Sashe 62
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzun kuma Waheedah nada wani cikin, yana son ta samu duk kulawar da take bukata, asibiti me kyau da baifi karfin shi ba.
Sannan ga kayan babies da itama kayan da zai mata da sauran hidindimu.
Amman auren ma shiya yanke hukuncin yin shi.
Dole ne yayi abinda ya dace.
Akan maganar kudin kayan ne sukai doguwar waya da Nuriyya.
Ya karbi account number dinta ya tura mata, ta mishi maganar tarewa yace mata saiya koma nan da sati biyu sai suyi maganar.
Badan bashida wajen da zai ajiyeta ba, sai dan har zuwa lokacin bai fadama Waheedah ba.
Duk wayar da zasuyi sai yaji zuciyarshi ta doka, hankalin shi baya kwanciya sai yaji tana mishi hira, gani yake kamar wani daga cikin yan gidansu zai sameta ya fada mata.
Duk da zaiso hakan, zasu hutar dashi, amman kuma dukkan zuciyarshi na fada mishi zai kyautu ya fada mata da kan shi.
In da zai samu kwarin gwiwar yin hakan.
Idan yace ga yanda watan ya wuce mishi da sauri haka yayi karya.
Bai taba ganin gudun kwanaki ba sai da yagan shi yana hada abinda yake bukata a yar jakar shi da yammacin juma'a, dan ranar zaibi motar dare ya isa Kano da safiyar asabar.
Yasan yau dinne ranar karshe da yake da ita da zai fadama Waheedah ya kara aure, idan bata sani yau ba sai yaje gida gobe tukunna, ba kuma yajin zai iya kallon idanuwanta ya fada mata.
Bashi da wannan karfin halin, yanzun kuma yake sanin hakan.
Gefen gadon dakin yake zaune, ya mika hannu ya dauko wayar shi.
Lambar Waheedah ya lalubo, basu dade da gama magana ba, ita tasa shi ya tashi ya hada kayan shi, tace karya taho da yunwa, yaci wani abu.
Amman abinci ne karshen abinda yake ranshi.
Sake kira yayi, ta daga da fadin
"Sadauki...
Harka shirya kayan?"
Kai ya daga mata batare da yace komai ba, dan a rayuwarshi ita kadaice take fahimtar shirun shi, da yayi magana da baiyi ba Waheedah takan fahimta, abin ya daina bashi mamaki.
"Menene?
Shirun nan naka yana mun yawa kwana biyu.
Wani abu yana damunka amman kaqi fadamun ko?"
Numfashi ya tsinci kanshi da saukewa da baisan yana rike dashi ba.
Muryarshi na rawa yace
"Magana nake so in fada miki, ba tun yau ba, tun ana gobe zan taho, bansan ta ina zan fara bane Wahee...a karo na farko da bansan yazan miki magana ba, ina nufin kece, komai fada miki nake batare da tunani ba, na kasa yanzun....
Ina so in fada miki har raina amman na kasa"
Ya karashe yanajin wani irin tashin hankali da bai taba tunani ba
"Nice kaman yanda kace...
Akwai wani abu da zaka boyemun?
Ka fadamun dan Allah...
Menene?"
Kai AbdulKadir yake girgizawa, yanayin muryarta ya kara sakawa yaji komai ya kwance mishi
"Bansan ya zan fara ba"
Shiru tadanyi na wasu dakika kafin tace
"Sadauki kana tsoratani, cikine a jikina ko ka manta?
Ka fadamun dan Allah"
Wannan karin hannu yasa yana dafe kan shi, bugun zuciyarshi na karuwa, sauke wayar yayi daga kunnen shi yana kashewa.
Kafin ya rasa kwarin gwiwar da yakeji ya bude shafin tura saqo ya fara rubutu
'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan yazan fada miki ba'
Ya tura yana jin kamar yabishi ya kamo, sai dai kamar auren shine, ya riga da ya faru, babu damar komawa baya ya canza komai, sakon ya riga ya shiga dan ya nuna mishi alama Waheedah ta samu, zufa yakeji a duk wata kafa ta jikin shi yana jiran ganin sakonta.
Da hasken wayar ya dauke sai ya sake tabawa, bai san ya dauki mintina talatin yana jiran sakonta ba saida ya duba lokaci.
'Dan Allah kice wani abu Waheedah, ki ce wani abu'
Nan ma saida ya kara mintina goma yana zufar da duk iskar fankar dake dakin bata kai mishi kafin yaga wayar shi ta kawo haske.
Jikin shi babu inda baya rawa ya daga yana dubawa.
'Ran daren da zaka tafi?
Wata daya daya wuce kenan ko?'
Da sauri ya fara bata amsa
'Da gaske Wahee, ki yarda dani tun ranar naso in fada miki, tun ranar'
Wannan karin bata dauki lokaci ba ta turo mishi
'Karka damu.
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, bari inyi alwala naji an fara kiran Magriba'
Wata irin ajiyar zuciya AbdulKadir din ya sauke, kafin ya sake ganin text dinta
'Allah ya tsare ya kawo mana kai lafiya, ka daici abinci karka manta.
Zan sa chargy an kawo wuta, saura 2%'
Da murmushi a fuskarshi yace
'Nagode, Nagode sosai.
In shaa Allah.
Ki kulamun da ku.
Zan kiraki dana shiga mota'
Ya sa ran amsa koya take, dayaga bata turo komai ba ya mike yana hakura.
Wanka ya shiga yayi ya fito ya sake kayan jikin shi tukunna ya fita masallaci.
Saida ya biya ya siya abinci yaci, hankalin shi yakeji ya kwanta sosai.
Yasan daman idan kowa bai fahimce shi ba, Waheedah zata fahimce shi, shisa take da matsayin da babu wanda yake dashi a rayuwar shi.
Yana dawowa jakar shi ya dauka yayi addu'a a bakin kofa kafin ya fita ya kulle gidan yana takawa zuwa gate da zai samu yaje inda zai hau machine zuwa tasha...!
#TeamWaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Wayar tasa a chargy kamar yanda ta fada mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da tayi.
Wayar take kallo tana gane asalin ma'anar 'Yawo kan gajimare'.
Duk da ba zatace ga ranar da wuyanta ya gajiya da daukar nauyin kanta ba, yau kan jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta.
Kafin kan nata yai wata irin sarawa cike da fahimtar ma'anar
'Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan ya zan fada miki ba'
Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta takeji yana barazanar kin wuce kirjinta yakai inda zai ba zuciyarta damar cigaba da dokawa yanda ya kamata.
Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da takeji yafi karfin hawayenta.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ta samu furtawa tana zama sosai kafin taja kafafuwanta ta dora kanta a sama ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taba shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da zata shiga tafi waccen wahalar sha'ani ba sai yanzun.
Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin kasusuwan jikinta.
Idan tace ga asalin abinda ya fi mata ciwo karya take.
Auren da yayi da batada darajar da zata sani kafin a daura shi, kallon idanuwanta bayan an daura din dayi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zabar ya fada mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta sakon waya.
"Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki?
Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al'amari ba?"
Waheedah take maganar kamar zararriya, dan batasan a fili takeyin ta ba, ta dai san daga wani bangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa.
Bata san iya lokacin da ta dauka a zaune tana kallon bango batare da tasan asalin abinda take tunani ba, banda wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi batajin komai.
Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, dakyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar
'Sadauki'
Ta gani rubuce a jiki
"Me kake so dani Sadauki?"
Ta tambaya tana kallon wayar harta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa.
Hannu ta mika ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran hadi da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya tace
"Hello..."
Tana mike kafafuwanta da sukai mata sanyi, ga abinda ke cikinta da taji ya dunqule waje daya kamar yana tayata daukar ciwon da takeji, hakan nasata fahimtar wani irin ciwon mara da batasan tun yaushe ya fara mata ba.
"Kin fara bacci ne?"
Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da taji muryarshi na kara mata ciwo, taji da magana dashi gara mata kallon bangon da takeyi, shi baya kara mata ciwo, amman muryar AbdulKadir din kamar gishiri a sababbin ciwukan da yaji mata takejinta.
"Na sa chargy ne"
Dan jim yayi ta dayan bangaren kafin yace
"Inata kira tun dazun babu network"
Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri
"Har kun taho?"
Ta tsinci kanta da tambaya
"Tun dazun, amman cunkoso har yanzun muna cikin Lagos"
Kai ta jinjina mishi
"Allah ya tsare maka hanya ya kawo ka lafiya"
Amsawa yayi da
"Amin..."
Yana dorawa da
"Ki kula da kanku"
Ita ta jinjina kan tana kasa cewa komai ta sauke wayar daga kunnenta, chargyn ta mayar, dakyar ta iya mikewa, wani irin jiri daya dibeta yasa ta koma tana kiran sunan Allah duk wanda ya zo bakinta.
Numfashi take fitarwa a wahalshe, ciwo take ji da bazai misaltu ba, tafi awa daya a zaune kafin ta iya mikewa, Fajr ma bata iya ta matsar dashi gefe ba, ita taja jiki kan katifar ta kwanta gefen shi.
Ko sallar isha'i batayi ba, amman ciwon da takeji ba zata iya zuwa bandaki har ta iyayin alwala ba.
Daga kwancen ma jiri take ji.
Bata san dare yayi ba sai lokacin da ta samu ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta taga karfe daya.
Ajiyewa tayi har lokacin jiri takeji.
Ga ciwon marar da takeji ya tsanantar mata, ga wasu ciwukan daban da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, amman mararta da zuciyarta su tafi ji.
Bango ta dinga bi har takai bandaki, dakyar ta iya daura alwala ta fito.
Daga zaune tayi sallah dan ba zata iya tsayuwar ba, azkar ta gabatar na bayan sallah, tana kwanciya anan kan kafet din dan ko addu'a bata iyayi ba.