi, da gaskene ya kamata Waheedah tasan yanda yagama tsara musu sauran rayuwar shi idan yana da rabon gani, bai taba hango komai na rayuwar aure da wata idan ba ita ba.

Ko a titi yaga budurwa da saurayi, ita ce take fado mishi a rai.

Idan kallo yake yaga wani abu daya burgeshi, da ita yake hasaso aiwatar dashi.

Yana mata kyauta lokaci zuwa lokaci, amman yana jin tamkar ya janyo ranar dazai kashe mata duka kudin da suke cikin aljihun shi, ranar da zai siyo duk rigar daya gani yake tunanin zatai mata kyau ya kawo ta saka mishi yagani.

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarta na mishi yawo a cikin kwanyar shi, wucewa yayi da niyyar shiga daki ya sake kaya, Yassar dakatar dashi da fadin
"Ka fadamun sunanta idan ban santa ba"
Saida ya murza hannun kofar dakinsu tukunna yace
"Waheedah...

Waheedah ce Yassar"
Wani dum Yassar yaji cikin kanshi, kafin hanjin cikin shi su hautsina suna saka shi mikewa babu shiri ya rufa ma Yazid din baya.

Yanda ya tura dakin na saka Yazid din tsorata, wani irin yanayi yake gani a fuskar Yassar daya saka zuciyarshi soma dokawa yana fadin
"Yassar?"
Cike da shakku da alamar tambaya, kai Yassar yake girgiza ma Yazid din yana son ya tabbatar mishi ba Waheedah bace yake so, yana son ya gaya mishi bai hada soyayya da Abdulkadir ba, kallon Yazid din yake da idanuwan shi yana rokon shi da cewar zuciyar shi batai mishi haka ba.

"Yassar..."
Yazid ya sake kira wannan karin muryar shi na rawa cike da tsoro, ko kadan bayason abinda tunanin shi yake shirin hasaso mishi, hannu yadan daga ma Yassar din yana saukewa, kafafuwan shi har rawa yake jin sunayi dan shi mutum ne mai raunanniyar zuciya.

Gadon da yake dakin ya laluba ya zauna a gefe, yanajin yanda zuciyarshi ke dokawa har cikin kunnnuwan shi.

Yanayin shi kawai da Yassar yake gani na kara tabbatar mishi da yanda ya dade da soyayyar Waheedah adane a cikin kirjin shi batare da kowa yasani ba.

Wani abu Yassar din yaji yana danne shi, yanda akai bai kula ba na bashi mamaki, dan shi mutum ne mai kula da al'amuran yan uwan shi.

Cikin wani yanayi yace
"Hamma..."
Yana tsintar bakin shi da yi mishi nauyi wajen karasa maganar da yake sonyi.

Halin da Yazid din zai shiga yake tunani.

Amman ko jiya da yana neman canji, bayan Abdulkadir din yazo ya dauki wallet din shi ya bude hoton Waheedah na jiki a manne, ya kuma ga ya sake wallet din, amman hoton na manne.

Yasan kanin shi, yasan kanin shi fiye da kowa a gidan.

Idan har ya cire hoton Waheedah daga dayar wallet din ya mayar a sabuwa tana da muhimmanci a wajen shi, idan har zai ajiye hoton daga farko to yana da tabbacin wani abu na faruwa a tsakaninsu.

Idan har zai iya bazai bari su hada yarinya daya da Yazid ba, yana numfashi bazai taba bari wannan rikicin ya faru ba.

"Dan Allah Yassar kace wani abu, a tsorace nake wallah"
Yazid din yace yana sa wani abu tsagewa biyu a kirjin Yassar din, da yake tsaye yana tattaro duk wani karfin halin dazai iya
"Ba Waheedah ba Hamma, kowacce yarinya banda ita"
Kai Yazid din yake girgiza mishi yana jin iskar dake dakin na fara yi mishi kadan, cikin sabon tashin hankali yace
"Yassar..."
Da sauri Yassar din ya girgiza mishi kai, ganin yanayin da yake fuskar shi, ya tabbatar Yazid na tunanin shine yake son Waheedah
"Bani bane, Hamma bani bane ba"
Kan shi Yazid yadan dafe da ya fara ciwo, yanajin alamar zazzabi nason rufe shi
"Abdulkadir ne, ba zance soyayya suke ba kai tsaye, amman hoton tane a jikin wallet din shi shekara daya kenan..."
Wannan karin da duk hannayen shi Yazid ya dafe kan shi yana wani irin sauke numfashi kamar wanda yasha gudu.

Zazzabin da yake ji na saukar mishi gabaki daya.

Dago fuskar shi yayi yana saka hannu ya dauki hular shi dake ajiye akan gadon ya soma fifita dashi, dan sosai iskar dakin ta mishi kadan har bayajin tana kai mishi inda ya kamata ballantana ya iya tunanin wani abu.

Shi kanshi Yassar din wani irin nauyi yake ji yana danne shi da bazai ce ga daga inda yake tasowa ba, amman Yazid din ya kamata yasan abinda yasani shima.

"Koni ba kullum nake kallon fuskar Abdulkadir in fada mishi magana ba, badon ina tsoron shi ba, sai dan ina gudun ya fada mun maganar da zan dake shi saina karya shi.

Ina kula dasu Hamma, cikin ido Waheedah take kallon shi tai mishi magana..."
Sosai Yazid yake fifita fuskar shi, muryar shi can kasan makoshi yace
"Kadan bani waje..."
Cike da wani irin yanayi Yassar yake kallon shi
"Hamma..."
Kai Yazid ya girgiza mishi, zuciyarshi yake ji ta kumbura ta cika kirjin shi taf, bayason ta tarwatse a gaban Yassar, bayason ta tarwatse a gaban kowa
"Dan Allah Yassar...

Bana son in breaking a gabanka...

Abin zaimun yawa..."
Numfashi Yassar din ya sauke yana kallon Yazid sosai, cike da son tabbatar da koma meye zai biyo baya, koya Yazid din zai karye, zai iya komawa dai-dai.

Kamar Yazid yasan me Yassar din yake tunani yadan tattaro sauran karfin da yake ji yana mishi murmushi hadi da jinjina mishi ka cike da son tabbatar mishi cewar wannan abin bazai kashe shi ba, tukunna Yassar ya juya ya fita daga dakin.

Kofar na rufewa Yazid ya kwanta kan gadon yana dunkule jikin shi.

Wani irin ciwo yake ji da bai taba tunanin akwai kalar shi ba.

Numfashin shi har tsai-tsayawa yake da yanda kirjin shi yake zafi, yana jin yanda da duk dakika wani abu a zuciyar shi yana karyewa hadi da faduwa a cikin kirjin shi da wani irin ciwo da bashida kalaman dazai dora shi.

Baisan tunanin me ya kamata yayi ba, asalima tunani daya yake cike da kan shi da zuciyar shi dake karyewa.

'Bazai hada soyayya da kanin shi ba'
Ko rana aka saka mishi da Waheedah yagane Abdulkadir din najin ta a zuciyar shi fiye da matsayin kanwa zai hakura yabar mishi, idan ma Allah bai nufa zai aureta ba, su biyun zasu hakura ta samu wani.

Amman soyayyarta zata kashe shi kafin ya hadata waje daya data kanin shi.

Yanzun yake kara godema Allah da bai furta mata ba, yana kuma tabbatar da wannan ne dalilin daya rike shi harya kasa furta mata.

Yafi minti goma a kwance yana son ciwon da yake ji ya lafa mishi ya tashi ya saka kayan shi dan masallacin idi zasu tafi su duka gidan.

Tana fitowa wanka, mai ta shafa ta zura doguwar rigar sabuwar atamfarta, dankwalin ta daura yanda zata iya dora hijab akai batare daya dameta ba.

Fuskarta ta duba a mudubi, atamfar yellow ce da ja, tayi matukar karbar hasken fatarta, maikon fuskarta taga kamar yai yawa.
Chapter 30 · 0% Book details