← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 94

Sashe 66

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kaf duniyar shi kuma Hajja ce kawai macen da Waheedah bataiwa nisa ba, duk da haka yanajin kamar ya kamata ta nuna mishi ranta ya baci, ko yaga kishi a idanuwanta, amman ya kasa ganin komai, yana kuma jin kamar tana boye mishi asalin abinda takeji ne.

Sosai ya riketa a jikin shi
"Allah ya bani ikon yi muku adalci"
Ya furta a hankali yana lumshe idanuwan shi, badan zuciyar shi bata dokawa Nuriyya ba, sai dan yanajin inda Waheedah take babu wanda ya taba hangowa balle harya zauna.

Ita din daban ce a rayuwar shi.

Hannuwanta Waheedah ta zagaya ta bayanshi tana sake shigewa jikin shi, ta lumshe idanuwanta da yanda takejin zuciyarta kamar da bulallukan tsokoki aka jerata, yanzun kuma rugujewa take ta ko ina, kurar ce take saka jikinta daukar wani irin dumi.

A hankali ta zame jikinta daga nashi tana sauke idanuwanta cikin nashi, rankwafowa yayi ya sumbace ta.

"Sai da safe"
Ya fadi yana juyawa, bata iya ce mishi komai ba, harya fice daga dakin yana komawa ya samu Nuriyya da tunda ya fita takejin kamar ta bi bayan shi ya dawo saboda wani irin azababben kishi daya turnuqeta, gani tayi ya dade, zuciyarta har tafasa takeyi, kwana daya take dashi, yace mata gobe zai wuce, Waheedah ba zata bar mata shi ya dawo ba, zuwa yanzun kishi ya maye gurbin duk wani tsoro data shigo dashi gidan.

Murmushi tayi tana ganin ya shigo, jikinta ya mutu ganin bai mayar mata da murmushin ba.

Karasawa yayi ya zauna gefenta yana kallonta, fuskar shi babu alamar wasa yace
"Bana son tashin hankali, bana son rigima badan ban iya ba, bansan yanda zan daina ba idan na fara.

Nasan halin matata tun kafin in aureta, nasan abinda Waheedah zatayi da wanda ba zatayi ba tun kafin insan zan aureta, bansan halinki ko daya ba na aureki, idan har naji rigima a gidana daga wajenki hakan zai fara.

Ko baki girmama Waheedah ba idan baki shiga huruminta ba nasan ba zata taba biyema kome zakiyi ba.

Zaman lafiyarta na da muhimmanci a wajena, idan har zamana dake zaiyi nisa zaki zauna da ita lafiya..."
Kai Nuriyya ta jinjina mishi a hankali, itama tasan halin Waheedah din, ba saiya jaddada mata ba, wanda duk yake tare da Waheedah yasan halinta, kuma ita bata shigo gidan dan ta nemi rigima da ita ba, duk da tanajin idan Waheedah tai mata ba zataki ramawa ba.

Zadai tayi karya in tace idanuwanta basa mata yaji da shirin taruwar hawayen bakin cikin maganganun shi.

Wani irin kishi takeji marar misaltuwa, zuciyarta na dan tsahirta mata da hannunta da AbdulKadir din ya kama.

Waheedah kuwa AbdulKadir na fita daga dakin ledar apple din ta bude ta dauki guda daya tana shiga bandaki ta wanko ta dawo kan gado ta zauna.

Cinye shi tayi batare data gane dandanon shi ko dalilin da yasa takeci ba, kafin taja kafafuwanta zuwa kan gadon ta kwanta akan bayanta, jin kirjinta na shirin budewa yasa ta juya tana kwanciya kan gefen hannunta na dama.

Wani abu takeji yana zubar mata, da sauri tasa hannu ta taba fuskarta, amman babu digon hawaye ko daya, kuka take amman daga ciki.

Ranar ne ya zame musu MAFARIN komai daya kawo su inda suke yanzun, ranar ne kuma Waheedah taji ta shiga wata duniya da tai nisa da zubar hawaye, duniyar data bata mukullin waccen data bari tana budewa tana zuba duk wani bacin rai da zai sameta ta rufe har zuwa yanzun...!
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#AnaTare
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
PRESENT
A rayuwar shi bai taba sanin menene asalin ma'anar kalmar wulakanci ba sai da yaje NDA, kamar yanda ba zaice ga tun lokacin da yake son saka uniform din sojoji ba.

Sai dai shi mutum ne da idan yasa abu a ranshi, wahala ko makamancin hakan baya hanashi cimma burin shi.

Zai iya rantsewa a yan shekararsu babu wanda ya sha wahalar da yasha a NDA, daga horo zuwa jibga, akwai lokutta da dama a shekarar shi ta farko da baiyi tunanin zai gama NDA da ran shi ba.

Saboda bai iya tauna magana kafin ya fadeta ba, kuma bai iyayin shiru idan yana tunanin akan gaskiyar shi yake.

Abinda ya ja mishi tsana da kauna daga wajen manyan shi.

Zai iya cewa kwana biyar din da yayi bakomai bane akan irin wahalhalun da ya sha a baya.

Abinda ya bambanta da sauran loluttan shine, bashi yayi laifin da kan shi ba, kuma yanzun da yake hanyar shi ta zuwa gida zai shiga gidan batare da yaga Waheedah ba, kuma yayi kwanakin biyar da tunaninta cunkushe a kan shi, ranakun da sukayi mishi wani irin tsayi naban mamaki.

Sabon da yayi da rashin wanka na tsayin lokaci idan aiki ya kaisu wajajen da babu nutsuwar yin hakan bai hanashi jin wari da karnin jinin da yake ba.

Ko sallama baiyi ba lokacin daya shiga gida, bangaren Nuriyya ya wuce, dan haka ko kadan bata tsammaci shigowar shi ba.

Ta dauka auren Anas shine babban tashin hankalin daya faru da rayuwarta, sai kwanaki biyar da suka wuce da ta dawo gida tana rasa inda zata saka rayuwar ta taji sanyi.

Da zazzabi ta wuni, ta kuma tashi dashi ganin har an kwana daya AbdulKadir din bai dawo ba, tayi tunanin zuwa gidansu ta sanar dasu halin da ake ciki, amman ta rasa samun karfin gwiwar yin hakan.

Wanda duk suke dan son ta a gidan su AbdulKadir din sanadin Waheedah ne daman, tun bayan auren ta da AbdulKadir babu wanda ya sake ko kallon inda take ballantana magana ta hadasu.

Ta gwada zuwa gidansu AbdulKadir din sau daya, tunda Hajja ta amsa mata gaisuwa bata sake ce mata komai ba, ta muzanta fiye da tunani ranar, dan har kuka tayi bayan ta fito, bata kuma sake marmarin komawa ba.

Babban tashin hankalin da ta shiga shine tunanin abinda zai biyo baya da fitowar AbdulKadir din, ta kira lambar Waheedah bata san adadi ba, amman a kashe, dan tasan inta fada mata zata gayawa yan gidansu AbdulKadir din ayi wani abu a kai.

Hankalinta in yayi dubu a tashe yake da taga kwanaki na tafiya babu alamar AbdulKadir din.

Yaune ta yanke hukuncin ko me su Hajja zasuyi mata zataje ta same su, dan in su basu kasheta ba, zullumi zai kasheta, ko abinci ta dan samu ta dafa, plate daya haka zata wuni tana jagalar shi.

Tayi zuru-zuru ta fita hayyacin ta, ko hankalinta a kwance yake sai tayi kwana biyu bata share dakinta ba, shima idan AbdulKadir na gari ne sai tayi shara ta gyara gado.

Daya tafi kuma tana hada sati dakinta baiga tsintsiya ba, yanzun kuwa a kwanaki biyar din nan ko wanke-wanke batayi ba, falon a hautsine yake da gwangwanin lemuka da robobin ruwa, dan tunda ta zo gidan shi rabon ta da shan pure water, inya bata kudi ruwan roba take zuwa ta siyo.

Ita kanta rabonta da wanka tun jiya, duniyar take ji ta hade mata waje daya.

Yanzun da AbdulKadir din yake a gabanta, wata irin ajiyar zuciya take saukewa da bata san daga inda take fitowa ba, ta dauka hawayenta sun gama karewa, sai yanzun da taji idanuwanta sun ciko taf da hawaye.

Bata taba tunanin bakin mutum zai iya kara baki ba sai yau, duk kumburin fuskar shi bai hana idanuwan shi yin zuru-zuru suna kara shigewa ciki ba.

Gashi yayi wani irin dukun-dukun.

Kallon ta kawai Abd
ulKadir yayi yana wucewa cikin dakin baccin su, kai tsaye bandaki ya wuce yana cire kayan da yasan sun rigada sun tashi aiki.

Bandakin yake gani yayi mishi kaca-kaca, ga kayan wanki saman injin wanki harda jiqaqqu, wanka yayi, ya saba jikin shi da sabulu yafi sau biyar amman duk da haka jin shi yake kamar akwai sauran dauda a jikin shi.

Towel ya dauka yana goge jikin shi ya daura shi a kugun shi ya fito, idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, dan bayajin komai, zafin dukan da yake jikin shi, ko bacin rai, shiru komai yake mishi.

A karo na farko da ko ganin Nuriyya din bai saka shi jin komai ba.

Banda Waheedah babu abinda yake cikin kan shi.

Takawa yayi yana fita daga dakin, a tsaye bakin kofa yaga Nuriyya tana kallon shi
"Masoyi..."
Ta fadi muryarta na rawa, fuskarta da bayanannen tsoro.

Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta yana kara saka tsoro cika zuciyarta
"Dan Allah...

Dan Allah kayi hakuri...

Kaji...

Bazan sake ba....

Dan Allah karka sakeni, kai mun komai karka sakeni, dan Allah..."
Numfashi nai nauyi AbdulKadir ya sauke, da gaske yake bayajin komai, ciki harda magana da ita, wucewa yayi da nufin karasawa bangaren Waheedah ya dauki kayan da zai saka.

Bin bayan shi Nuriyya tayi tana kamo hannun shi, gabaki daya shirun shi ya kara rikitata
"Masoyi..."
Tsaye AbdulKadir yayi batare daya juyo ba, hannun shi yake kokarin zamewa daga cikin nata, ta sake kamashi tana matsawa ta zagaya ta fuskance shi, wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, tana saka shi tuna yanda ko kadan batasan shi ba, da ta kyale shi, ta nemi waje ta zauna, da bata tsaya a gaban shi tana mishi kukan da baiga dalilin shi ba.

Numfashin ya sake saukewa
"Kaji...

Dan Allah kayi hakuri...dan Allah...

Wallahi ba zan sake ba"
Nuriyya take fadi kuka mai karfi na kwace mata, hannun shi AbdulKadir ya zare daga cikin nata, yana rabata ya wuce, jin takun tafiyarta yasa shi juyawa
"Bance kin mun wani abu ba, ban miki magana ba saboda bana son yin magana da kowa, ki kyaleni Nuriyya, ki kyaleni kafin mu samu matsala..."
AbdulKadir ya karashe maganar yana juyawa ya wuce, da idanuwa Nuriyya tabi shi, zatace yana da wata irin kula da ko a tunaninta ba tayi zaton zata samu a gidan aure ba, abinda duk ta nuna tana so yana kokarin yi mata, idan kudi ta tambayeshi yana bata, wani lokacin yana ce mata bashi da kudin da zai bata ta kashe, akwai hidimar da zaiyi.
Chapter 66 · 0% Book details