← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 94

Sashe 46

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanda za'a raka Zahra har katsina, itama za'a rakata har Minna?"
Kai Hajja ta jinjina sai lokacin ta fahimci abinda yake fada
"Eh, Hajiya Talatu, Hajiya Aisha, Dadda, Da waye naji suna maganar, su bakwai daine zasu rakata, saboda sauran zasu raka Zahra"
Girgizama Hajja kai yakeyi tunda ta fara magana, shi bayason wannan al'adar, a tsarin shi koda na wani gari bane yazo da mota ya dauki matarshi su tafi, su Anty Talatun da take magana su sukaje sukai jeren kaya har Minna din tun satin bikin.

Hakan ma ya isa, Allah ya amfana ba sai sun raka mishi mata ba, bayason wannan al'adar ko kadan
"Kice musu su zauna abinsu Hajja, nida ita kawai zamu tafi da na dawo daurin auren..."
Kallon shi Hajja take kamar bashida hankali
"Bangane me kake son cewa ba"
Numfasawa yayi
"Wani rakiyar amarya nake magana...

Ni banaso...

Su zauna"
Wata dariyar takaici mai sauti da bata da alaka da nishadi Hajja tayi, tana sa AbdulKadir fadin
"Koni in gaya musu suyi zamansu?"
Cike da takaicin da ta kwana biyu bataji irin shi ba take kallon AbdulKadir din
"Wallahi idan baka bacemun daga nan ba saina kwasheka da mari..."
Kallonta AbdulKadir din yakeyi shima
"Mari fa Hajja...me nayi ni?

Me nayi?"
Yake tambaya yana son sanin dalilin da Hajja zatace zata mare shi dan ya fadi ra'ayin shi, yaga kirkine shi su Anty Talatun zasuyiwa, kuma yace bayaso ba sai ayi abinda yace ba tunda matar tashi ce.

"Saina marekan zaka barmun daki ko?"
Dakuna fuska yayi
"Ai bansan me nayi bane ba...

In fada musu zan dauki matata ko zaki fada musu"
Numfashi Hajja ta sauke, idan ta biyema AbdulKadir ba mari ba kawai, rufeshi da duka zatayi.

Batasan ranar da zaiyi hankali ba, har ranta taji dadin hadin auren shi da Waheedah, ko bakomai tana fatan hankali da nutsuwar yarinya su tausasa halayyar AbdulKadir din, har dadi takeji ganin tunda aka fara hidimar bikin babu wanda yai kuka da shi, babu wanda yace yayi mishi rashin kunya.

Amman yanzun yana son jama kanshi zagi da bakin mutane.

"Al'adace hakan, ba kuma za'a canzata daga kanka ba, daga nan har Minna zakace abarka ku tafi ku kadai saboda kai baka da hankali..."
Hajja take maganar cikin fada
"Hajja..."
AbdulKadir ya kira tana katse shi da
"Wallahi idan baka bacemun dagani ba sai ranka yayi mugun baci...

Kuma inji ka sami wani da maganar nan dan Allah...

Yau ka nunamun ban isa dakai ba AbdulKadir kai musu maganar nan..."
Hajja ta karasa tana mikewa taci gaba da hada kayanta da takeyi lokacin daya shiga dakin.

Tunda ya fita ranshi a bace yake harya karasa shiryawa suka fito suna hotunan nan sama-sama yake jinshi, addu'a yake kar wanda ya tabo shi ballantana ya sauke mishi bacin ran da yake ji.

Ko da ake musu hotuna da Waheedah, yana jinta tai magana dai-dai kunnen shi
"Waya tabamun kai Sadauki?"
Taso tasa murmushi ya kwace mishi, tun randa ta fara furta mishi sadaukin nan yaji sunan ya mishi dadi sosai.

Sai dai hakan baisa bacin ran ya tafi ba, ko amsa ma bata samu ba har suka bar wajen.

Da bacin ran ya karasa masallacin, haka har aka gama daurin auren aka fito daga masallacin, a kasan ranshi yakejin wata irin nutsuwa taban mamakin da igiyar data kulle tsakanin shi da Waheedah.

Nanma saida aka tsaya bata lokaci wajen daukar wasu hotunan, danma Abba yace musu a tafi gida, akwai tafiya a gabansu.

Babbar rigarshi ya cire dan jinshi yake a takure yana sake kayan, duk da wata shaddar ya sake sakawa, amman bayajin nauyinta kamar wanda ya cire, ninke su yakeyi yaji Yassar ya shigo dakin da sallamar da ya amsa yana ci gaba da linke kayan da yakeyi.

"Kayi sauri, an fara shirye-shiryen tafiya..."
Kai kawai AbdulKadir din ya dagama Yassar yana saka shi fadin
"AbdulKadir..."
Bai amsa ba tunda kunnuwa ne suke jin magana
"AbdulKadir..."
Ya sake kira, kananun idanuwanshi ya sauke kan fuskar Yassar
"Kunnuwane suke ji Hamma...

Kasan ina jinka ai"
Numfasawa Yassar yayi
"Zaka dauki yar mutane zuwa wani gari, AbdulKadir ba'a aura maka ita dan an gaji da ita ba, ba kuma a aura maka ita dan an gaji da kula da ita ba.

Rokonka nake karka kuntata mata, karka cutar da ita..."
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance
"Dan ba'a jarabawar samun limanci da nace ka yanki form Hamma..."
Kai Yassar yake girgiza da murmushi a fuskar shi
"Dan ubanka ba maganar wasa nake dakai ba, nasiha nake maka"
Ware mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Abinda yasa nace limanci zai maka kyau kenan"
Dafe kai Yassar yayi, baisan ranar da AbdulKadir zai fara daukar abubuwa da muhimmanci ba, ganin babu alamar zai saurare shi yasa shi mikewa yana fadin
"Abba na kira..."
Dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Dan Allah Hamma kace ba wata nasihar za'aimun ba...

Wai ita Waheedah ba za'ai mata bane ba?

Nima ai aurena aka bata, me yasa ni kadai za'a dinga yiwa....

Itama kaje kace ta riqeni amana, karta cutar dani..."
Kofar Yassar ya bude kamar baiji abinda AbdulKadir din yace ba
"Hamma magana nake kana tafiya..."
Ficewa yayi yana jan kofar, fuska ya kara dakunawa yana dibar kayan ya tura cikin karamar jakar daya shirya duk kayanshi da zai iya dauka a ciki, yawanci kananun kayane, manyan fiye da rabi anan gida yabarsu.

Jakar ya bari kan gado yana fita daga dakin zuwa bangaren Abba yana shiga da sallama, babu kowa sai Waheedah da take zaune a gaban Abba, ta sake rigar dazun, bai gama ganinta ba sosai cikin rigar ta sake, yanzun bayama iya ganin fuskarta dan lafayane a jikinta anja shi an rufe fuskarta gabaki daya, yanayin yanda kafadunta suke rawa yasa shi gane kuka takeyi.

Gefenta ya zauna yana fadin
"Abba gani...Hamma yace kana kirana"
Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin kaunar su fal cikin ranshi, yana kuma mamaki har lokacin yanda kaddarar rayuwa ta kawosu inda suke yanzun.

Cikin ranshi yake ma Allah godiya yana karawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci.

"Idan da wani yace mun zaku zo nan a rayuwar ku ko na yarda zan jinjina lamarin..."
Abba ya fara magana yana dorawa da
"Ko da kukejin ana kiran hakuri a zaman aure, badan yana jigon auren bane gabaki daya, sai dan yana taka muhimmiyar rawa a zamantakewa ta yau da kullum.

Abu daya zan fada muku, karku bani kunya, ku dukanku karku bani kunya.

Matsalar aurenku kuyi kokarin ganin kun shawo kanta da kanku, sirri na daya daga cikin abubuwan da suke da muhimmanci a aure...

Ku rike sirrin junanku kamar fitar dashi zai iya zame muku matsala.

Dan nace hakan kuma ba ina nufin ya baku damar da zaku cutar da junanku dan zaku rike a matsayin sirri ba.

A duk lokacin da hakan ya faru, kuke ganin ba zaku iya ba ku daga waya ku kirani, shine kawai mutuntakar da zakuyi mun, ku sanar dani kafin yanke hukunci mai girma..."
Su dukansu sunyi shiru suna sauraren Abba, Waheedah daman tunda aka rakata wajen Mami take kuka, har aka kawota wajen Abba, yanzun ma kukan takeyi sosai.

AbdulKadir kanshi Abba yasa jikinshi yin sanyi, tabbas aure abune mai girman gaske, bazai tuna ranar karshe da Abba ya zaunar dashi yana mishi nasiha har yanajin kaunar shi a tare da kalaman shi ba sai yau.

"Allah yai muku albarka a zamantakewar ku, Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi..."
Abba ya karasa da wani yanayi mai nauyi a muryarshi, har a kasan ranshi ya fara jin kewar yaran nashi.

"Mungode Abba..."
AbdulKadir ya fadi yana mikewa, amman Waheedah ta kasa mikewa, magana zai mata Anty ta shigo, bata ce mishi komai ba tazo ta kama Waheedah tana janta suka fice daga dakin.

Kukan da take yai mishi tsaye a makoshi.

Bin bayansu yayi yana wucewa bangarensu dan ya dauki jakarshi, yasan zai kwana biyu bai shigo Kano ba, makarantar Waheedah ma transfer akai mata zuwa Minna din, badan Abba yasan mutane ba da hakan yai musu matuqar wahala.

Kuma yanda yakeji bazai iya barinta a Kano ba, inda duk yasa kafa nan zata mayar da tata.

Saidai ta hakura da makarantar.

MINNA
Gajiya takeji har a kasusuwan ta, wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taba zuwa wani waje daya wuce kauyen bugaje.

Jitai kamar zasu je karshen duniya, kamar tafiyar kwanaki ce a maimakon ta yini daya.

Sosai ta gode ma Anty Aisha data hada mata ruwa mai zafi tace taje tai wanka.

Sosai tadanji dadin jikinta, wasu kayan ta samu an dauko mata, doguwar rigace ta atamfa sabuwa fil, dauka tayi ta saka tukunna ta dauki hijabin da tagani dan gabatar da sallar magriba tabi data isha'i tunda ta samu tsarki.

Hakan kuwa tayi, lokacin data idar an kawo musu abinci kala-kala a take-away da alama siyowa akayi.

Guda daya aka ajiye mata a gabanta, ta cire hijabin ta dora kan gadon da yake dakin kenan tana shirin bude robar abincin dake gabanta da batajin yunwar cin shi ko kadan saboda kewar gida da takeyi ga kuma gajiya, aka kwankwasa dakin.

"Waye?

Shigo..."
Anty Talatu ta amsa, AbdulKadir ya shigo da sallama, a bakin kofar yai tsaye yana fadin
"Anty sannunku da hidima...

Waheedah dan zo"
Wata irin kunya taji ta rufeta ganin gabaki daya su Anty ne a wajen, harda danginta na wajen uba guda biyu.

"Ki tashi kije mana"
Anty Aisha ta fadi, kafafuwanta da matukar nauyi taja su tana mikewa, mayafinta da aka fito dashi shima sabo ta dauka, sai lokacin AbdulKadir ya mayar da kanshi yana fita daga dakin, kafafuwanta babu karfi ta wuce tana fita daga dakin, ji takeyi kamar idanuwansu nakanta duk da tana jin suka cigaba da hirarsu kafin taja musu kofar.

Kamar hakan AbdulKadir yake jira ya kama hannunta yana fara janta
"Ina zamuje?"
Ta tambaya, juyowa yayi yana kafeta da idanuwanshi da suka sakata yin shiru, saida taga suna shirin nufar hanyar da zata fita dasu daga gidan tukunna tace
"Takalmana Hamma..."
Hannunta ya saki yana kallon kafafuwanta, hanyar bedroom din da suka baro ya nufa, tsinin takalmanta yasa shi gane sune ya kwaso mata yana dawowa ya ajiye mata su, sakawa tayi ya sake kama hannunta suna fita.
Chapter 46 · 0% Book details